Aminiya:
2025-04-10@05:05:50 GMT

Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’

Published: 9th, March 2025 GMT

Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci.

Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar.

Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai

Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin al’ummar Musulmi.

A jawabinsa bayan buɗa-bakin azumi, Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata jin daɗin malaman Tsangaya da kuma yara Almajirai.

Ya bayyana muhimmancin ilimin Alƙur’ani ga al’umma tare da jaddada buƙatar samar da yanayi mai ɗaukaka koyo da koyarwa.

Gwamnan ya yi bayanin yadda gwamnatinsa ta yi gagarumin ƙoƙari wajen gina manyan makarantun Tsangaya da ƙananan makarantun Almajirai a faɗin jihar, tare da haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani cikin tsarin karatu.

Haka kuma, ya yi nuni da cewa yara Almajirai an sanya su cikin shirin lafiya na Go-Health, wanda ke ba su damar samun kulawar lafiya kyauta domin tabbatar da lafiyarsu.

“Mu a matsayin gwamnati mun fahimci muhimmiyar rawa da makarantun Tsangaya ke takawa wajen tarbiyya da cigaban ilimi ga yaranmu.

“Wannan ne ya sanya muka fifita jin daɗinsu ta hanyoyi daban-daban, ciki har da gina makarantun Tsangaya da kuma shigar da su cikin shirin Go-Health domin samun ingantacciyar kulawar lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Gwamna Inuwa.

Da yake magana a madadin malaman Tsangaya, Goni Mai Babban Allo ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya kan goyon bayan da yake bayarwa ba dare ba rana.

Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya ɗauki matakai na musamman, ciki har da gina makarantun Tsangaya, sanya fitilu masu aiki da hasken rana a makarantun, da haɗa Almajirai cikin shirin kula da lafiya na jihar Gombe.

“Ba mu taɓa samun gwamnati da ta damu da jin daɗin malaman Tsangaya da ɗalibanmu kamar wannan ba,” in ji Goni Mai Babban Allo.

A cikin girmamawa ga ƙoƙarinsa da kuma sadaukarwarsa, Ƙungiyar Alarammomi ta naɗa Gwamna Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’, alamar kasancewarsa bawan Alƙur’ani mai sadaukarwa.

Tun da farko, a jawabinta na maraba, Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan harkokin Tsangaya da Ilimin Almajiranci, ta yi kira ga Alarammomi da su ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Yahaya jihar Gombe malaman tsangaya Gwamna Inuwa Yahaya makarantun Tsangaya malaman Tsangaya a makarantun Tsangaya da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Zulum Ya Yi Allah-wadai Da Sabbin Hare-haren Boko Haram Da Sace-sacen Mutane A Borno

Sai dai ya koka da yadda hare-haren da aka kai kwanan nan, inda aka tarwatsa sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, Izge a karamar hukumar Gwoza da sauransu wanda hakan ya yi sanadin kashe mutane ‘yan gari da jami’an tsaro, lallai abun damuwa ne matuka.

 

Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wani taro na musamman na tsaro wanda ya samu halartar babban kwamandan runduna ta 7 ta rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Haruna da kwamandojin sassan rundunar da kwamishinan ‘yansanda na jihar da shugabannin sauran hukumomin tsaro.

 

Taron ya kuma samu halartar Shehun Borno Alh. Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi; Shehun Bama, Sarakunan Biu, Uba, Askira, Gwoza, yayin da Shehun Dikwa da Sarkin Shani aka wakilce su.

 

Zulum ya yabawa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da jami’an tsaro bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen yaki da Boko Haram.

 

Ya kara da cewa, dole ne a kara kaimi ta hanyar samar da kayan yaki na zamani ga sojoji domin dakile duk wani sabon harin da zai addabi sassan yankin Sahel na Borno da ke kan iyaka da kasashen Jamhuriyar Chadi, Nijar da Kamaru.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Yi Kira Da A Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Tare Da Kasashe Makwabta
  • ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang
  • Likitocin Nijeriya dubu 16 sun yi ƙaura zuwa ƙetare — Ministan Lafiya
  • Gwamna Zulum Ya Yi Allah-wadai Da Sabbin Hare-haren Boko Haram Da Sace-sacen Mutane A Borno
  • Kyautar LEADERSHIP Ta Kara Zaburar Da Mu Kan Sauke Nauyin Al’ummar Jigawa Akanmu – Gwamna Namadi
  • Gwamnan Kano Ya Sadaukar Da Lambar Yabonsa Ga ‘Ya’yan Marasa Ƙarfi A Kano
  • Ya Kamata Lambar Yabo Ta Zama Hanyar Ƙarfafa Mana Gwuiwa – Misis Nda-Isaiah
  • Jam’iyyar Labour Ta Yi Barazanar Dakatar Da Peter Obi Da Gwamna Otti
  •  HKI Ta Kai Munanan Hare-hare Akan Yankin Khan-Yunus
  • ACF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Kawo Karshe Tashe-Tashen Hankula Filato