HausaTv:
2025-04-25@09:53:46 GMT

Trump Ya Yi Barazanar Korar Daliban Da Ke Goyon Bayan Falasdinawa

Published: 5th, March 2025 GMT

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga.

Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York.

Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.”

Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya Trump ya yi barazanar korar duk daliban da suka shiga zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

A karshen watan Janairu, Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta bukaci gwamnati ta kori daliban kasashen waje da suka shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.

Ya yi zargin cewa zanga-zangar da aka yi a harabar jami’ar ta haifar da “kyama, barna da kuma cin zarafi a kan ‘yan kasarmu, musamman a makarantunmu da harabar jami’armu.”

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da masana shari’a sun dage cewa wannan umarni ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: bayan Falasdinawa zanga zangar Trump ya yi

এছাড়াও পড়ুন:

 Ministan Tsaron Pakistan Ya Yi Wa Pakistan Barazanar Kai Mata Hari Mai  Tsanani

A daidai lokacin da sabani yake yin tsanani a tsakanin India da Pakistan, bayan wani hari da aka kai a Kashmir da ya yi sanadiyyar mutuwar  mutane 26, ministan tsaron kasar Pakistan Khajah Asif ya ce; matukar India ta keta hurumin kasarsa, to kuwa za ta fuskanci mayar da martani mai tsanani.

Minista Khajah Asif ya kuma gargadi kasar ta India da ta guji keta hurumin kasar Pakistan.

Asif ya kuma bukaci India da ta gudanar da bincike akan harin da aka yi a ranar Talata a yankin Kashmir, kuma ta nesanci yin wani abu wanda zai jefa yankin cikin yakin da ba a san yadda karshensa zai kare ba. Haka nan kuma ya ce; Tushen matsalar tana nan a cikin kasar India,kuma wadanda su ka shirya kai harin suna nan a cikin India, don haka a cikin India ya kamata ta neme su.”

A lokaci daya kuma ministan tsaron na Pakistan ya jadada cewa; Kasarsa ba ta da sha’awar yaki ko kadan, amma idan aka kallafa mata yaki, to martanin da za ta mayar zai zama mafi dacewa kuma  cikin karfi.”

A nashi gefen, ministan harkokin wajen  kasar Pakistan Muhammad Ishaq Dar, ya ce, kasarsa tana sa ido da bibiyar abinda India take yi a kusa, kuma a shirye take ta kare tsaronta da iyakokinta.”

Dar ya kuma fada wa wata  tashar talabijin din cewa; Pakistan kasa ce da take da makaman Nukiliya, tana kuma da dandazon makamai masu linzami masu karfi, kuma India ta kwana da sanin hakan, don haka ta guji keta hurumin kasar Pakistan da tsaronta.”

India ta zargi Pakistan da hannu a harin da aka kai a yankin Kashmir wanda ya yi sanadiyyar mutane 26. Kasar ta India ta kori Jakadan Pakistan daga kasarta, sannan kuma ta kira yi nata jakadan daga Islamabad. Bugu da kari Indiyan ta dakatar da aiki da yarjejeniya akan ruwa a tsakanin kasashen biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zulum Ya Taya MNJTF Da Gwamnatin Alihini Bayan Harin Boko Haram A Wulgo
  • Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya
  • Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran
  •  Ministan Tsaron Pakistan Ya Yi Wa Pakistan Barazanar Kai Mata Hari Mai  Tsanani
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
  • An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure
  • Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
  • Ƙasurgumin Ɗan Fashin Da Ake Nema Ruwa A Jallo Ya Mutu Bayan Arangama Da ‘Yansanda A Kano
  • Kungiyar Hamas Ta Bukaci Goyon Baya Daga Sauran Falasdinawa Na Gabar Yammacin Kogin Jordan
  • Hargitsi A Filin Wasan Kwallon Kafa Tsakanin Al-Ahly Tripoli Da Al-Suwaihli A Kasar Libiya