2025-04-05@12:34:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 91
«bayan Falasdinawa»:
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci. Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa. Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA Gobara ta tashi a Jami’ar Northwest da ke Kano Ta kuma yi watsi da iƙirarin da ake na cewa sojoji sun rage kai hare-hare kan makiyaya, ’yan bindiga, ɓarayin shanu da sauransu, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kame Turji. Wannan na zuwa ne kimanin kwana ɗaya bayan Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu da ke ƙaramar...
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su. Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya. Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da motocin Sarkin ke wucewa. Duba hotunan hawan a ƙasa: Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46 a duniya, ta aika sako cikin shafinta na yanar gizo inda take goyon bayan kungiyoyin Hamas da Hizbullah na kasar Lebanon sannan tana allawadai da kuma aibata HKI kan kissan yara da take yi a Gaza. Gwamnatin kasar Amurka dai tana ganin kanta a matsayin kasa wacce take gaba wajen kare hakkin fadin albarkacin baki, amma idan al-amarin ya shafi HKI sai ta nuna...
Sarkin Kano mai daraja ta daya wanda ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, don haka, ya amince da janye duk wasu shirye-shiryen bikin hawan Sallah mai ban sha’awa, wanda ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da al’adu (UNESCO) ta bayyana a matsayin gadon bil’adama mara misaltuwa. LEADERSHIP ta rawaito cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya sanar da dakatar da bikin hawan Sallah, saboda barazanar tsaro da jami’an leken asiri suka rahoto a jihar. Dangane da haka, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda...
Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke shirinsa na yin hawan, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da malamai da dattawa suka ba shi. “Muna tabbatar muku cewa hawan Sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai haddasa tashin hankali, wajibi ne a dakatar,” in ji Aminu Ado Bayero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi. Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi. Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano. Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma. A cikin wata...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura. Yace, an sami gudunmawar kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah. A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu, Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
Ya ce, “Da misalin karfe 7:28 na safe ne wasu da ke sharar masallacin suka ga mutumin a kwance a cikin masallacin, sai suka yi kokarin tayar da shi domin su yi shara amma shiru. Nan da nan, sai mutanen suka sanar da Musulman yankin lamarin, inda suka garzaya da shi zuwa asibiti, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa. Musa ya ce, daga bisani aka mika gawar marigayin ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallo a wasan da Portugal ta doke abokiyar karawarta ƙasar Denmark a daren ranar Lahadi, ƙwallon ita ce ta 929 da tsohon ɗan wasan na Manchester United ya jefa a tarihinsa na ƙwallon ƙafa, duk da cewar ya ɓarar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan da Portugal ta tsallake rijiya da baya, hakan ya sa ta kai wasan dab da na kusa da na karshe a gasar ta Nations League. An tashi wasan ne da ci 3-3 jimilla bayan mintuna 90, amma Francisco Trincao ya sake zura kwallo a minti na 10 na ƙarin lokaci bayan da mai tsaron ragar Denmark Kasper Schmeichel ya ture wata ƙwallon da Goncalo Ramos ya buga....
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet. Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
Dubban dubatan mutane masu goyon bayan magajin garin Istambul a kasar Turkiya ne suka fito kan titunan birnin inda suke bukatar gwamnatin Urdugan ta sake shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mutane suna ganin Ekrem Imamoglu, dan takarar shugaban kasa ne a zaben shugaban kasa mai zuwa kuma mai yuwa ya kara shugaban Urdugan a zaben, saboda yawan magoya bayansa a kasar, musamman a birnin Istambul. Labarin ya kara da cewa Imamoglu mutum ne wanda yake da karbuwa a cikin mutanen kasar, wanda kuma ana ganin mai yuwa ya kada shugaba Urdugan a zaben shugaban kasa mai zuwa. Don haka ana ganin gwamnatin Urdugan ta sa aka kamashi, tare da zargin cin hanci da rashawa,...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All… Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967. Inda yahudawan suka mamaye har da gabacin birnin Qudus sannan sun ginawa yahudawa...
An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim. An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a....

Ma’aikatar Harkokin Wajen JMI Ta Yi Allawadai Da Kungiyar G7 Wacce Ta Zargin Kasar Da Abubuwa Da Dama
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...

Kungiyoyin Falasdinawa Suna Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki. Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau. A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi. Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan. “A wannan karon,...
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare, duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya yi nuni da lamari na baya-bayan...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da tallafin kayan abinci ga magidanta dubu 30 a fadin jihar. A yayin da yake kaddamar da tallafin tare da bayar da jari ga masu kananan sana’oi a gidansa a ranar Litinin, ya bayyana cewar tallafin wani mataki ne na saukakawa mabukata halin kunci a watan Ramadan mai girma. Sojoji Sun Miƙawa Gwamnatin Borno Mutane 75 Da Suka Ceto Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Masanin Aikin Jarida, Kabir Ɗangogo Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa, ya bukaci wadanda za su rarraba kayan abincin da su gudanar da gaskiya da adalci wajen tabbatar da tallafin ya kai hannun wadanda suka cancanta a mazabu 244...

Tutocin Falasdinu Sun Yi Ta Kadawa A Birnin Sao Paulo Na kasar Brazil, A Gagarumin Gaggami Da Masu Goyon Bayan Falasdinawa Suka Shirya
Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran. A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan...
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo. Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
Ministar Harkokin Mata, Imaan Suleiman Ibrahim, ta yi alƙawarin sasanta Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida bayan kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a ya same ta da laifin karya dokokin majalisar. Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC Yayin da ta ke magana da manema labarai bayan taron bikin Ranar Mata ta Duniya, ministar ta bayyana takaicinta kan dakatarwar da aka yi wa Natasha. Ta ce, “Abin takaici ne kuma bai kamata ya faru ba. A majalisa ta baya, muna da mata Sanatoci guda tara, amma yanzu huɗu...
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci. An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu. Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan. Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba. Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za...
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayar da shawarar a dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida. Kwamitin ladabtarwa da ɗa’a ne, ya bayar da shawarar biyo bayan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, kan cin zarafinta. Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya rasu A yi adalci a binciken mutuwar dan kwallon Nijerirya a Uganda —Gwamnatin Sakkwato A zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis, Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya gabatar da rahoton kwamitin, inda ya bayyana cewa Natasha ta ƙi bayar da haɗin kai wajen binciken da aka yi. Kwamitin ya kuma bayar da shawarar a dakatar da biyanta albashi tare da janye mata jami’an tsaron da ke kula da ita. Rikicin ya...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York. Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.” Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya...
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron da kasashen larabawa suke yi a Masar, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin da su ka bijiro da shi na sake gina yankin Gaza, ba tare da an fitar da Falasdinawa daga cikinsa ba. Gutress ya ce; Ina maraba da kuma nuna cikakken goyon bayana ga shirin da taron kungiyar kasashen larabawa ta bijiro da shi na sake gina Gaza.” Gutrress ya kuma ce: MDD a shirye take ta shiga da karfi a yi wannan aikin da ita. Haka nan kuma babban magatakardar MDD ya yi kira da a dauki duk matakin da ya kamata domin ganin ba a sake komawa yaki a Gaza ba. Gutteres ya kuma ce, Gaza ba...
Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.” Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka”...
Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa. ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci. Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata. Amma daga bisanio ya zarge su da...
Sai dai, a martanin da ta yi ta bakin lauyanta a ranar Asabar, Giwa ya bukace matar Sanata Akpabio ta da janye kanta a rikicin don bai wa mijinta damar kare kansa saboda wanda yake karewa tana da “kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da zarginta.” Sanata Natasha ta kai karar Akpabio da mai taimaka masa, Mfon Patrick gaban kotu, inda ta bukaci diyyar Naira Biliyan 100.3 bisa zargin bata mata suna bayan takaddamar da ta biyo bayan sauya mata kujera a zauren majalisar dattawa. Sanata mai wakiltar Kogi ta Arewa, wacce aka dakatar kuma aka mika wa kwamitin da’a na majalisar dattawa koke akanta, a yayin wata hira da gidan talabijin, ta ce, Sanata Akpabio ya ki...
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira. Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa. Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967. A ranar Talata...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar. Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci. Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar. Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci. Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan...
Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ma’aikatan da suka rasu. Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a ofishin fansho da ke Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa kudaden sun hada da na barin aiki, da na ma’aikatan da suka mutu. A cewarsa, ma’aikatan 281 sun hada da na jiha, da kananan hukumomi da na hukumar ilimi, wadanda suka yi ritaya na son rai ko kuma sun kai shekarun ritaya ko kuma wadanda suka mutu suna aiki. Dakta Bilyaminu Shitu...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da kungiyar Hamas ke yi. Bayanai sun ce za’a saki falasdinawan su 206 a cikin sa’o’I 24 masu zuwa. Dangane da dakatar da sakin fursunonin, Hamas ta zargi Isra’ila da “saka dukkan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin hatsari mai tsanani” tare da yin kira ga kasashe masu shiga tsakani da su shiga tsakani. A nata bangaren, Hamas za ta mika wasu gawawwakin ‘yan Isra’ila hudu da...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda. Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene. Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya...
Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa. An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar. ’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya...

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza a jiya Lahadi. Ya kara da...
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron kasar nan. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. A cewar sa, kiran ya zama wajibi domin karfafa tsaro a fadin Najeriya. Alhaji Badaru Abubakar, ya yi nuni da cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar cikin ‘yan watannin nan. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi iya bakin kokarinta wajen yaki da rashin tsaro, kuma za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin da ake so. Ministan ya...
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza. Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman,...
Kafin ya zama sanata, ya yi majalisar dokokin ta tarayya da ya wakilci mabazar Toro daga 2011 zuwa 2018. An shirya masa jana’iza da ƙarfe 1pm a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairum 2025 a Masallacin da ke kofar gidansa da ke Gwarimpa, Abuja. Cikakken labarin daga baya:
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...

Iran Ta Yi Tir Da Shugaban Hukumar IAEA Saboda Sanya Siyasa Da Daukan Bangare A Jawansa Na Baya Bayan Nan
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi hukumar IAEA mai kula da al-amuran makamashin nukliya a duniya, bayan da babban sakataren kungiyar Rafaei Grossy ya fita daga matsayin dan ba ruwammu, a cikin harkokin siyasa a aikinsa, inda ya furta wasu jawabai dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gorossi ya fita daga matsayinsa na gwararre da kuma masanin harkokin makamashin nukliya ya kuma dauki bangare a wani taro da yan jirudu da ya gabatar a birnin Tokyo na kasar Japan. A cikin jawabin da yayi wa yan jaridu Grossi ya Iran tana ‘gasa makamashin Uranium har zuwa kasha 60% wanda ya kusan kaiwa ga makamashin Nukliya, sannan bata bawa hukumar IAEA hadin...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Saudiyya ta kira shugabannin kasashen Larabawa na yankin Gulf da kuma Masar da Jordan a wani taron domin tattauna batun Gaza. Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ne ya gayyaci shugabannin a taron na gobe Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyar SPA ya ruwaito. Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yakin Gaza da kuma sake gina Zirin a wani mataki na tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shakatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan korar mutanen Gaza zuwa wasu wurare. Saudiyya ta ce taron na ranar Juma’a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta. Yin hakan ya na nuna yanda al-amarin musayar Fursinoni yake da muhimmancin ga falasdinawa. Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen larabawan yankin tekun pasha a birnin Muscat na kasar Oman a jiya Lahadi. Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya kara da cewa; ya zama wajibi a ji sauti daya daga kasashen musulmi na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falasdinu. Arakci wanda ya yi ishara da ganawa ta farko da aka yi a matakin ministocin kasashen kungiyar larabawa...
kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika wasu ‘yan Isra’ila uku da ta yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross a wani musayar fursunonin da aka sako Falasdinawa 369 a wata musanya ta baya-bayan nan a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. An saki ‘yan Isra’ilan uku a birnin Khan Yunus da ke kudancin Gaza, inda Isra’ilawan suka yi jawabi ga jama’a kafin mika su ga kungiyar agaji ta Red Cross. Sakin dai shi ne na shida tun bayan da tsagaitawar ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu bayan fargabar da ake yi a makon da ya gabata cewa yarjejeniyar ta kusa rugujewa bayan da Isra’ila ta ki ba da isassun kayan agaji a Gaza. Yawancinsu...

Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...

Kungiyar Hamas Ta Bukaci Al’ummar Duniya Ta Goyi Bayan Al’ummar Falasdinu Kan Batun Neman Korarsu Daga Kasarsu
Kungiyar Hamas ta yi kira ga ƙungiyoyin duniya da su fitar da matsayinsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi don yin watsi da batun neman tilastawa Falasdinawa yin hijira daga Zirin Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira ga al’ummar Falastinu, al’ummar Larabawa da al’ummar musulmi da dukkan ‘yantattun kasashe a duk fadin duniya da su fito domin gudanar da gagarumar zanga-zanga da tarukan goyon bayan al’ummar Falasdinu gami da hadin gwiwa a dukkanin birane da wuraren taruwar duniya, domin jaddada yin watsi da yin Allah wadai da shirin korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Laraba ta ce: Ranakun Juma’a, Asabar da Lahadi masu zuwa...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
Kazalka, matsalar ta sanya wasu iyalai da dalibai da dama a kasar yin kokarin jurewa matsin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta, wanda hakan yak e kuma kara zamowa, babbar barazana ga rayuwarsu. Bisa fashin baki da rahoton ya yi ya nuna cewa, a shiyoyi shida na kasar, banbancin hauhawan farashin na kayan abincin, ya sha ban ban, inda a yakin Kudu Maso Yamma, lamarin na hauhawan farashin kayan abincin, ya fi yin kamari.
Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata. Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer Ba...

Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyin Bayan Falasdinawa Bayan Tattaunawar Trump Da Natanyahu Dangane Da Gaza
Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”. Maganganun Trump a baya-bayan nan, dangane da yankin Gaza dai, ya jawo cece-kuce da dama kan al-amiran a duniya, A birnin Washington dai mutane sun yi ta kawo batun kare hakkin ‘yan kasa’ da kuma tauya hakkin wata al-umma wacce ta yi shekarun fiye 75 tu na neman hakkinta na komawa kasarta, daga kasashen da suke rayuwa, rayuwa irin ta yan gudun hijira na lokaci mai tsawo. A lokacin...
Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da tsawaita wa’adin karɓar kuɗin aikin Hajjin bana. NAHCON ta ce daga yanzu zuwa 10 ga watan Fabrairu ƙofa a buɗe take ta ci gaba da karɓar kuɗin kujera ga maniyyatan da ke son sauke farali a bana. Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka Ana iya tuna cewa, da misalin ƙarfe goma sha biyun daren ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025, ne wa’adin biyan kuɗin kujerun aikin hajjin bana ya cika. Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce tsawaita wa’adin wata dama ce ga maniyyatan da ba...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa. Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.” A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai...
Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi. Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama, akan hare-haren na rundunar kai daukin gaggawa tare da kakkabo da dama daga cikinsu. Wadannan hare-haren dai sun faru ne jim kadan bayan wata ziyara da shugaban majalisar shugabancin kasar ta Sudan janar Burhan Abdulfattah ya kai garin “Um-Ruwabah’ wanda sojojin Sudan din ba su dade da kwato shi ba. A cikin makwannin bayan nan dai sojojin na Sudan suna cigaba da samun nasara akan...
Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga karatu har na tsawon shekaru biyu. Labarin ya nakalto hukumomin Jami’ar na cewa, wadannan daliban sune suka shirya zanga-zanga a cikin Jami’ar, inda suka maida ita cibiyar goyon bayana Falasdinawa a Gaza. Ta kuma kara da cewa wannan kin kabilar samiyawa ne. Jami’ar ta sa an kama wasu malaman jami’ar, ta kuma dakatar da wasu daga karantarwa, sannan wasu kuma an koresu daga jami’an kwatakwata....
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im. Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...