Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Matakin Isra’ila Na Hana Shigar Da Kayan Agaji A Gaza
Published: 3rd, March 2025 GMT
Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.
Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka” na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar “ta yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na hana agajin jin kai da mashigin da ake amfani da shi wajen kai agaji.”
Ma’aikatar ta ce “wadannan ayyukan sun saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta, dokar jin kai ta kasa da kasa, Yarjejeniyar Geneva ta Hudu, da dukkan ka’idojin addini.”
Yarjejeniyar Geneva ta hudu da aka amince da ita a shekarar 1949 bayan yakin duniya na biyu, ta ta’allaka ne kan ba da kariya ga fararen hula, ciki har da yankunan da aka mamaye.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta dauka na
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kiyaye Girmama Kasashen Tsibirai Na Yankin Tekun Pasifik
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye girmama kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik a fannoni 4.
Firaminista Brown ya yi nuni da cewa, kasarsa ta tsibiran Cook ta dora muhimmanci ga girmamawar da Sin ta nuna mata, kasar Sin ta kiyaye yin hakan tun da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. A sakamakon girmama kasar tsibiran Cook da Sin ta yi, sauran kasashen duniya sun fara kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kasar tsibiran Cook. Kasar tsibiran Cook ta nuna godiya ga kasar Sin kan wannan batu, kuma ita ma tana girmama kasar Sin. Duk yadda kasa ta kasance babba ko karama, ya kamata kasashe su nuna girmamawa ga juna, hakan shi ne tushen raya dangantakar dake tsakaninsu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp