2025-04-03@21:21:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1155
«Isra ila ta dauka na»:
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Gobara ta lalata wani ɓangare na gidan Ado Bayero Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025. Da yake jawabi gabanin miƙa su a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su a arewacin tekun Bahar Maliya. Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin...
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai inganci. Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da...
Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan. “Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su ji ba gani ba.” Sai dai hukumomin ‘yansanda a jihar sun ki cewa komai kan lamarin. Majiyar ‘yansandan ta yi ikirarin cewa, “tunda ana ci gaba da aikin hadin gwiwa na sojoji a yankin, ‘yansanda ba su da hurumin yin magana kan ci gaban tsaro a yankin. Da aka tuntubi runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya ta mika wakilinmu ga rundunar ‘Operation...
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Rahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba. INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ba ta cika sharuɗɗan da ke cikin sashi na 69(a) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ba.” INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha Sai dai hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani kan wannan ci gaba nan ba da...
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025. Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya. Ƙungiyoyin sun...
Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza. Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya. Ministan alakar kasashen waje da aiki tare, Ronald Lamola wanda ya yi Magana da ‘yan jaridar kasar tasa, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi kasar ta janye karar da ta shigar a gaban kotun kasa da kasa ta manyan laifuka. Haka nan kuma ya ce; Neman yardar Amurka ba shi ne aikin da Afirka ta Kudu ta sanya a gaba ba, abinda yake gabanta...
Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi. Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa...
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan asarar rayuka sanadiyyar wadannan hare-haren na’yan sahayoniya. A shekaran jiya Talata ma dai sojojin na mamaya sun kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beirut hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu. Hari na shekaran jiya shi ne irinsa na biyu a cikin unguwar Dhahiya tun bayan tsagaita wutar yaki. Haka nan...
Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums, Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din ta almayadin cewa, an sami wadanda su ka jikkata. A garin Humah, jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren har sau 10, sannan kuma jiragen sun dauki lokaci mai tsawo suna shawagi a samaniyar birnin wanda ya yi sanadiyyar harin. A birnin Hums, kafafen watsa labarun yankin sun ce an ji karar fashewar abubuwa masu karfin gaske a kusa da filin saukar jiragen sama...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba. Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar. Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar. Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu). Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”, kana mataki mai karfi da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin. Kamar yadda aka sani, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, wanda ba ta taba zama kasa ba, kuma ba zai taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya. Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace. Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi. Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi. Shugaban...
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki. Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, mai yuwa yayi tasiri a barazanar da kasar Iran take fuskanta na kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar. Aragchi ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya ne, kuma har yanzun kasar Iran tana kan bakanta na aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya don kare hakkinta na mallakar fasahar makamashin nukliya wannan dokokin kasa da...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya. A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin. Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin...

Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Yemen na fada a jiya Talata, kan cewa sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a wadan nan hare-hare kan USS Harry S.Truman kuma saun sami bararsu kamar yadda aka tsara. Labarun ya kara da cewa yakin yana ci gaba tsakanin bangarorin biyu. Kuma wadan nan hare hare sun zo ne saboda...
Rahotanni na cewa Allah Ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sunusi ya rasuwa. Wata sanarwa da ta fito daga cikin iyalansa ta tabbatar da rasuwar, inda ta ce nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi masa jana’iza. Alhaji Abbas Sanusi kawu ne ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas. Marigayin shi ne Wamban Kano babban ɗan majalisar Sarki kafin daga likafar sarautarsa zuwa Galadiman Kano.
Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, agogon kasar. A yayin bikin bayar da gudummawar kudi ga wadanda girgizar kasar ta shafa a birnin Nay Pyi Taw a yau Talata, shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya ce, mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar wacce ta afku a kasar a ranar Jumma’a, sun kai 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana 441...
Alƙaluman Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce Isra’ila ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 cikin kwanaki 10 da suka gabata a hare-haren da suke ci gaba da kai wa sassan Gaza. Alƙaluman da UNICEF ta fitar ta ce a jimilla ƙananan yara fiye da dubu 15 ne Isra’ilan ta kashe cikin kusan watanni 18 da ta shafe tana yiwa yankin na Gaza luguden wuta, kuma daga lokacin da ƙasar ta katse yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninta da Hamas ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 tare da jikkata 609. Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola...
Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL A jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar...
Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi. Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin. HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi “A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na...
Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib. Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba kuma za mu yi taraddudin daukar dukkanin matakan kare kai ba, akan jiragen ruwan abokan gaba a nan gaba. Kwanaki biyu da su ka gabata, sojojin Yemen sun kai wasu hare-hare akan jirgin dakon jiragen yaki na “Trauman’ da sauran jiragen yakin da suke ba shi kariya. Sojojin na Yemen suna kuma ci gaba da kai wa HKI hare-hare da jiragen sama marasa matuki da...
Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata. Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a Minna jihar Neja. Malam Jibrin Baba Ndace ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ya zama wajibi saboda nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu ya kasance nasarar mu baki daya, don haka akwai bukatar mu kasance cikin nasara. Daga nan sai ya mika gaisuwar ban girma ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya na bikin sallah karama tare...
Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah. Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr. Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr. Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka. Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya. Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar. Da yake...
Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari. Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. Jiragen yakin na HKI sun yi shawagi a kasa-kasan birnin Beirut kafin aji karar fashewar abubuwa masu karfi. Kafafen watsa labarai sun ambaci cewa jiragen sun kai harin ne akan wani dogon gini a cikin unguwar. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 3 ne su ka yi shahada,yayin da wasu 4 su ka jikkata. Masu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci. A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a yankin inda ya ce a yau wani bangare na duniyar musulmi ya samu munanan rauni. ‘’ Falasdinu ta ji rauni, Lebanon ma ta ji rauni, inji shi. Laifukan da aka aikata a wannan yanki ba a taba ganin irinsa ba, an kashe yara kusan 20,000.” Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci a hankali tare da daukar nauyin da ya rataya a...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin. Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana. Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin...
A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin. Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr. Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto...
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo. Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari. Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar Zazzau Da yake miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin, Sarkin ya ce “mun ga an ɗauki mataki kan yanayin da ake ciki a Jihar Edo. “Saboda haka muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka bayan kammala bincike don ba wani dalili ka kashe mutum ba tare da wani haƙƙi ba....

Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a kokarin da kwamitin ya yi na kiyaye muhalli. Dole ne a nace ga jagorancin da JKS ta bayar a wannan bangare, da ma sauke nauyin dake wuyan hukumomin wurare daban-daban karkashinta. Taron ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kara karfin sa ido a siyasance, da mai da hankali kan yadda ake tabbatar da manufofi da tsare-tsaren kwamitin, ta yadda za a ba da tabbaci...
A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan Tehran dubban daruruwan mutanen suka fito zuwa babbar masallacin Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran inda suka gudanar da sallah mai raka’o’I biyu tare da jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khamina’e. Duk da cewa ana samun babbanci tsakanin musulmi kan ranar ajiye azumun amma akalla ba wanda zai yi azami kasa da kwanaki 29. A cikin watan dai, musulmi...

Yawan Kayayyakin Da Aka Yi Hada-hadarsu A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Sin A 2024 Ya Ci Gaba Da Kasancewa Na Farko A Duniya
Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya. Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu. Amma a wani bangare a cikin wannan Ramadan, duk tare da jin dadin da muka samu, amma watan yana tattare da dacinsa, kissan mutanen Falasdinu, tare da goyon bayan Amurka. Kasashen yamma suna tuhumar Iran tana amfani da sojojin wadanda suke wakiltantan a abinda yake faruwa a yankin. Amma gaskiyar al-amarin sune suke da wakili a wannan yakin, kuma itace HKI, wacce taek wakiltansu a ayyukan ta’addanci da take yi...
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1. Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba. Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta...

Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka amsar wasikar da ta aiko mana, inda a cikinta, muka kara jaddada cewa babu wata tattaunawa kai tsaye da Amurka, kuma an tura wasikar ta inda na Amurkan ta fito wato ta kasar Omman. Don haka muna jiran matakan da Amurka zata dauka a kan amsar. Daga karshe shugaban ya kammala da cewa duk wata mu’amala da gwamnatin kasar Amurka ba zai taba yiyuwa kai...
Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan shekara 4 ya yi kururuwa, inda ya kira ’yan sanda bayan mahaifiyarsa ta shanye masa ice cream dinsa. Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Al’amarin ya faru ne a cikin a garin Mount Pleasant, Wisconsin — mai nisan kilomita bakwai, yamma da Racine — lokacin da yaro dan shekara 4 ya...
Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har 13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har da Yankunan Malikah da Sarf na birnin San’aa babban birnin kasar. Wasu kafafen yada labaran kasar Yemen sun bayyana cewa, kafin haka jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kan kasar ta Yemen wadanda suka kai ga shahadar fararen hula 12 da kuma raunata wasu 2 a birnin San’aa babban birnin kasar. Washington ta bada sanarwan cewa ta na kai hare-haren don tabbatar da tsaron...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian ya tabbatar da cewa an isar da martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump ta hanyar Oman. Ya jaddada cewa, yayin da Iran ta yi watsi da tattaunawar kai tsaye, ba ta taba rufe kofar yin shawarwarin kai tsaye ba matukar dai aka cimma wani abu da bai yi karo da manufofin Iran ba. Ya kara da cewa, “Kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin. A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren soji da Amurka ke kaiwa sassa daban-daban na kasar Yeman, wanda ke sanadin mutuwar fararen hula da kuma lalata kayayyakin more rayuwa. Ya kara da cewa: Hare-haren da sojojin Amurka suke kai wa kasar Yamen, wanda ya zo daidai da irin yadda gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmaanci. Kamfanin dillancin labarum “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunis ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Lrabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude...
Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24. A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon jiragen yakin na Amurka da kuma sauran jiragen da suke ba shi kariya a cikin tekun “Red Sea”. Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce; Sun kai wa jiragen na Amuka hare-hare ne da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta. An shiga makwanni na uku kenan da sojojin na Yemen suke mayar da martani akan hare-haren da sojojin Amurka da...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a Gaza, Khalil al-Hayyam, ya ce ƙungiyar ta amince da ƙudirin da masu shiga tsakani daga Masar da kuma Qatar suka gabatar. Miji ya kama matarsa da kwarto ta na’urar drone Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Ofishin firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ma ya ce ya karɓi tayin, amma ya gabatar da nasa tayin ”wanda ya ci karo da wanda masu shiga tsakanin suka gabatar masa, a...
Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya bayyana cewa ware ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan wata hikima ce ta jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ruhullah Alkhomaini(q) wanda ya dace da hakan kan musulmi a kan wannan al-amari. Kuma tare da yardarm All…ana ci gaba da samun nasara a kan wannan manufar. Sheikh Kasim ya kara da cewa duk tare da gagarumin taimakon da HKI take samu daga kasashen yamma...
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan: Kabbarori: Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi. Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd. Zakkar Kono: Wajibi ne ga duk wanda...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa. Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015. An ga watan Sallah a Saudiyya Dalilin da Aminu Bayero ba zai iya jagorantar hawan Sallah ba — Kurawa Buhari ya bayyana hakan a saƙonsa na taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, wanda ya cika shekaru 73 a doron ƙasa. Sanarwar da mai magana da yawun Buhari, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, ta ce tsohon shugaban yana alfahari da alaƙarsa da shugaban ƙasar na yanzu. Sanarwar...
Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki. Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa sun yi luguden wuta kan motocin daukar marasa lafiya a zirin Gaza, inda Hamas ta yi Allah wadai da harin” da ya janyo asarar rayukan ma’aikatan ceto. Rahotanni sun ce an gano gawarwakin ma’aikatan ceto goma sha biyar, wadanda aka binne a kusa da motocinsu, wadanda suka lalace gaba daya sakamakon harin na Isra’ila. Har ila yau kungiyar ta jaddada cewa kai hare-hare da gangan...
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba. Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.
Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan. Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata. Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda suk suka ayyana dokar ta baci a ranar Juma’a. Tuni kasar Myanmar ta nemi taimakon kasashen duniya da kuma kungiyoyi don agazawa wadanda girgizar kasarta shafa. Kasar Iran ta ce a shirye take ta taimakawa kasashen biyu da girgizar kasar ta shafa. A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya fitar yau Asabar ya ce Iran a shirye take ta shiga...
Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu. Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia. Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu. “Kamar yadda aka...
Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka. Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar Mutum 14 sun shiga hannu kan kisan ’yan Arewa a Edo Bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Juma’a, ya nuna matar tare da wata ƙawarta suna tunkarar wajen da aka kange, inda jami’an tsaro suka hana su wucewa. Sai dai matar ta fusata, tare da marin ɗan sandan,...
Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...

Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can. Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen...
Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma tsawon mita 180. Sannan Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025. Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka sare su, sannan aka banka musu wuta a abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin abin “aikin rashin imani” na tashin hankali bisa la’akari da bambancin kabilanci. A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na gidauniyar, Injiniya Dakta Abubakar Gambo Umar, ya fitar, gidauniyar ta nuna damuwarta kan yadda hare-haren da ake kai wa ‘yan Arewa ke ƙaruwa a wasu sassan Kudancin kasan nan, tana...
Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar daurin talala a cikin gidansa. Babban magatakardar MDD ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar ta Sudan ta Kudu da su ci gaba da riko da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya,inda ya ce: “ A dawo da gwamnatin hadin kan kasa, da aiki da alkawullan da aka yin a zaman lafiya da sulhu, da hakan ne kadai hanyar dawo...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne. Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi. Har ila...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu. A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano...
Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam (JNI) , ta raba kayayyaki da sauran kyatuttukan Sallah ga marayu 50 gabanin bikin Sallah ƙarama a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. An gudanar da bikin ba da tallafin ne a harabar makarantar sakandare ta Bulabulin da ke birnin na Maiduguri. Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin daraktan kungiyar JNI reshen Maiduguri, Malam Ibrahim M. Bello, ya jaddada muhimmancin tallafa wa mabuƙata, yana mai jaddada cewa wannan shi ne babban burin ƙungiyar. Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin da su yi amfani da kyaututtukan domin biyan...
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau. An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny. A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza. An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da...
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai. Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta...
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun 2025, wanda ya kai yawan Ganga 1,465,006 da ake hakowa a kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, da hauhawar farashin kayan abinci da man fetur, da bala’in yanayi, da kuma matsugunan jama’a, ya sa miliyoyin mutane ke fafutukar samun abinci mai gina jiki. Rahoton UNICEF ya kara bayyana cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Nijeriya, kusan miliyan 11, na fama da matsanancin rashin abinci, wanda hakan ya sa kashi 50 cikin 100 na ka fuskantar barazana ga...
Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025. Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi. Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka...
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...

Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha cikin...

Iran Ta Bada Amsa Ga Wasikar Shugaban Kasar Amurka Ta Gayyatar Kasar Zuwa Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal Trump yana son janye tallafin da kasarsa ke bayarwa don wannan shirin, wanda yake yakar cutar Malaria da wasu cututtuka a wadannan kasashe. Labarin ya kara da cewa za’a dakatar da ayyukan samar da magunguna da alluran riga kafa har guda 5,341 idan an dakatar da tallafi, wanda yake cinye dalar Amurka biliyon 75 a ko wace shekara. A halin yanzu dai hukumar ta USAID ta bada dalar Amurla biliyon 48,...
A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya. A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil da mata da maza, kowanne na ƙoƙarin sayen sabbin kaya. Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano Kayayyakin da aka fi saya sun haɗa da atamfofi, mayafai, adire, dogayen riguna, leshi, sarƙoƙi, yadi, da sauran kayan ado. Kasuwanni sun cika maƙil da masu...