HausaTv:
2025-04-28@22:25:57 GMT

Iran : Samar Da Kasashe Biyu Baya Tabbatar Da ‘Yancin Falasdinawa

Published: 8th, March 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo.

Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya mantawa da shi ba.

Araghchi ya kara da cewa, tare da mutunta ra’ayoyin wasu kasashe ‘yan’uwa kan batun samar da kasashe biyu, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta na kan ra’ayinta na cewa, wannan mafita ba za ta kai ga tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu ba,” in ji Araghchi, yana mai jaddada matsayin Iran na bayar da shawarar kafa wata kasa ta dimokiradiyya wacce ke wakiltar dukkan ‘yan Falastinu.

Araghchi ya kuma yi kakkausar suka ga yunkurin gwamnatin Amurka na tilasta al’ummar Gaza kaura,” yana mai dagnata hakan da keta dokokin kasa da kasa, da yarjejeniyar Geneva ta hudu.”

Ya kuma bukaci kasashe mambobin kungiyar OIC da su aiwatar da irin wadannan matakai a matsayin wata hanya ta tursasawa gwamnatin sahyoniyawan ta dakatar da laifukan da take aikatawa kan al’ummar Gaza da sauran kasashen yankin.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Araghchi ya

এছাড়াও পড়ুন:

 Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Nasarar Nguema A Zaben Shugaban Kasa

Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi.

Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.%  da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara.

Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba.

Magoya bayan Nguema sun yi bikin  hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki.

Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin sake gina cibiyoyin gwamnatin kasar da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Gabon dai kasa ce mai arzikin man fetur, sai dai kuma mafi yawancin mutanen kasar suna rayuwa a cikin talauci.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
  • Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa
  • Daidaikun Kasashe Za Su Kara Karfi Idan Suka Hada Hannu Tare
  • Karon Farko Sin Ta Fi Samar Da Wutar Lantarki Ta Aiki Da Makamashin Nukiliya A Duniya
  •  Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Sun kashe ‘Yan Hijira Da Dama A Yankin Tekun Maliya
  • Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
  • ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
  • Gwamnan Babban Bankin Sin: Harajin Amurka Ya Jefa Kasuwanni Da Kasashe Masu Tasowa Cikin Hadari
  • Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ke Ci Gaba Da Rike Kambun Kasa Na Mafi Yawan Samar Da Danyen Mai A Afirka — OPEC
  •  Kotun Tsarin Mulki Ta Gabon Ta Tabbatar Da Nasarar Nguema A Zaben Shugaban Kasa