2025-03-09@12:10:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9
«Araghchi ya»:
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna da kekyawar kariya daga makamai. Don haka da sauki makiyammu ba zasu cutar da cibiyoyin ba. Ministan ya bayyana haka ne a taron kasashen musulmi na OIC wanda aka gudanar a birnin Jedda na kasar Saudiya a yau Asabar. Ya ce iran zata ci gaba da neman fahintar juna ta hanyar diblomasiyy, Amma idan sun dage zasu yi amfani da karfi to Iran a shirye...
Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa. “A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane yake: ba za mu yi shawarwari cikin matsin lamba, barazana, da takunkumi ba.” “Saboda haka,” in ji ministan harkokin wajen Iran, “babu yuwuwar yin shawarwari kai tsaye tsakaninmu da Amurka kan batun nukiliya matukar dai ana ci gaba da yin amfani da mafi girman matsin lamba a yadda take a halin yanzu.” Misra Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da...
Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin da ya yi a ranar Litinin, a babban taro na 2025 kan kwance damara, a hedkwatar MDD dake Geneva, Mr. Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da MDD da su ba da fifiko kan batun kawar da makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa “dole ne kasashen duniya su tilastawa Isra’ila bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi (NPT) don kawar...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen larabawan yankin tekun pasha a birnin Muscat na kasar Oman a jiya Lahadi. Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya kara da cewa; ya zama wajibi a ji sauti daya daga kasashen musulmi na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falasdinu. Arakci wanda ya yi ishara da ganawa ta farko da aka yi a matakin ministocin kasashen kungiyar larabawa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a yau litinin, a birnin Hamedan. Imam Khumaini (q) ne ya jagoranci kasar zuwa ga nasara a shekara 1979, Juyin juya halin da ya kawo karshen Sarautar Muhammad Reza sha Pahlavi. Ministan ya kara da cewa Jagoran juyin juya halin musulunci ya rika ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Iran kan wannan batun, sannan abinda ya fada shi ne duk wani mai...
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata matsin lamba kan kasar ta Donald Trump za ta cutura. Iran dai ta caccaki matakin da shugaban AMurka ya dauka ind aya sanya hannu kan umurnin sanya sauraren matakn matsin lamba kan Tehran a game da shirinta na nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana a wani sako a X cewa siyasar matsim lamba ta gaza a baya, kuma za ta ci karo da tsayin daka mai karfi. Abbas Araghchi ya kara da cewa abu ne mai sauki a samu hanyoyin tabbatar da cewa Iran ba ta nemi kera makamin nukiliya ba. To amma a sa’i daya kuma wajibi ne Amurka da kasashen yammacin duniya su dage takunkumin karya tattalin arziki da suka...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya. Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma ya zauna da shugaban kasarta. A wani bangare na maida martanin Aragchi ya bayyana cewa dangane da fadinsa, ba zai taba amincewa Iran ta mallaki makaman Nukliya ba, yace Iran mamba ce a yarjeniyar NTP, a kuma hukumar makamashin nukliya ta IAEA. Zasu lamunce masa kan cewa Iran bata bukatar makaman nukliya. Amma duk da haka Iran ba zata taba sayar da hakkinta na mallakan...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...

Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba. Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda...