HausaTv:
2025-04-03@06:02:00 GMT

Tawagar ECOWAS Ta Fice Daga Guinea-Bissau Bayan Barazana Daga Shugaban Kasar

Published: 3rd, March 2025 GMT

Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.”

Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa.

ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci.

Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.

 Amma daga bisanio ya zarge su da wuce gona da iri ta hanyar tattaunawa da wasu shugabannin ‘yan adawa.

Ita dai tawagar ta ECOWAS, an dora mata alhakin samar da mafita ta samar da zaman lafiya a kasar Guinea-Bissau, ta hanyar mai da hankali kan cimma matsaya ta siyasa kafin zaben da aka shirya yi a ranar 30 ga watan Nuwamba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Umaro Sissoco Embalo ke shiga takun tsaka da tawagar ECOWAS a kasar sa ba. A lokacin da ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa tare da goyon bayan jami’an tsaro, ya kori mambobin ECOWAS da ke kasar tare da tare da cewa bai maraba da wakilin kungiyar.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.

 

Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.

 

Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

 

Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban kasar na ciyar da kasar gaba.

 

“A madadin ‘ya’yan jam’iyyar APC na Zamfara da al’ummar mazaba ta, na mika sakon taya murna ga shugaba Tinubu na cika shekaru 73 da haihuwa. “Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya kara masa shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, da wadata, da kuma hikimar da zai jagoranci kasar nan ta hanyar da ta dace. Za mu ci gaba da yi masa addu’ar samun nasara a matsayinsa na shugaban kasa,” inji shi.

 

 

COV/AMINU DALHATU

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Tinubu Ya Tube Kyara A Matsayin Shugaban Kamfanin NNPC Ya Kuma Sannan Ya Maye Gurbinsa
  • Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC
  • Ma’aikatan Kasar Sin Sun Ceto Mutum 8 Zuwa Yanzu A Myanmar
  • Ana Zaman Dar-dar A Kasar Zimbabwe Saboda Shirin Zanga-zangar Tsofaffin Sojaji
  • Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
  • Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF
  • Tawagar Aikin Ceto Ta Kasa Da Kasa Ta Kasar Sin Ta Isa Myanmar
  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris
  • Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi
  • Kasar Sin Ta Jaddada Bukatar Karfafa Cinikayya Da Ketare Tare Da Fadada Bude Kofa