2025-04-19@09:25:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 112

«Gwamna Inuwa Yahaya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu yawa, an baje kolin su a yayin da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta gabatar waɗanda ake zargin a ranar Juma’a Ga wasu hotunan kayan da aka ƙwato:          
    ’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa  da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu tara, ciki har da mata hudu. Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da fargaba. Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa A kauyen Birnin Yero, ’yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza.  Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
    Wani jami’in fadar mulkin Amurka ( White Hosue) ya nakalto shugaban kasar Amurka Donald Trump yana fada a yau Laraba cewa, shugaban kasar Amurkan ya rattaba hannu akan wata doka ta fada da kin jinin yahudawa da ta kunshi cewa duk wasu dalibai ‘yan kasashen waje da masu ci rani a kasar,  idan su ka shiga cikin Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa to za a kore su daga Amurka. Dokar da Trump din yta sanya hannu a kanta ta kuma kunshi bayar da umarni da ma’aikatar shari’ar kasar aka cewa ta bi diddigin duk masu barazanar ta’addanci, da ruruta wutarsa, da mabarnata dake cutar da yahduawan Amurka.” Haka nan Trump ya ce zai soke izinin shiga cikin kasar ta Amurka...
    Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
    Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
    Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu. SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai. Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan...