‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’
Published: 4th, March 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang.
A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar.
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel saɓanin rahoton da ke cewa masu garkuwa da mutane ne suka kashe shi.
Adeh ta ce rasuwar Mista Parradang na zuwa ne bayan ya yi wata baƙuwa mace da ta kai masa ziyara ɗakin otel ɗin ya kama na kwana guda.
“Bisa rahotanni da ke cewa an yi garkuwa da tsohon jami’in Hukumar Shige da Ficen sannan daga bisani aka kashe, muna so mu tabbatar da gaskiyar lamarin.
“Abin da ya faru shi ne da misalin ƙarfe 12 na ranar 3 ga watan Maris, Mista Parradang ya ziyarci Otel ɗin Joy House da ke yankin Area 3 na Abuja a wata baƙar mota ƙirar marsandi.
“Ya biya Naira 22,000 kuɗin kwana ɗaya. Sai dai bayan wani ɗan lokaci ya buƙaci ɗaya daga cikin masu aiki a otel ɗin cewa ya yi baƙuwa yana so a rako ta ɗakin nasa.
“Matar da ta kai masa ziyara ta bar otel ɗin da misalin ƙarfe 4 na yammacin wannan rana.
“Har bayan tafiyar wannan mata Mista Parradang bai fito daga ɗakin ba, sai washegari da misalin ƙarfe 4 na asubahi wani abokinsa mai aikin ɗamara ya biyo sawu yana cigiyarsa har otel ɗin.
“Yana zuwa kuwa aka garzaya da shi [abokin nasa] har ɗakin, inda aka tarar da gawarsa zaune a kan kujera.
“Nan da nan aka sanar da ofishin ’yan sanda na Durumi kuma suka zo suka ɗauki hotuna da sauraren ababen da su taimaka musu wajen gudanar da bincike.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, a halin yanzu an miƙa gawar Mista Parradang zuwa Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin ɗauka matakan da suka dace “yayin da ma’aikatan otel ɗin ke ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai a binciken da suka gudanarwa.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: David Shikfu Parradang Hukumar Shige da Fice Hukumar Shige da Mista Parradang
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun hallaka mutum 6 a ƙauyukan Kebbi
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata.
Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu.
Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren DankaliWannan ta’addanci ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba.
Gwamna Nasir Idris ya bayar da tabbacin inganta a tsaro jihar.
Ganin yadda mutane ke cikin tsoro, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar jaje ƙauyukan a ranar Asabar.
Ya tabbatarwa da al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar tsaro, musamman a yankin Kebbi ta Kudu.
Gwamnan ya bayyana cewa mafi yawan hare-haren da ake fuskanta a Kebbi na zuwa ne daga maƙwabtan jihohi.
“Tun daga lokacin da muka hau mulki, muna ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar tsaro, kuma muna samun ci gaba.
“Rashin ɗaukar matakin gaggawa daga jami’an tsaro a wasu maƙwabtan jihohi yana bai wa ’yan bindiga damar kutsowa cikin yankunanmu suna kai hari,” in ji Gwamnan.
Ya buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
A yayin ziyarar, Gwamna Nasir Idris ya bayar da tallafin miliyan 10 ga iyalan waɗanda aka kashe.
Haka kuma, ya bayar da umarnin gina Masallacin Juma’a da kuma bohol guda biyu da ke amfani da hasken rana a ƙauyen Rausa Kade.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Arewa, Hon. Sani Aliyu Tela, ya jinjina wa Gwamnan bisa wannan kulawa.
Ya bayyana cewa harin ya faru ne a daren Alhamis, inda ’yan bindiga suka kai farmaki domin satar dabbobi.
“Sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, suka harbi mutum ɗaya a Bagiza. Mun yaba da kulawar da kake ba mu,” in ji shi.
Jama’a dai na fatan matakan da gwamnati ke ɗauka za su kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi yankin.