2025-03-04@23:04:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14
«Mista Parradang»:
Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje. Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS). Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...

A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja. Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar. Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi. Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda...
Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da yadda za a gudanar da bincike kan mutum-mutumin inji, yayin ba da izini gare su. Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi yadda ya kamata. Bayanin ya nuna cewa, an tsara ka’idar bisa bukatun tsoffi a fannonin samun kulawa cikin harkokin yau da kullum, da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan tsara mutum-mutumin...
Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho. Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu. “Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da...
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida A cewarsa, samun ‘yancin cin gashin kai ba yana nufin cewa shugabannin ƙananan hukumomi ba za a iya hukunta su ba idan sun aikata ba daidai ba. “Shugabannin ƙananan hukumomi ba su da kariya a tsarin mulkin ƙasa. Idan aka samu rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen jama’a,...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu. A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ruwaito cewa, taron karramawar, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati dake Dutse Babban Birnin Jihar, ya hada da wadanda suka ci gajiyar shirye-shiryen gwamnati da suka hada da J-Teach, da J-Agro, da J-Health, da J-Millionaires, da sabbin likitocin da aka dauka aiki a bangaren lafiya. A yayin taron, kowanne rukuni ya mika lambar yabo ga Gwamna Umar Namadi don nuna...
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya. A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Mu’azu Elezah ya nuna bukatar hukumar ta kara kaimi wajen yayata wa al’umma ayyukanta domin zuwa yanzu mutane kadan ne suka san kasancewar hukumar da ayyukanta a sassan kasar nan, “Ya kamata ku zuba jari sosai wajen fadakar da al’umma irin ayyukanku, da kuma yadda mutane za su amfana daga tallafin yaki da sauyin yanayi na majalisar dinkin dunuya” in ji shi
Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin yaki na ” Drone” ya cilla kan wata mota a kan titi a garin Jarjoun da Iqlim Attuffah inda suka kashe mutane 3 sannan wasu kusa da motar guda 4 sun ji rauni. Majiyar yahudawan ta bayyana cewa sun kashe wani kwamandan kungiyar Hizbullah ne, amma shaidu a yankin sun tabbatar da cewa duk wadanda HKI ta kashe ba mayakan kungiyar Hizbullah ne ba. Wannan...
Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi. Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin. Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta. ...

Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026. Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan...
Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci...