Aminiya:
2025-03-23@03:56:13 GMT

Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa

Published: 12th, February 2025 GMT

Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar.

Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu.

An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC

Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya.

Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi.

Yawancin ’yan majalisar sun goyi bayan ƙudirin, inda suka ce hakan zai ƙara wa gwamnati kuɗin shiga tare da bunƙasa tattalin arziƙi ƙasa.

Sai dai wasu, kamar ɗan majalisa Sada Soli, sun nuna damuwa kan wasu sassa da ba a fayyace su ba a ƙudurorin, waɗanda ka iya haifar da matsaloli a nan gaba.

Duk da haka, bayan tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da ƙudirin a karatu na biyu ta hanyar kaɗa ƙuri’a.

Mataki na gaba shi ne miƙa ƙudirin ga kwamitocin majalisar domin ƙara yin nazari, tare da gyara matsalolin da ke tattare da ƙudirorin.

Idan aka amince da shi, za a gabatar da shi a karatu na ƙarshe kafin ya zama doka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan majalisa Dokokin Gyaran Haraji Majalisar Wakilai Muhawara

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Kira Jakadun Kasashen Jamus da Butaniya Zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje Don Jan Kunnensu

Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta Iraki.

Sannan ta bayyana yadda kasar Burtania ta dade tana adawa da JMI, daga ciki har da goyon bayan da kasashen biyu suke bawa HKI a kissan kiyashin da take wa falasdinawa a gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Chelle Ya Fara Da Ƙafar Dama A Super Eagles 
  • Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Wike Ya Kwace Filaye 4,794 A Abuja Saboda Rashin Biyan Kudin Ka’ida
  • Ribas: Ba mu karɓi sisin kwabo domin amincewa da dokar ta baci ba – Majalisar Wakilai
  • Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Zama Ƴar Amshin Shata — Kwankwaso
  • Gwamnati Ta Jaddada ƙudirin Kare ‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki Da ‘Yancin ‘Yan Jarida
  • An kori shugaban hukumar leken asiri ta cikin gidan Isra’ila
  • Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
  • Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas
  • Iran Ta Kira Jakadun Kasashen Jamus da Butaniya Zuwa Ma’aikatar Harkokin Waje Don Jan Kunnensu