NHIS: Kotu ta ɗage bayar da belin Farfesa Yusuf zuwa 27 ga Fabrairu
Published: 13th, February 2025 GMT
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa.
A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.
A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016.
Ana zargin ya amince da sayen mota kan kuɗi Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a kasafin kuɗi.
Hakazalika, EFCC ta ce Yusuf ya bai wa gidauniyar GK Kanki Foundation kwangilar bayar da horo ta Naira miliyan 10.1ba tare da bin ƙa’ida ba, duk da cewa mutum 45 kaɗai aka horar maimakon 90 da aka bayyana.
Bugu da ƙari, ana tuhumarsa da bai wa kamfanin ɗan uwansa Hassan Yusuf, Lubekh Nigeria Limited kwangilar Naira miliyan 17.5, wadda ita ma aka ce ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.
Yusuf ya musanta duk zarge-zargen da ake yi masa.
A zaman kotun, lauya mai gabatar da ƙara, Francis Usani, ya buƙaci a hana belin Yusuf, inda ya ce bai cika sharuɗan belin da EFCC ta ba shi a baya ba, wanda ya haɗa da wajibcin kai kansa ofishin hukumar sau biyu a kowane mako.
Ya ƙara da cewa Yusuf ya yi fariya da dangantakarsa da masu ruwa da tsaki a siyasa, don haka akwai yiwuwar ya tsere idan aka bayar da belinsa.
Ya kuma bayyana cewa jami’an EFCC sun sha wahala kafin su kama shi tare da gurfanar da shi a kotu.
Sai dai lauyan Yusuf, O.I. Habeeb (SAN), ya roƙi kotu da ta bayar da belinsa, inda ya ce laifukan da ake zargin sa da suna da ikon samun beli bisa doka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Usman Yusuf zargi bayar da belin Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnoni 20 Na Fuskantar Matsin Lambar NULGE Kan Rashin Aiwatar Da Mafi Karanci Albashi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dokar albashi na naira 70,000 a ranar 29 ga watan Yuli na 2024, bayan shafe watanni ana muhawara da kungiyoyin kwadago.
Sabon mafi karancin albashin na wata-wata ya karu da kaso 133 daga naira 30,000 zuwa naira 70,000, sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.
Da yake ba da bayani kan halin da ake ciki, shugaban kungiyar NULGE ya ce, “A zahirin gaskiya muna fuskantar matsaloli da jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara aiwatar da mafi karancin albashi ba.
“Muna da Jihohi irinsu Sakkwato, Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Borno, Kurus Ribas, Abuja, da dai sauransu, wasu sun fara biyan ma’aikatan jiharsu albashi sun bar ma’aikatan kananan hukumomi da malaman firamare, amma mun ci gaba da hada kai da rokon su da su yi wa wadannan ma’aikata abun da ya kamata.
“Wasu daga cikinsu sun yi alkawari amma sun kasa cikawa. Muna fatan nan ba da jimawa ba za a warware wadannan damuwowin,” in ji shi.
Dangane da aiwatar da dokar cin kashin kan kananan hukumomi kuwa, shugaban NULGE ya yi bayanin cewa har zuwa yanzu Babban Bankin Nijeriya bai tuntubi kananan hukumomi kan bude asusun bankuna ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp