Ku Ajiye Makamanku Ba Tare Da Wani Sharaɗi Ba Kafin Lokaci Ya Ƙure – Gwamna Lawal
Published: 14th, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su.
Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga.
Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare da gyara tubabbun su.
“Shirin Arewa maso Yamma na neman bayar da tsarin tuba ga mutanen da ke da hannu cikin ayyukan ‘yan bindiga. Wannan yunƙurin zai ƙunshi horar da su wajen sana’o’i, canja musu tunani, da sake musu fasalin aƙida.”
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimaka wa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ‘yan bindiga da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.
“Ina so in sake mayar da alƙawarin da gwamnatinmu ta yi na tallafa wa waɗannan tsare-tsare da sauran dabaru masu inganci da ake amfani da su wajen kai wannan yaƙi zuwa ga ’yan bindigar har sai an fatattake su yadda ya kamata tare da murƙushe su.
“Amma ga waɗanda suka yi niyyar miƙa makamansu ba tare da wani sharaɗi ba da son rai, suna da ‘yancin yin hakan. Kafa Hedikwatar Rundunar Tsaro ta Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma zai ba da dama da masu niyyar tuba tare da gyara musu ɗabi’arsu.
“A kan wannan batu, ina so in miƙa godiyata ga Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Christopher Musa, na ganin jihar Zamfara ta cancanci karbar baƙuncin Operation Safe Corridor na 3 a ƙasar nan.
“Ina kuma so in gode wa shugaban kwamitin aiwatar da ayyukan Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma, Manjo Janar EV Onumajoro, wanda kuma shi ne Babban Hafsan Harkokin Tsaro na Hedikwatar Tsaron Nijeriya, da tawagarsa saboda ganin Zamfara ta dace da kafa hedikwatar wannan muhimmin dakaru.
“Daga ƙarshe muna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kuma Babban Kwamandan Askarawan Tarayyar Nijeriya, bisa dukkan ƙoƙarinsa da goyon bayansa ga hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
“Abin da ake buƙata shi ne ƙara ƙarfafa nasarorin da aka samu wajen murƙushe ayyukan ’yan bindiga da sauran aikata laifuka. Ina so in tabbatar muku da ƙudurinmu na yin komai don ganin cewa wannan shirin ya yi nasara. A garemu a yau, wannan shi ne haihuwar sabuwar Zamfara mai tsari.
“Da waɗannan ‘yan kalamai, ina so in miƙa wannan cibiyar domin yin aiki a matsayin hedikwatar Operation Safe Corridor na Arewa maso Yamma domin amfanin jihar Zamfara da kuma ƙyaunatacciyar ƙasarmu Nijeriya.”
Tun da farko, Manjo Janar Onumajuru, wanda ya wakilci Babban Hafsan Tsaron Ƙasar, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da yake baiwa sojoji a yaƙin da ake da ’yan bindiga a Zamfara.
“Operation Safe Corridor dakaru ce mai aiki da cikakken tsari. Tana aiki a matsayin hanyar samar da zaman lafiya. Bayan karbar ragamar wannan ginin, za mu ci gaba da haɗa kai da Gwamna da al’ummar Zamfara, waɗanda su ne masu ruwa da tsaki a wannan aiki, domin tabbatar da haɗin kai da samun nasara.
Aminu Dalhatu/Gusau
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lawal Tsaro Zamfara Arewa maso Yamma jihar Zamfara yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara
’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara.
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata.
Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban.
Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.