2025-03-24@05:59:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 505
«Lawal»:
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...

Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma...
Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla. Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin...
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga...
Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet. Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi...
A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa,...
An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin...
A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar. Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan...
KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin...
“Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi. Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya. A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a...
Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata kungiya mai suna Grassroots Mobilizers for Better Nigeria Initiative (GMBNI), ta yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wani Almajiri a ƙaramar hukumar Gwaram, Jihar Jigawa. Ƙungiyar ta bayyana matuƙar bakin ciki da ɓacin rai game da wannan cin zarafin da aka yi wa yaron, wanda ya kai ga mutuwarsa cikin...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa. Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar...
Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
An gudanar da Sallar Juma’a a mako na uku na watan Ramadan a Masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da tsauraran takunkumin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta dauka, tare da halartar Palasdinawa 80,000. Kamfanin dillancin labaran Al-Naba y bayar da rahoton cewa, dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a...

Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama
Jakadan dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, Chen Xu, ya gabatar da jawabi a madadin kungiyar abokantaka ta inganta hakkin bil’adama, da tattaunawa da hadin gwiwa da sauransu, yayin taron MDD karo na 58 da ya gudana a jiya Alhamis. A cikin...
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci...
Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na...

Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da...
Sai dai, bisa ladabi da girmamawa ga masarautu, Gwamna Bala Muhammad ya amince da roƙon ɗage Hawan Daushe. Duk da haka, gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda ba a tuntuɓe ta ba kafin yanke wannan shawara. Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sarakuna domin kyautata zamantakewa da ci gaban...
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Dubban dubatan mutane masu goyon bayan magajin garin Istambul a kasar Turkiya ne suka fito kan titunan birnin inda suke bukatar gwamnatin Urdugan ta sake shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mutane suna ganin Ekrem Imamoglu, dan takarar shugaban kasa ne a zaben shugaban kasa mai zuwa kuma mai yuwa...
An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa. Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan...
Cibiyar Bincike Kan Harkar Noma (IAR) tare da hadin gwiwar Hukumar Yada Sakamakon Bincike da Wayar da Kan Manoma ta Kasa (NAERLS), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sun shirya taron kwana guda a Kaduna domin masu ruwa da tsaki kan aikin bunkasa noman dawa a Najeriya. Taken taron shi ne: “Gabatarwa da Tattaunawa Kan...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027. Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu...
Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila...
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe...
Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A...
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin...
Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah. Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron...
Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga...
Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara...
A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun...

An Gudanar Da Tarukan Tattaunawa Na Kasa Da Kasa Masu Jigon “Sin A Yanayin Bazara” A Turkiya Da Colombia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya umarci ɗaukacin Masarautun Kano guda huɗu da su fara shirye-shiryen Hawan Sallah da bisa al’ada aka saba domin ganin jama’a da maziyarta sun nishaɗantu a yayin bukukuwan Sallah na bana. Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin wani taron buɗa-baki da sarakunan gargajiya da aka yi a ɗakin...
MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400. Wakilin kasar Rasha a MDD ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada...
Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa;...
Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar...
A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya...
Kasar Sin na matukar adawa da haramta amfani da kirkirarriyar basira ta DeepSeek da gwamnatin Amurka ta yi a ranar Talata, biyo bayan rahoton da kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar na cewa, ma’aikatar cinikayya ta Amurka ta haramtawa ma’aikata amfani da DeepSeek kan na’urorin da gwamnati ta samar musu. Mai magana da yawun ma’aikatar...
HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bayyana cewa Gwamna Umar Namadi ya amince da rabon kujeru 54 na Hajj ga malamai da jami’an da za su jagoranci Alhazai don aikin Hajjin 2025. Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga wakilin Radio Nigeria a Dutse, babban birnin jihar. ...
A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa...

Munanan Hare-hare Sojojin HKI A Gaza Da Safiyar Yau Talata Sun Yi Sanadiyyar Shahadar Fiye Da Falasdinawa 200
Rahotanni Daga Gaza sun ce adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da safiyar yau sun haura 200 Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fitar a yau Talata ta ce; Adadin shahidan sanadiyyar sabbin hare-haren HKI sun kai 244. Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin adadin shahidan ba, da...