Gurgu mai mata huɗu da bai yarda da yin bara ba
Published: 15th, February 2025 GMT
Duk da kasancewar Malam Murtala Abubakar nakasasshe mara kafafu, amma bai lamunci yin bara ba. Hasali ma, ya rabu da matarsa ta fari saboda dabi’arta ta yin bara.
Shekaru 50 da suka wuce Malam Muratala ya rasa kafafunsa, tun yana dan shekara bakwai a duniya. A haka ya ci gaba da rayuwarsa, inda a halin yanzu yake kula da iyalansa, mata hudu wadanda dukansu nakasassu ne da ’ya’yansu 15.
A haka yake fadi-tashin daukar dawainiyarsu, domin tsare mutuncinsa, saboda ya yi imanin cewa, “Bara tana rage daraja da kimar mutum.” Wannan ne ma ya sa ya rabu da matarsa ta farko saboda dabi’ar bara.
Rayuwar Malam Murtala, wanda a lokacin da yake dan shekara bakwai yake takawa da kafafunsa zuwa ko’ina, ta juya ne bayan da ya kamu da wata cuta mai wuyar ganowa. Amma tsawon shekarun da ya yi da wannan lalura, yanzu ya zama babban abin misali da ke tabbatar da cewa nakasa ba kasawa ba ce.
A Najeriya, kasar da nakasassu da dama ke dogaro da bara don, Malam Murtala ya zama gagara-badau.
Madigancin, mazaunin unguwar Rikkos ne da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda yake da dan shagon kayan masarufi da ya kafa tun shekaru kusan 25 da suka gabata. Da dan abin da yake samu daga shagon nasa da ke a tashar mota ta ‘Plateau Riders’ a birnin Jos yake kula da iyalinsa.
Auren mai nakasa shi ne zaman lafiyaYa bayyana cewa daga bayan manyan ’ya’yansu sun shawo kansa, kuma yanzu ya dawo da babbar matarsa, a kan tsatsauran sharadin cewa ba za ta sake komawa bara ba, shi kuma zai samar mata da dan jarin fara sana’a a gida.
Ya bayyana rayuwarsa tare da su a matsayin “zabi cikin nutsuwa,” yana mai cewa ya auri nakasassu ne domin samun “salama da hutu a gida.
“Auren mace mai lafiya na iya jawo mini matsala,” ya yi dariya, ya kara da cewa, “Idan mazan da ke da nakasa za su rika auren mata masu lafiya, wa zai auri matan da ke da nakasa? Wannan na nufin za a bar mata da dama masu nakasa babu aure ba, kuma hakan zai tilasta wa yawancinsu ci gaba da bara.”
Shi da matan nasa hudu babu wanda ke motsa kafafunsu sakamakon yanayi daban-daban na rashin lafiya, amma duk da haka ba sa yin bara. A maimakon haka, kowacce ta sami karamin sana’ar da ta dogara da shi.
“Na karfafa musu gwiwa su gudanar da kananan sana’o’i a cikin gida domin mu taimaka wa juna wajen ciyar da iyali,” in ji shi, inda ya bayyana cewa yana son kowacce daga cikin matansa ta samu ’yancin samun kudi, musamman saboda ba ya samun isasshen kudi don biya wa dukkansu bukatunsu.
Ya samu goyon bayan matansaKaltume, matarsa ta biyu, tana goyon bayan matsayinsa a kan bara. Ta ce duk da yanayin kafafunta, ba ta taba jin sha’awar yin bara ba, tun kafin ya aure ta.
Ita ma ta yi imani da cewa “bara tana zubar da darajar mutum,” tana mai cewa duk yanayinsu su biyar, amma suna jin dadin rayuwarsu kuma suna da yakinin cewa Allah Zai tausaya musu matukar suna kokarin neman halak.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidansu da ke gefen unguwar Rikkos, ya ga yadda gidan da aka gina da laka ya cika da harkokin daban-daban da kuma kasuwanci. Matan Murtala uku da ke gida suna aiki cikin kuzari tare da jajircewa don samun abin rayuwa.
Wakilinmu ya lura da yadda matan suke kai-komo a cikin gida cikin kwarewa duk da yanayin jikinsu. Matan suna jan jiki daga daki zuwa kicin don kula da gyada da ake soyawa a kan wuta. Cikin sauki za a gane cewa magidancin ya gina gidansa ne a kan tushe mai karfi na jajircewa, kirkira, da tallafawa juna.
Kaltume wadda ke kwararriya ce a sana’o’i daban-daban ta shaida wa wakilinmu cikin farin ciki cewa, “Na kware wajen yin kitso, kuma duk Asabar, mata suna taruwa a nan gida in yi musu kitso su biya ni. Ina kuma hada turaruka da sabulai na gargajiya, wadanda nake sayarwa a shagunan kayan masarufi, har da na mijina.”
Ko da yake cewa sauran matan Murtala sun ki yin magana da wakilinmu, amma Kaltume, ta ce kowacce daga cikinsu na da nata sana’ar.
“Mu uku muka kware wajen suyar gyada, yayin da matar gida ta hudu ke sayar da kayan lambu. Muna aiki tare don tallafa wa juna da kuma inganta walwalar iyalinmu,” in ji ta.
Malam Murtala Abubakar ya ce, shi da iyalinsa suna cikin farin ciki a yanzu, amma ba koyaushe ake samun hakan ba.
Yadda na daina baraA cikin yanayi mai cike na damuwa bayan ya tuna rayuwarsa ta baya, Malam Murtala ya ce ya tashi yana yin bara tun yana yaro, duk da cewa yana kin bara kuma yana kuka yana rokon iyayensa.
Ya ce, “Na san cewa duk sadaka da nake samu a kan tituna yana taimaka musu, amma suk da hakan ban taba jin dadinsa ba.”
Murtala ya ce a yayin da yake tasowa ya yi tafiya har zuwa Enugu da Aba da Fatakwal a Kudancin kasar nan don yin bara. Sai dai, a hankali ya gane cewa ba ta da tabbas, sai ya zabi neman hanyar halal ta rayuwa.
Magidancin ya ce, “Daina bara na da matukar wahala, amma na yanke shawarar neman sana’a, duk da cewa ba ni da jari.
“Na yi tafiye-tafiye daga wuri zuwa wuri don neman hanyar samun abin rayuwa, amma ban samu jari ba, kuma ba na son ci gaba da bara. Da taimakon Allah, bayan shan wahalhalu da dama, na sami damar kafa karamin shago na kayan masarufi. Duk da cewa kasuwancin ba ya da isasshen jari, na gudanar da shi tsawon shekaru fiye da 20,” in ji shi.
Yadda yake rayuwaA yanzu da yake da mutane 20 a karkashinsa, ya ce yana biyan kudin makarantar ’ya’yansa daga dan kudin da yake samu daga sana’arsa.
Ya ce, a cikin yaran “Wasu sun kammala firamare, wasu kuma sun gama sakandare. Na aurar da ’ya’yana mata guda biyar. Ga ’ya’ya maza kuwa, na saka su a sana’o’i daban-daban saboda ba zan iya daukar nauyin karatunsu nan gaba ba.”
Dattijon ya bayana cewa yana cikin farin ciki da kwanciyar hankali da ya daina dogaro da bara kumam yana alfahari da kadan din da yake samu daga shagonsa.
Sai dai ya ce, a baya-bayan nan, bara ta so ta ja shi a lokacin da ya gobara ta kone shagon nasa kurmus. Amma duk da jarabar barar da ta addabe shi, jajircewarsa ta yi galaba, ba tare da ya mika wuya ba.
Ya ce, “Na san irin illar da bara ke yi ga darajar mutum,” yana mai bayyana cewa abokan arziki da masu fatan alheri a tashar mota sun taimaka masa wajen tara kudin sake gina shagonsa da ci gaba da kasuwanci. “Ina gode wa Allah bisa ci gaban da aka samu zuwa yanzu,” in ji shi.
Bayan da ya kwace daga bara, yanzu haka yana cikin masu kira kan guje ta. Ya bayyana rayuwar mabaraci a matsayin mai cike da bakin ciki, wadda babu wani mai hankali, ko mai nakasa ko lafiyayye, da ya kamata ya so yin ta. Sai dai, ya ce mutane da dama suna yi ne saboda rashin damar tara jari don fara kananan sana’o’i. Ya jaddada cewa, “Ni dai na yi sa’ar tsira daga bara. Babu wata kima ko daraja a cikinta.”
Kaltume, ta bayyana cewa bai kamata nakasa ta kashe wa mutum zuciya ba. Ta shawarci nakasassu da ke yin bara da cewa “Ba yana nufin ka rasa duk jikinka ba ne. Ka nemi sana’a ka ci gaba da rayuwa kamar kowa. Ka fara wani abu ka roki Allah Ya sa albarka; za ka ga ka samu nasara.” Ta kara da cewa masu bara a kan titi suna fuskantar mummunar yanayi wanda ke sa su kamuwa da cututtuka daban-daban.
Yayin da yake hawa babur dinsa mai kafa hudu da aka kera masa na musamman, Malam Murtala ya ce ana iya shawo kan masu bara su bar kan tituna idan kowa zai ba da gudummawar da ta dace.
A karshe ya yi kira ga gwamnati da ta gane cewa nakasassu suna da muhimmanci a cikin al’umma, ta kuma tallafa musu da sana’o’i. “Ba duk masu nakasa ne ke son kashe rayuwarsu a kan tituna suna bara ba. Nakasasshe mai hankali zai so ya daina bara,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta kashe N5bn domin bai wa mata tallafin kiwon awakai a Katsina
Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai.
Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar.
Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu a gundumomi 361 da ke faɗin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani ginishiki ne na bunƙasa harkokin noma da kiwo wanda yake da burin ganin Katsina ta zama ja gaba a fannin dogaro da kai a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
A cewar Gwamnan, kiwon awakai yana da muhimmanci kuma ɗaya ne daga cikin muradin gwamnantinsa na bunƙasa harkokin noma da kiwo da wadatar abinci sannan kuma abin dogaro da kai ga ƙananan manoma.
A nasa jawabin, mashawarcin gwamnan ma musamman kan harkokin kiwo, Suleiman Yusuf, ya ce bai wa mata tallafin awakai babbar hujja kan yadda gwamnatin ke ƙoƙarin ganin ta rage talauci a tsakanin al’umma.
“Mun ƙaddamar da wannan shiri ne saboda fahimtar da muka yi wa muhimmacin da rawar da mata suke takawa wajen bunƙasar tattalin arziki.
“Saboda haka wannan tallafi aka bai wa matan muna da yaƙinin cewa zai kawo kyakkyawan sauyi a tsakanin al’umma,” in ji Yusuf.