Nazari A Kan Noman Agwaluma
Published: 15th, February 2025 GMT
Har ila yau, nau’in Agwaluma na agbalumo ko kuma na Udara, na bukatar yi masa ban ruwa sosai, musamman don ya yi saurin nuna a cikin kasar noman da aka shuka shi.
Bugu da kari, idan manomi zai sayo Irin nomansa, ya tabbatar da ya sayo a gurin da aka fi sani, musamman don ya samu ingantacce kuma mai lafiya.
Ba Ta Kariya Daga Kamuwa Da kwari Ko Sauran Cututtukan Da Ke Harbin Amfanin Gona:
Ana bukatar manomi ya tabbatar da yana ba ta kariya daga harbin kwari ko cututtukan da ke yi mata illa bayan ana shuka ta, domin irin wadannan cututtukan ko kwarin na iya hana Irinta da aka shuka ruba a cikin kasar noman da aka shuka Irin.
Zuwa Tsawon Wane Lokaci Agwaluma Ke Kammala Girma?
Bayan an shuka Agwaluma, musamman Gona na fara fitar da ‘ya’yanta ne daga shekara biyar zuwa 10, inda kuma ake saran saiwar jikinta, domin adana wa ta fi bukatar yanayin da ya kai ma’unin yanayi daga 60 zuwa 70.
Har ila yau, wasu sun yi hasashen cewa, ba za a iya yin noman Agwaluma a Nijeriya ba, amma maganar ba haka take ba; domin ana iya yin nomanta kuma ta yi kyau sosai har dimbin wacce za a yi hada-hadar kasuwancinta abin da kawai ake bukata shi ne, mayar da hankali kan shuka ta da aka yi da nuna kwarin gwiwa da kuma ba ta kulawar da ta dace.
Abubuwan Da Ya Kamata A Tanada Na Noman Agwaluma Don Samun Riba A Nijeriya
Samar Da Kyakkyawan Tsari:
Kafin ka fara yin nomanta, ka tabbatar ka tsara yadda noman nata zai kasance, musamman domin kaucewa yin asara bayan ka zuba jarinka a ciki.
Gyaran Gonar Shuka Ta:
Kafin ka shuka Irinta, ana bukatar ka tabbatar da kasar noman nata mai kyau ce.
Zabo Nau’in Da Ya Dace:
Na bukatar ka zabo daga cikin nau’ukanta biyu, wato na Udara ko kuma na Agbalumo, inda ake iya gano su ta hanyar girmansu.
Amfanin na kai wa tsawon shekara takwas kafin ta kammala girma, inda kuma aka kara habaka nau’insa wanda zai iya girma bayan shekara uku.
Yadda Ake Girbe Agwaluma:
Akasari, ana girbe ta ne a watan Disamba, sai dai a wannan lokaci, ba ta yin dadi sosai; saboda haka, ana so a bar ta a gonar da aka shuka ta har wani ruwan saman ya kara dukan ta kafin a girbe ta, inda ake yi mata girbin bayan Ganyen ta ya rikide zuwa ruwan dorawa.
Tsara Dabarun Hada-Hadar Kasuwancinta:
Bayan an shuka ta ta girma, za a iya kai ta kasuwa don sayarwa, domin ana nuna ci gaba da batan ta a kasuwa ganin cewa, ana yawan yin amfani da ita. Haka kuma manomi, zai iya wallafa tallan ta a kafar yanar gizo, don masu bukata su gani su kuma saya.
কীওয়ার্ড: Nazari
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Shirye-shirye Sun Yi Nisa A Jihar Jigawa
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce shirye-shirye sun yi nisa game da aikin Hajjin shekarar 2025 a jihar.
Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ne ya bayyana hakan ga Radio Nigeria a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
A cewarsa, zuwa yanzu hukumar ta mika sunayen maniyyata fiye da dubu ɗaya da suka kammala biyan kuɗin aikin Hajji daga jihar zuwa ga Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).
Ya ce tuni aka fara shigar da waɗanda suka kammala biyan kuɗin cikin tsarin neman biza.
Labbo ya bayyana cewa hukumar ta biya Hukumar Hajji ta Ƙasa kuɗi naira biliyan takwas a madadin alhazan jihar na shekarar 2025.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce ana gudanar da tarukan bita ga maniyyata a kullum, a kananan hukumomi 27 na jihar, ta hannun wasu malamai don ilmantar da su game da aikin hajjin.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba jakunkuna da za su daukin nauyin kilo 8 da unifom ga jami’an yankuna da cibiyoyi domin rabawa mahajjatan.
Shugaban hukumar ya ja hankalin maniyyatan da su riƙa halartar traon bita saboda muhimmancinsa.
Ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa goyon baya da haɗin kai da yake ba hukumar domin samun nasarar gudanar da aikin hajji ba tare da wata tangarda ba.
Radio Nigeria ta ruwaito cewa Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware kujeru sama da 1,800 ga jihar domin aikin hajjin bana.
Usman Muhammad Zaria