2025-03-24@11:26:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2422

«Nazari»:

    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar...
    Wani Sufeto Dansandan da ke aiki a Jihar Kuros Ribas, ya harbe matar abokin aikinsa har lahira tare da jikkata wasu mutane biyu a harbe-harben da ya yi a ranar Lahadi. Mai magana da yawun rundunar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da faruwar lamarin ga Labarai a birnin Kalaba, inda ta bayyana cewa jami’an Dansandan...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana...
    Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23...
    Wasu manyan ’yan Nijeriya da suka tafi Umarah sun yi wa Gwamnan Katsina Dikko Umar Radda ta’aziyya a Saudiyya. A safiyar Lahadi ce dai Allah Ya karɓi rayuwar mahaifiyar Gwamnan, Hajiya Safara’u Umaru Baribari bayan shafe tsawon lokaci tana jinya a Jihar Katsina. Wata mata ta haifi jaririn da ba nata ba NAJERIYA A YAU:...
    Wata mata mai suna Krystena Murray ’yar Amurka, wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne, ta fara ɗaukar matakin shari’a a kan wani asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IBF). Matar tana zargin asibitin da yi mata dashen...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake...
    Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar  karkashin kungiyar Tahrir Sham  suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hausawa sun yi gaskiya da suka ce ‘yawan mutane su be kasuwa’. Yawan hada hadar da ake yi tsakanin ‘yan kasuwa da abokan cinikinsu na ɗaya daga cikin abun da zai tabbatar maka kasuwanci na gudana kamar yadda ake so. Sai dai da zarar an ce watan Ramadana...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin...
    A yau Lahadi firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gana da dan majalisar dattawan Amurka sanata Steve Daines, tare da wasu ‘yan kasuwan Amurka da suka zo kasar Sin, don halartar dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 wanda ya gudana a nan birnin Beijing. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu,...
    A yau Lahadi ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin tattauna raya kasa na kasar Sin na 2025 a nan birnin Beijing, taron da cibiyar binciken raya kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar asusun binciken raya kasa na kasar Sin. Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci bikin bude...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja. Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba. Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa ’Yan...
    4 – Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi kofa ce ta kowane sharri. 5 – Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa. 6 Ki nuna wa mijinki...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta...
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma...
    A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.  A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan,...
    Ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan ta bada sanarwan cewa kasar Iran ce a gaba da dukkan kasashen makobta da kasar Afganisatan wacce tafi shigo da kayakinta cikin kasar a shekara ta 1403 ta kalandar Iraniyawa da ta kare. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Afganistan Abdussalam Jawad...
    Hukumar birnin istambul ta bada sanarwan dakatar da Akram Imamoglu daga matsayinsa na magajin garin birnin Istambul na wucin gadi, har zuwa lokacinda za’a tabbatar da kubutarsa daga abubuwan da aka zarginsa da su. Tashar talabijin ta Almayaddeen ta kasar Labanon ta nakalto mahukunta a birnin Istambul na bada labarin cewa za’a zabi wanda zai...
    Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara. Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin...
    Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kimanin shekaru 12 da suka wuce, wato a ranar 23 ga watan Maris din shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da tunanin raya al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya, a karon farko, yayin da yake jawabi a wata jami’a dake birnin Moscow na kasar Rasha. Asalin tunanin ya shafi al’adun...
    Al’ummar Jihar Kano, sun shiga shida ruɗani yayin da rikicin Masarautar jihar, ya ɗauki wani sabon salo game da shirin gudanar da bikin hawan salla. Tsagin sarakunan jihar na 15 da na 16, wato Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta kama wasu matasa huɗu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani yaro ɗan shekara shida, Shuaibu Safiyanu, a ƙauyen Sade da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Aminiya ta ruwaito cewar mahaifin yaron, Safiyanu Abdullahi ne, ya sanar da Sarkin garinsu, Musa Isah, cewa a ranar 20 ga...
    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga...
    Ya kara bayanin cewa an dauki matakin ne inda har abin ya shafi daliban da suke mazabun majalisar Dattawa biyu na Jihar Osun. Ya nuna jin dadinsa inda ya furta ce wa“Wani abin farinciki ne gare ni dana samu yawan daliban da suka samu damar yin rajista daga mazaba ta da kuma saiuran mazabun na...
    Wani abin al’ajabi da ban tsoro ya auku inda rana tsaka garin Zip da ke Jihar Taraba ya nutse baki dayansa a cikin Kogin Biniwai. Wakilin Aminiya ya ziyarci garin domin gani da ido, inda ya ruwaito cewa a halin yanzu babu sauran wani gini ko bishiya da ake gani a garin, duk kogin ya...
    Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani...
    Rahotanni daga Yemen na cewa sojojin Amurka sun kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama na Hudayda a wani sabon hari kan kasar Yemen tun bayan da Washington ta sanar da kai munanan hare-hare kan kasar dake adawa da hare-haren da Isra’ila ke kai wa al’ummar Gaza. Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga...
    Gwaje-gwajen da aka yi a ranar 17 ga Maris sun nuna cewa dan wasan tawagar farko Marc Casadó yana da rauni a gefen damansa, za a kara yin gwajin dan wasan don sanin girman raunin da kuma kwanakin da zai shafe ta na jinya, hakazalika Gwaje-gwaje a wannan rana kuma sun tabbatar da cewa dan...
    A tattaunawarsa da Aminiya wani manomin gurjiya, Malam Muhammad Dahiru Kanda ya bayyana cewa, ya shafe sama da shekara 25 yana noman gurjiya ba tare da ya taba samun wani tasgaro ba. Ya kara da cewa, shi noman gurjiya na da muhimminci matuka domin kuwa yana samar wa duk mai yin sa babbar riba. Mata...
    A cewarsa, domin tabbatar da gudanar da wannan tantancewar, an samar da kwakkwaran kwamitoci a matakin jiha da kananan hukumomi tare da sauran sassan hukumomin da ke da alaka da kudi, sannan an ba su umarni samar da dukkan bayanan biyan albashin nan take. Farouk ya bukaci ma’aikatan da matsala ta shafa su kai kansu...
    Ita maganar bada damar tsayawa takara ba tare da zaben fidda gwani ba an dauki matakin ne saboda yadda aka ga ‘yan adawa ko jam’iyyun adawa suke kokarin tayar da babbar kura mai hayaki,wa ita jam’iyyar mai rike da kambun mulki a 2027 domin “Ba a san maci Tuwo ba sai Miya ta kare”. Ana...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a...
    Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata. Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel...
    A Sudan bayan sake karbe fadar shugaban kasa da ke birnin Khartoum, sojojin kasar sun ci gaba da kai farmaki a babban birnin kasar a ranar Asabar, inda suka sake karbe iko da wasu gine-gine, ciki har da babban bankin kasa da hedkwatar hukumar leken asiri da kuma gidan adana kayan tarihi na kasar. Ana...
    Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar...
    Kallo ya koma sama bayan da mata suka karbe ragamar kasuwancin kayan lambu a a tsakiyar birnin Gombe, inda a baya kasuwancin kayan ya kasance a hannun maza kadai na tsawon lokaci. Wannan sabon sauyi ya da ya taso a hankali ya faru ne a sakamakon matsalolin kudi da nauyin kula da kai da kuma...
    Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.  A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.8...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada bukatar bin dokar da ta hana kiwon dare da makiyaya ke yi a fadin jihar domin rage hadurra a tituna, wanda ke haddasa asarar rai ko shiga mawuyacin hali a sanadiyar raƙuman da ke bi ta manyan tituna. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da ya karbi...
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa,...