Fina-finai Masu Dogon Zango A Masana’antar Kannywood: Ci Gaba Ko Akasin Haka?
Published: 16th, February 2025 GMT
A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar.
Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina; na daga cikin fina-finan da ke kan gaba a ‘YouTube’, harkokin fina-finan Kannywood, sun koma wannan kafar ne; tun bayan da tattalin arzikin masana’antar ya tabarbare sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa ‘YouTube’ din zai inganta kasuwancin masana’antar kamar yadda yake a baya.
An dade ana shirya fina-finan Hausa masu dogon zango, amma fim din Izzar So, na Lawan Ahmad; na cikin wadanda suka fara jan hankalin masu shirya fina-finan masana’antar, inda yanzu kusan duk manyan furodusoshi suka koma haska fina-finansu a kafar.
A baya can, a kan nuna fim babba ne a duk rana, amma yanzu fina-finan sun yi yawan da dole a haska biyu ko sama da haka, wanda hakan yasa wasu ke cewa, suna shan wahala wajen kallon fina-finan, ganin yadda fina-finan masu dogon zango ke kara yawaita, sai wasu ke ganin hakan a matsayin ci gaba, a gefe guda kuma, wasu ke cewa sun yi yawa.
A rahoton na BBC Hausa, za a iya kallon yawaitar fina-finan a matsayin ci gaba, sannan a gefe guda kuma za a iya kallon hakan a matsayin koma baya, ci gaba ne wajen samar da ayyukan yi ga jarumai da sauran ma’aikata da kuma bai wa ‘yan kallo damar samun sabbin fina-finai a koda-yaushe.
Amma yawaitar yin fina-finan, zai iya taba ingancinsu; sakamakon gaggawar fitar da su, Hausawa na cewa, “Idan dambu ya yi yawa, ba ya jin mai.” Sannan kuma, za su iya cunkushewa a kasuwa a rasa samun wanda zai yi babbar nasara, sai dai, masu sharhi na cewa, akwai bukatar a hada karfi da karfe wajen ganin an rika fitar da manyan fina-finai masu ma’ana da za su yi tasiri, su kuma samar da kudaden shiga; maimakon yin fina-finai barkatai da ba su da ma’ana ko inganci.
Wani abu da mutane ke gani shi ne, yawaitar fina-finan zai toshe hanyoyin samun kudi ga masu shirya fina-finan, tunda masu kallo za su raba hankalinsu wajen neman wane fim za su mayar da hankali su kalla, hakan zai sa su kasa tsayawa wuri daya wajen kallon, ma’ana maimakon a yi awa daya ana kallon fim guda, sai a raba wa fina-finai uku mintuna ashirin-ashirin; don a samu a kalli kowane daga ciki, musamman ma mata.
Idan kuma hakan ta faru, akwai yiwuwar ‘YouTube’ ya biya kamfani kudi kalilan, dalili kuwa shi ne; ‘YouTube’ na duba yawan masu kallo da kuma yawan lokacin da suka bata wajen kallon, domin kwatanta abin da ya kamata su biya a kan wani abu da aka dora a kan ‘Youtube’ din.
Maimakon fim daya ya samu ‘yan kallo kamar misali dubu dari biyar, sai ka ga bai fi dubu dari zai iya samu ba, saboda watakila akwai wasu fina-finan da yawa da masu kallon za su so su kalla a dan kankanin lokacin da suka ware, domin kallon fina-finan.
Haka kuma, yawaitar fina-finan manyan furodusoshi na matukar yin tasiri wajen durkushewar kananan furodusoshi masu tasowa, domin kuwa; kananan furodusoshi ba su da kudin da za su dauki nauyin fim din da za a iya shafe shekaru ana haska shi, sannan kuma ba lallai ne ya kasance da mabiya masu yawa a shafinsa na ‘YouTube’ ko wata kafar yanar gizo da za su kalla ba, ballan tana har ya samu wani abin kirki.
Har ila yau, akwai kuma bukatar a samu tsayayyen tsari wanda zai rika kididdige fina-finan da za a haska, domin ‘yan kallo su san su, su kuma san wanne za su bibiya tare kuma da shirya kallon nasu.
Dangane da inganci kuwa, masana sun tabbatar da cewa; akwai bambanci tsakanin fina-finan Hausa masu dogon zango da na kasashen waje, masana’antar fina-finan Hausa; ba su dade da fara mayar da hankali wajen fina-finai masu dogon zango ba, inda tuni sauran kasashen kuma, misali kamar Amurka da Indiya, suka riga suka yi nisa.
Don haka, salon rubuta fina-finai da ingancin aiwatar da su; ko shakka babu, ya sha bamban nesa ba kusa ba, har ma yadda ‘yan kallo ke daukarsu; ba zai taba zama daya ba.
Sai dai kuma, sun ce akwai bukatar masu shirya fina-finan na Hausa, su kara dagewa wajen inganta ayyukansu, domin kuwa akwai wadanda harkar fim, ba sana’arsu ba ce, sai kawai su ce za su shige ta gaba-gadi, kuma sai ka ga babban jarumin Kannywood, ya shiga sun yi fim mara inganci tare da shi, wanda ko alama hakan bai dace ba.
কীওয়ার্ড: Kannywood shirya fina finan masana antar
এছাড়াও পড়ুন: