2025-03-29@10:57:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2631

«masana antar»:

    Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma. A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan...
    ’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo. Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike. Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya. Har ila yau, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere. Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da...
    Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu-  Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah. Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba. Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook. Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki...
    Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...
    Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can. Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen...
    Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum.   2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma.   3-Maganin Basir Sadidan Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo. Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki...
    Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma  tsawon mita 180. Sannan   Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
    Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar Syriya a shekara ta 2011 zuwa 2017 don ingiza kasashen yamma kan gwamnatin kasar Siriya na cewa ta yi amfani da makaman guba a kan mutane, don cimmmai manufofinsu a kasar ta Siriya. A halin yanzu dai shugaban Trump zai dakatar da tallafin da ya ke bawa kungiyar mai yuwa saboda sun cimma manufarko a kasar Siriya ta kifar da gwamnatin Bashar a Al’asad. A...
        Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025.   Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka sare su, sannan aka banka musu wuta a abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin abin “aikin rashin imani” na tashin hankali bisa la’akari da bambancin kabilanci.   A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na gidauniyar, Injiniya Dakta Abubakar Gambo Umar, ya fitar, gidauniyar ta nuna damuwarta kan yadda hare-haren da ake kai wa ‘yan Arewa ke ƙaruwa a wasu sassan Kudancin kasan nan, tana...
    Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar. Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar. Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Kamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara. “Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta. Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda...
    Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
    Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike  da kirkiro wasu abubuwa.” Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin  ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya. da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya...
    Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai  cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar daurin talala a cikin gidansa. Babban magatakardar MDD ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar ta Sudan  ta Kudu da su ci gaba da riko da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya,inda ya ce: “ A dawo da gwamnatin hadin kan kasa, da aiki da alkawullan da aka yin a zaman lafiya da sulhu, da hakan ne kadai hanyar dawo...
    Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na  harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne. Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi. Har ila...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
    Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Maharan sun kai harin ne a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Wani mazaunin yankin ya ce: “Mummunan hari ne. Sun zo kwatsam suka fara harbi. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don kare al’ummarmu.” Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba. Kakakin rundunar, DSP Alabo...
    A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu. A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano...
    Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ce ’yan shi’a sun kai wa jami’an tsaro hari da bindigogi, duwatsu, da wasu makamai. A sakamakon haka, aka tura ƙarin dakaru domin kwantar da tarzomar. “Kwamishinan ’yan sanda, CP Ajao Saka Adewale, ya yi tir da wannan hari da aka kai wa jami’an tsaro,” in ji kakakin rundunar,...
    Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [19] Fashin Baƙi: Maganar da Ibn Juzai ya fadi a kan tawakkali tana bayyana ainihin ma’anar dogaro ga Allah cikin dukkan al’amura na rayuwa, wato samun alheri, da kiyaye shi, da kuma kauce wa masifa, ko kuma fita daga cikin masifa idan ta afku. Tawakkali yana nufin dogaro ga Allah da zuciya ɗaya tare da yin ƙoƙari da dalilan da Allah ya tanadar don cimma buri. Ba wai kawai mutum ya jingina da Allah ba tare da yin aiki ba, ko kuma ya dogara da aikinsa ba tare da tawakkali ba, sai dai a haɗa su duka. Bangarorin Tawakkali: Ibnu Juzai ya kasa tawakkali zuwa...
    A yammacin yau Juma’a ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a birnin Lhasa na jihar Xizang wato Tibet, inda aka fitar da “Takardar bayanin ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adam a Tibet a sabon zamani”. Takardar ta yi nuni da cewa, a ko da yaushe, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna mai da hankali kan ayyukan da suka shafi Xizang, kuma suna ci gaba da kyautatawa da raya tsarin mulkin Xizang, da daukar matakai masu inganci don raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawo alheri ga jama’a, da inganta hadin kai da ci gaban kabilu, da kuma kare hakkin dan Adam na dukkan kabilun...
    Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a  iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai. Matsalar tsaro Ko shakka babu...
      Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, tare da hadin gwiwar First Impression Communication Limited, ta shirya wani taro kan shirin Samar da Ruwa Mai Tsafta a Birane da Karkara da Tsabtace Muhalli da Kiwon Lafiya (SURWASH) da ya gudana a Arewa House, a Kaduna.   Da yake bude taron, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, Dakta Ibrahim Hamza, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance matsalar karancin ruwa a jihar.   Kwamshinan wanda Mataimakin Daraktan Albarkatun Ruwa, David Roven Aliyu ya wakilta, ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse a wasu al’ummomi domin inganta tsaftar muhalli da kiwon lafiya.   “Shirin SURWASH na Najeriya wani shiri ne da Asusun...
    Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin. Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana. A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
    Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau. An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny. A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza. An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da...
    A yau Juma’a aka kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao. Cikin kwanaki 4, kimanin wakilai 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 ne suka hallara a lardin Hainan na kasar Sin tare da musayar ra’ayi mai zurfi karkashin jigon na “Gina makomar asiya a duniya mai sauyawa.” A matsayinta na mai masaukin bakin, kasar Sin ta gabatar da shawarwari 4 da suka yi daidai da ra’ayin mahalarta taron. Shawarwarin sun hada da karfafa hadin kai da hadin gwiwa wajen inganta aminci, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa da dunkulewa, da samar da ci gaba da wadata na moriyar juna, da kiyaye zaman lafiya da tsaro da zaman jituwa. Alkaluma sun...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
    Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da shugabannin al’ummar Uromi bisa matakin da suka ɗauka domin daƙile yiwuwar tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai. Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta...
    Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da suka fito daga sassan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi ya jadadda cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin musamman ma cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta cimma gaggaruman nasarori wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da dorewar walwalar al’umma dogaro da jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato jKS da kokarin al’ummar Sinawa cikin hadin kai, kuma ba za a raba wadannan nasarori da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba, cikin hadda gudunmawar da kamfanonin ketare dake kasar Sin suke bayarwa....
    Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe sun fito daga Fatakwal, a Jihar Ribas, amma ‘yan banga sun ɗauka cewa ‘yan ta’adda ne. Gwamna Okpebholo ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru, inda ya jaddada cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a kisan. Amnesty International da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi kira da a tabbatar da an yi adalci. Gwamnan Edo ya yaba wa shugabannin Arewa bisa yadda suka kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba. Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara A jiya Alhamis ce Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa na gasar La Liga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0. Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar yin zaman faɗi da tazarar maki 3 a...
    Kimanin mutum 150 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wata mummunar girgizar ƙasa daban-daban da suka auku a ƙasashen Myanmar da Thailand. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa girgizar ƙasar wadda ta auku a wannan Juma’ar ta jikkata ɗaruruwan mutane a yayin da baraguzai suka danne gommai. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa an fuskanci wata mummunar girgizar kasa har kashi biyu masu ƙarfin awo 7.7 da 6.4 a Myanmar, tare kuma da wata girgizar ƙasar mai karfi da ta yi ɓarna a kasar Thailand wacce ta shafi wasu wurare a yankin. Girgizar ƙasa ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar DSP Yazid, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin. Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan...
    A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwankwaso ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta masu laifin. “Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji shi. Tsohon gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da gwamnatin Kano da sauran jihohin da abin ya shafa, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansu. Kisan ya haifar da cece-ku-ce kan hatsarin da ke tattare da ɗaukar doka a hannu, tare da buƙatar a ƙara inganta tsaro don hana irin haka faruwa a gaba. Jagororin siyasa da na al’umma da dama...
    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818  sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune,  kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
    Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke shirinsa na yin hawan, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da malamai da dattawa suka ba shi. “Muna tabbatar muku cewa hawan Sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai haddasa tashin hankali, wajibi ne a dakatar,” in ji Aminu Ado Bayero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar. Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin. Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama wasu matasa uku da ake zargi da satar kekunan ɗinki guda 19 a cibiyar koyon sana’a ta Dala Lawanti da ke Maiduguri. A cewar ’yan sanda, wani mai gadi a cibiyar, Kaka Modu Mustapha, mai shekaru 34, ya haɗa baki da wasu matasa biyu – Bukar Mustapha mai shekaru 16 da Ibrahim Mohammed mai shekaru 17 – domin aikata satar a ranar 22 ga wata Maris, 2025. ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio Kakakin rundunar, SP Nahum Kenneth Daso, ya ce jami’an ’yan sanda daga yankin Bulumkutu, sun samu rahoto game da satar, inda suka gudanar da bincike tare...
    Ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena, ‘yan uwana maza da mata wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya. Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya.   Sako daga Yusuf Murtala Assalaikum alaikum, Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a...
    Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
    “Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin  kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.” Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake zargin da matasa suka kama shi domin cetonsa daga hannun matsan inda aka garzaya da shi asibiti. Ya ci gaba da cewa wasu matasa a yankin da lamarin ya faru sun bi sawu inda suka kama daya daga cikin wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne kuma suka damke shi. Ya gargadi mazauna jihar kan yin yin hukuncin nan na daukar doka a hannunsu...
    Wakilin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Islamic Jihad a Tehran ya bayyana cewa: Ranar Qudus wata dama ce ta samar da hadin kai. A wannan rana al’ummar musulmi suna sabunta alkawarin da suka yi da Allah dangane da batun Palastinu. Ranar Kudus tana hada kai tare da karfafa gwagwarmayar Musulunci a yankin. Ya ci gaba da cewa, dukkanin bangarori na sun yi imanin cewa,  hanya daya tilo ta kubutar da Kudus da kuma ‘yantar da kasar Falasdinu ita ce goyon bayan Kudus da kuma tinkarar mamaye yankunan Falastinu da hakan ya hada da wannan masallaci mai alfarma da yahudawan sahyuniya suke yi. Ranar Kudus ta duniya ita ce ranar da ke bayyana dukkan sharrin Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma...
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
    Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne  a Abuja  bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da  halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana. Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana. Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria  tsakanin kasashen biyu. Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua ...
    Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025. Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi. Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka...
    Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar. Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu “Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba. “Kuma muna shirye mu ƙara...
    Yadda Ake Ba Da Ita Ana ba da ita kafin a fita zuwa Sallar Idi ko kafin Ranar Sallah da kwana daya ko biyu. Abin da ake bayarwa shi ne Muddan Nabiyy (mudun awo ne dan madaidaici wanda za a iya auna shi da cikin tafukan hannun mutum mai matsakaicin tsawo) guda hudu a kan kowane mutum. Ana fitarwa daga dukkan nau’in abinci, kamar mu a nan mu ce shinkafa, masara, doya, dawa, dauro, cukwi, nono da duk dai abin da galibin mutane suke amfani da shi a matsayin abinci. Malaman kasar Maroko wadda kasa ce ta Malaman Musulunci kuma ‘yan’uwanmu ne Malikawa; sun yi fatawa cewa ya halasta a ba da kudi a madadin abinci a Zakkar. Za a...
    Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar. Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi Yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe. A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri. A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi...
    kungiyar ta koka kan cewa bai dace a yi amfani da EFCC wajen kamun Jami’an gwamnatin jihar Bauchi da nufin nuna yatsa wa Gwamna Bala Muhammad wanda ya kasance mai fitowa da hakikanin gaskiyar halin da talakawa ke ciki da nema musu hakkinsu daga wajen shugaban kasa. kungiyar ta lura da cewa in ana amfani da irin wannan salon lallai za a samu nakasu wajen kyautata demukradiyya a kasar nan domin mutane da dama za su yi shiru kan abubuwan da suke tafiya ba daidai ba domin gudun musgunawa. Eyes on Democracy ta kuma nuna shakku kan yadda aka kama Akanta Janar din a lokacin da yake halartar taron FAAC a Abuja, inda ta bayyana cewa hukumar EFCC ba ta...
    Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
    A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.” Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya  Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah. Yadda ake fitarwa Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda...
    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...
    Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha  cikin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
    Gwamnatin kasar Amurka tana shirin dakatar da bada kudade ga hukumar GAVI wacce take samar da alluran riga kafi don tallafawa kasashe masu tasowa daga ciki har da tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trus ta Najeriya ta nakalto wata sanarwa daga hukumar USAID bayar inda take cewa gwamnatin shugaba Donal  Trump yana son janye tallafin da kasarsa ke bayarwa don wannan shirin, wanda yake yakar cutar Malaria da wasu cututtuka a wadannan kasashe. Labarin ya kara da cewa za’a dakatar da ayyukan samar da magunguna da alluran riga kafa har guda 5,341 idan an dakatar da tallafi, wanda yake cinye dalar Amurka biliyon 75 a ko wace shekara. A halin yanzu dai hukumar ta USAID ta bada dalar Amurla biliyon 48,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi. A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi Masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 15 kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga lamarin. “Bayan samun labarin garkuwar, jami’anmu sun ƙaddamar da bincike, inda suka kama mutum biyar da ake zargi, sannan suka ceto wanda aka sace a ranar 17 ga watan Maris,” in ji sanarwar....
    Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci. A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba voyayayen abu bane, musammamn duba da cewa, yawan aukuwar tashe-tashen hankula, kalubalen rashin tsaro da matsatin tattalin arziki, suna manyan hummulhaba’isin da ke janyo karancin abinci a a cikin alumma. Misali, yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabas, ayyukan ‘yan bindiga daji a yankin arewa masu yamma da kuma rikice-rikicen kabilanci a sauran yankuanan, sun janyo tarwatsa miliyoyin alumomi daga matsugunan su, lalata gonakansu wanda...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah? Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
    Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba ne illa murkushewa da kuma takura wa wasu kamfanonin kasashen ketare, tare da danne hakkokin sauran kasashen duniya na samun ci gaba. Yana mai cewa, hakan zai yi matukar cutar da kamfanonin tare da kawo cikas ga kwanciyar hankali da samun wadataccen tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ya kara da cewa, matakin zai yi kafar ungulu ga kokarin warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da...
    Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama. Bugu da kari,...
    Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji. La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani sabani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za...
    Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana wasan ɓuya da jami’an tsaro da wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Ɗan jarida mai bincike kan harkokin ’yan bindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗan bindigar. Isuhu Yellow ya yi fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya  Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba. Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar. Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar. Ƙudurorin...
    Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar.   Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci. A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
    A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa. Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai...
    Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a gaba. Sarkin ya ce, “Bisa umarnin da jama’a suka ba mu da kuma jajircewar da muka yi na ba su kariya, mun ga ya dace mu janye duk wani shiri da aka yi na bukukuwan Sallah bisa la’akari da halin da ake ciki.” Ya kara da cewa, tuntubar da aka yi da manyan malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki sun yi tasiri a...
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Sallah: Yadda ake shirin caɓa ado duk da tsadar kaya Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya  Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba. Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar. Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar. Ƙudurorin...
    Majalisar Wakilai ta janye ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu. Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar. Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba. Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar. Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin bayan cece-kucen da hakan ya haifar a faɗin ƙasar. Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin...
    A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya. Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da suke rike da birnin na Khartum. Sojojin kasar ta Sudan sun nuna shugaban majalisar sojan kasar Janar Burhan  a cikin fadar shugaban kasa, inda ya sanar da cewa; An ‘yanto da Khartum. A karon farko jirgin  Janar Burhan ya sauka a filin saukar jiragen sama na Khatrum, tun bayan da yaki ya barke. Tun a jiya Laraba ne dai  sojojin na Sudan su ka sanar...
    A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya. A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil da mata da maza, kowanne na ƙoƙarin sayen sabbin kaya. Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano Kayayyakin da aka fi saya sun haɗa da atamfofi, mayafai, adire, dogayen riguna, leshi, sarƙoƙi, yadi, da sauran kayan ado.   Kasuwanni sun cika maƙil da masu...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
     Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya  bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus. Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa, wasu barguzan makami mai linzamin sun fada a unguwar “Mifo Hurun”. Har ila yau harba makami mai linzamin daga Yemen ya sa an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin saukar jiragen sama na “Ben Gorion”. Jaridar “Yesrael Home” ta ce miliyoyin mutane ne su ka shiga dakunan boya saboda kaucewa makami mai  linzamin da aka harbo daga Yemen. A jiya Laraba Sayyid Abdulmalik al-Husi, jagoran...
    Manzon musamman na ministan harkokin wajen Iran a kan Syria, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya gana da karamin minista a gwamnatin kasar Katar inda su ka tattauna halin da ake ciki a kasar Syria, haka nan kuma sun jaddada wajabcin shigar da dukkanin bangarorin al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da gwamnati. A jiya Laraba ne dai Muhammad Ridha Shaibani ya kai ziyara birnin Doha  inda ya gana da ministan na kasar ta Katar  Muhammad al-Khalifi domin yin shawara akan Syria. Shaibani ya bayyana mahangar Iran akan Syria, da  ya kunshi ganin an shigar da kowane bangare na al’ummar kasar a cikin sha’anin tafiyar da kasar, ya kuma zama sun taka rawa wajen ayyana makomar kasar. A nashi gefen ministan...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland Chen Xu, ya gabatar da jawabi a jiya Laraba, yayin taro na 58 na kwamiti mai kula da harkokin kare hakkin bil Adama na MDD, don bayyana ra’ayin kasar Sin kan halin da Palasdinu da Isra’ila ke ciki. A cewarsa, daruruwan fararen hula sun yi asara sakamakon hare-hare ta sama da aka kaiwa zirin Gaza, kuma Sin na matukar adawa da hakan, tare da bayyana bacin ranta game da tabarbarewar matakin tsagaita bude wuta a wurin, wanda aka dauka bayan an sha matukar wahala. Ya ce abin da aka sa gaba cikin gaggawa shi ne kaucewa daukar ko wane irin mataki dake...
    A yayin da muka kammala watan azumin Ramadan, muna gabatar da wannan fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki ta Sallah kamar haka: Zakkar Fidir: Zakatul-Fitr ko Zakkar Fid-da-Kai, ita ce sadakar da ake fitarwa a karshen azumin watan Ramadan. Sunnah ce wajiba a kan kowane Musulmi namiji da Musulma mace, babba da yaro, da da bawa, ana so ya fitar da ita ko a fitar masa kafin zuwa Sallar Idi. Kuma ya halatta a fitar da ita kwana uku ko biyu ko daya kafin ranar Sallar Idi Karama don a ba fakirai da miskinadamar sarrafawa su yi farin ciki a ranar Idin. Mai gida zai fitar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet. “Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in...
    Ya kuma yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yansu tare da hana su shiga ayyukan da ka iya haddasa tashin hankali. Ya tunatar da al’umma cewa Sallah lokaci ne na zaman lafiya, haɗin kai, da farin ciki, don haka dole ne kowa ya fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Rundunar ta kuma samar da lambobin kiran gaggawa don bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa a lokacin bukukuwan sallar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
    Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton cewa akalla Falasdinawa 142,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin mako guda kacal saboda tsanantar hare-haren bama-bamai na Isra’ila. Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a wani taron manema labarai a jiya Laraba cewa, hare-haren da kuma umarnin gudun hijira, tare da hana kayan da ke shiga Gaza da kuma hana ayyukan jin kai a cikin yankin, suna yin mummunan tasiri ga daukacin al’ummar sama da miliyan biyu. Dujarric ya yi nuni da cewa, yayin da rikicin ya tsananta, ana sa ran adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zai karu sosai. A yammacin ranar Talata,...
    Bayanai daga falasdinu na cewa an kashe Hamas Abdul-Latif al-Qanou wani kakakin kungiyar Hamas a wani harin da Isra’ila ta kai a arewacin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Quds na Falasdinu ya bayar da rahoton  cewa, jami’in ya yi shahada ne a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa a garin Jabalia da ke arewacin zirin Gaza. Har ila yau harin ya yi sanadin jikkatar mutane da dama da suka hada da kananan yara. Wannan kisan dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren wuce gona da irin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza tun a watan Oktoban shekarar 2023, bayan wani dan takaitaccen lokaci inda ta saba ka’idojin tsagaita...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa. Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar. Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
    An kama mataimakin shugaban ƙasa na farko a Sudan ta Kudu Riek Machar a babban birnin ƙasar Juba, a yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar zaman tankiya tsakaninsa da Shugaba Salva Kiir. Faɗa tsakanin dakarun da ke goya wa shugabannin biyu baya ya tsananta a yankunan Rejaf da ke kudancin Juba da Wunaliet da ke yammaci. Rahotanni sun bayyana cewa an kama shi ne tare da uwargidansa Angekina Teny. Ana samun fargabar cewa kama shi zai iya kawo tarnaƙi ga yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasar. Kama Machar na zuwa ne bayan shafe makonni ana samun tashe tashe hankula bayan shugaba Kiir ya tsare wasu daga cikin abokan Machar a farkon watan nan. Tawagar majalisar ɗinkin duniya da ke...
    Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na tallafawa shirin inganta ilimi na bunkasa Afirka (BEAR) III, wani shiri na hadin gwiwa da hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da Jamhuriyar Koriya suka yi.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Balarabe Abdullahi Kiru, yace aikin yana da nufin haɓaka ilimin fasaha da na sana’a a faɗin Afirka, tare da mai da hankali kan ƙarfafa tsarin ilimin fasaha da na sana’a da horo (TVET).   Aikin zai mayar da hankali ne kan harkar noma, tare da mai da hankali kan sarrafa kayan noma da sarrafa su bayan girbi.     A cewar...
    FRSC, ta miƙa lamarin ga ‘yansanda don bincike, tare da yin kira ga direbobi su kiyaye dokokin hanya domin guje wa irin wannan hatsari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi alkawarin inganta sansanin horas da kuratan sojoji dake Zaria wato Depot domin baiwa hukumar Soji damar ci gaba da aikin horaswa a wajen.   Ministan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kai ziyarar tantance sojojin Najeriya da ke Chindit Cantonment a Zariya.   Ministan ya kuma ce, ma’aikatar tsaro ba za ta bar wani abu ba, wajen tabbatar da cewa makarantar firamare ta Chindit ta samu ingantuwar kayan aiki don dacewa da tsarin zamani a matsayin hanyar kara kwarin gwiwa na hafsoshi da sojoji na Kantoment da ke amfana da wajen.   Ya kara da cewa ofishin sa zai hada kai da gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an kammala makarantar...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai har iyakar Bachaka da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin garin. Harin ya faru ne kwana guda bayan da dakarun tsaro suka kashe wasu dakarun Lakurawa a yankin. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ba a tantance sunayen jami’an Kwastam da aka kashe ba. “Eh, an kai hari, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin Bachaka,” in ji kakakin rundunar, Nafiu Abubakar. Bayan...
    Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi mazauna jihar kan yin gine-gine a kan bututun ruwa a fadin jihar.   Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Usman Yunusa Lade, ya yi wannan gargadin a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban bututun ruwa dake Flower Garden, a Ilorin.   Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Sakatariyar Dindindin, Misis Christiana Asonibare, ta ce “kamar gine-gine, masallatai, coci-coci da shaguna a kan bututun ruwa da jama’a ke yi yana da illa ga samar da isasshen ruwa a fadin jihar.”   Yunusa -Lade ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar yin la’akari da bututun ruwa kafin a gina wani gini domin kaucewa lalata bututun ruwa da...
    Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.   An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi.   Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma’aikatan gwamnati.   “Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,”...
    Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bikin Sallar Eid-el-Fitr Durbar, saboda matsalar tsaro da ya sa aka dakatar da shirye-shiryen.   Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa ta karamar hukumar Nasarawa da ke Kano.   Ya kuma jaddada cewa zaman lafiya a tsakanin jama’a ya fi muhimmanci fiye da bikin Durbar.     Bayero ya yi nuni da cewa manyan Malaman addinin Musulunci da dattawa da masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisarsa suka bada shawarar a soke bikin domin a samu zaman lafiya.   Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen ziyartar...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...