Gwamnatin Filato ta dakatar da haƙar ma’adinai saboda matsalar tsaro
Published: 21st, February 2025 GMT
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025.
Ya yanke wannan shawara ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Haka kuma, ya ce yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro.
“Akwai ƙaruwar ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke haifar da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na jihar.
“Haka kuma, yawan baƙin da ke shiga yankunan haƙar ma’adanai na ƙara yawan laifuka kamar ta’addanci, garkuwa da mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji Gwamna Mutfwang.
Domin shawo kan wannan matsala, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciki waɗanda ke da izinin haƙar ma’adanai da kuma ƙirƙirar tsarin kula da ayyukan haƙar.
Gwamnan ya ƙara da cewa za su yi aiki tare da Gwamnatin Tarayya domin tabbatar da tsare-tsaren doka da kuma inganta matakan tsaro.
“Za mu haɗa kai da Gwamnatin Tarayya domin bitar yadda ake sanya ido kan ayyukan haƙar ma’adanai.
“Haka kuma, za mu tabbatar da cewa kamfanonin haƙar suna bai wa al’umma gudunmawa,” in ji shi.
Gwamnan ya yi alƙawarin duba matsalar tsaro a yankunan da ake haƙar ma’adanai gaba ɗaya tare da tabbatar da cewa kamfanonin haƙar ma’adanai suna taimaka wa al’ummomin yankunan da suke aiki a cikinsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Caleb Muftwang gwamna Haƙar Ma adanai matsalar tsaro haƙar ma adanai ayyukan haƙar
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 45 Sun Rasa Rayukansu A Wani Sabon Hari A Filato
Sai dai har yanzu rundunar ‘yansandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ƙoƙarin da samun martaninsu ya ci tura.
A gefe guda kuma, gwamnatin jihar Filato ta nuna damuwa kan hare-haren da ake samu a wasu sassan faɗin jihar, lamarin da ke ƙara haifar da damuwa a zuƙatan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp