2025-02-22@15:33:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 19

«ayyukan haƙar»:

    Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine. A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan shahidai biyu a birnin Beirut, inda ake sa ran tawagogin daga kasashe 78 za su halarta. Shugaban kwamitin da ke sa ido a jana’izar, Sheikh Ali Daher, ya sanar a ranar Juma’a cewa za a fara jana’izar a hukumance a ranar Lahadi daga karfe 1 na rana (agogon kasar). Jami’ai da dama da suka hada da shugaban kasar Lebanon da kakakin majalisar dokokin kasar za...
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025. Ya yanke wannan shawara ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Haka kuma, ya ce yawan baƙi da ke shiga yankunan da ake haƙar ma’adanai na ƙara haddasa matsalar tsaro. “Akwai ƙaruwar ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, wanda ke haifar da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na jihar. “Haka kuma, yawan baƙin da ke shiga yankunan haƙar ma’adanai na ƙara...
    Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa a gidan fensho na Dutse ya ce taron yana kara jaddada kudirin gwamnati na  tabbatar da gaskiya da inganci a tsarin tafiyar da fansho. Ya kuma jaddada mahimmancin kula da harkokin kudi da kuma bukatar samar wa wadanda suka yi ritaya kudaden fansho domin ci gaba da gudanar da rayuwarsu. “Wannan yarjejeniya ta nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da...
    Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...
    Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru  har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...
    Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
    Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya,  wato Muslim Charity For United Kingdom a turance. Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon  ilimi na zamani, da sauransu. A cewar daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, wannan shiri ya yi daidai da kokarin da gwamnati ke yi na karfafa fannin ilimi. Haɗin gwiwar zai magance matsalolin da ke addabar ilimin addinin Islama, da tabbatar da cewa makarantun Islamiyya sun sami tallafin da ya dace don samu  ingantaccen yanayin karatu da koyarwa. Ya yi nuni da cewa, Kwamishinan Ilimi...
    A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)    
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa,  zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo  muhimman  batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya. Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili na cigaba da zamansu. Shekih Na’im Kassim ya bayyana ranar 23 ga watan nan na Febrairu ta jana’izar Shahid Sayyid Hassan  da kuma shahid Hashim Safiyuddin a  matsayin ranar jaddada mubaya’a ga tafarkin da ya tafiyar da rayuwarsa a kansa da shi ne gwgawarmaya. Babban makatakardar kungiyar ta Hizbullah dai ya gabatar da jawabi ne na tunawa da jagororin Hizbullah da su ka gabata, inda...
    Binciken shiyya-shiyya na ayyukan ya nuna cewa shiyyar Kudu-maso-Kudu ta geo-siyasa ce ta kan gaba a jadawalin ayyuka 114 da aka yi watsi da su, inda Jihar Akwa Ibom ke kan gaba da ayyuka 87. An nakalto cewa kawo yanzu gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya zuba Naira biliyan 47.93 cikin ayyuka 36 na kwamitin kudi da manufofin gwamnatin tarayya (FGPC) da ya gada, da kuma Naira biliyan 4.04 cikin 51 na ayyukan gaggawa (EIPs) da ya gada daga gwamnatin da ta shude, adadin da ya kai Naira biliyan 51.96. Shiyyar Arewa maso yamma ta biyo bayansu da ayyuka 44 da aka yi watsi da su, wanda jihar Zamfara kadai ke da ayyuka 33 da ba a kammala ba....
    Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da al’umma a jihar Jigawa. Badaru wanda ya nuna gamsuwarsa matuka, ya ce gwamnatin jihar ta kammala ayyukan tituna guda 23 cikin 26 da ta gada. Ya kara da cewa sauran ayyukan tituna guda uku sun kusa kammaluwa domin amfanin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati mai ci za ta kawo karin ayyukan raya kasa, don haka akwai...
    A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai  ya taka rawar a zo a gani  wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
    “An zargi Asibitin da yin aiki ba tare da rajista ba da kuma yin ayyukan likitanci a cikin wani gidan haya da ake ganin bai dace da ayyukan kiwon lafiya ba.   “Bincike na farko ya nuna cewa, wani dattijo kuma shugaban Al’umma ya rasu sakamakon tiyata da aka yi masa a Asibitin, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa, majinyata da dama sun tsira da kyar daga bisani aka kai su wasu Asibitoci don samun kulawar gaggawa.   “Da isar su, tawagar binciken ta gano asibitin a cikin wani mawuyacin hali da rashin tsafta,” in ji shi.
    Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid  Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
    Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar. Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta. Yankin Gabashin...
۱