Aminiya:
2025-04-14@17:32:48 GMT

Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ke ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna

Published: 22nd, February 2025 GMT

Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa hukumomin tsaro na kara ɗaukar matakan daƙile matsalar a Kauru, Kachia da sauran yankunan da abin ya shafa.

Wasu sassan Abuja za su kasance cikin duhu a ƙarshen mako – TCN Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi

Ya gargaɗi duk masu bai wa ’yan ta’adda mafaka ko goyon baya da su daina, domin hukuma za ta ɗauki matakin ladabtar da su.

Sanatan ya kuma bayyana aniyarsa ta horar da matasa a fannin fasahar zamani da ICT domin su samu ƙwarewa da damar gogayya a matakin ƙasa da ƙasa.

Har ila yau, ya yaba da ƙoƙarin shugabanni da masu ruwa da tsaki wajen samar da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Kachia, wacce yanzu ke da reshe a garin Manchok.

Dangane da batun canza Asibitin Tunawa da Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Katung, ya bayyana cewa ƙudirinsa yana jiran sauraron ra’ayoyi a Majalisar Dattawa.

Ya ƙara da cewa ƙudiri makamancinsa a Majalisar Wakilai ya riga ya kai matakin karatu na uku, kuma bayan amincewar Majalisar Dattawa, za a haɗa su don gabatar wa Shugaban Ƙasa domin ya rattaba hannu.

Bugu da ƙari, Sanatan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta bai wa malaman kimiyya fifiko wajen ɗaukar sabbin malamai a makarantun sakandare domin inganta harkar ilimi.

A nasa ɓangaren, Shugaban SKJF, Ango Bally, ya ce taron manema labaran wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙungiyar na wayar da kan jama’a kan ayyukan Sanata Katung a Majalisar Dattawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gargadi Sanata Marshal Majalisar Dattawa a Majalisar

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
  • ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya godewa ministan harkokin wajen kasar Omman
  • Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
  • Yadda Ake Tuwan Amala Da Miyar Uwaidu
  • Yadda bom ya tashi da ɗan gwangwan a Legas
  • Dalilai 12 Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmanci Ga Al’umma (1)
  • Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
  • Atiku ya jagoranci manyan ’yan siyasa sun ziyarci Buhari