Tawagar Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ta Kare Matakin Sayar Da Jirgin Samanta Mara Mataki Ciki
Published: 23rd, February 2025 GMT
Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba
Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed.
Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da rahusa.
Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa: Babu wani haramcin sayar da jirgin a doka, kuma duk wata kasa da ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da shi ba wajen kai wa wata kasa hari, tana iya neman sayan jirgin.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran a Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi gargadin cewa keta hurumin Lebanon da Isra’ila ke yi barazana ne ga zaman lafiyar duniya
Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan.
Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, yana mai bayyana hare-haren a matsayin wani mummunan tashin hankali da ke barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya.
Yayin da yake ishara da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da sojojin Isra’ila suka yi, Baghaei ya ce sabbin hare-haren da yahudawa suke kaiwa a Gaza musamman a cikin ‘yan kwanakin nan, ya kara tabbatar wa duuniya cewa Isra’ila ba ta mutunta dokoki na kasa da kasa.
Ya jaddada alhakin da ke kan kasashen duniya, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na shiga tsakani da kuma dakatar da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a kan fararen hula da kuma keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta.