2025-03-28@21:12:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 548

«Iran a Majalisar Dinkin Duniya»:

    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
    Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau. An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatollah Khumeiny. A Iran ma kamar sauren sassan duniya jama’a sun fito kan tituna domin gudanar da bukukuwan ranar Qudus ta duniya, inda suke bayyana goyon bayansu ga Falasdinawa tare da yin tir da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza. An kuma yi irin wannan gangamin a kasashe da dama na yankin yammacin Asiya da suka hada da Iraki da...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai. Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta...
    A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818  sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune,  kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
    Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
    Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...
    Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci  IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban  jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha  cikin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
    Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet. “Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa. Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar. Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu. Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.” Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar...
    Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman. Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu. Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a...
    Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta. Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa. Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Sanata Lawan, ya jajanta wa mutanen da suka yi asarar dukiya sakamakon gobarar. Ya ce haƙƙinsu ne su taimaka wa juna, kuma zai ci gaba da ƙoƙari don ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu tallafin da ya dace. Ya bayyana cewa wannan tallafin zai ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
    Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin. Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar yau Laraba, inda ya haɗa wata babbar mota ƙirar DAF da babur ƙirar Jincheng. Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce tuƙin ganganci ne ya haddasa hatsarin. “Daga cikin mutum shida da hatsarin ya shafa, biyu sun rasu, yayin da ɗaya ya...
    Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura.   Yace, an sami gudunmawar  kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah.   A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu,  Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington. A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba...
    Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar. Wani jami’in Ma’aikatar Kare...
    Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus. Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin. Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar. Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin Kwamishinan yana kuma yaba masa kan ƙwazon da ya yi wajen sauke nauyin da aka ɗora masa. Kazalika, gwamnan yana yi wa Manjo-Janar Idris fatan samun nutsuwa da kwanciyar hankali a ritayar da ya yi. Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar 16 ga watan Agustan bara ne aka rantsar da Manjo-Janar Muhammad...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba. Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Armeniya Ararat Mirzoyan a Yerevan, Araghchi ya nanata cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye da Amurka ba a karkashin yanayin matsin lamba da  barazanar soji, da kuma kakaba takunkumi. Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Duba daga  rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan watan na Maris. Wani jirgin ruwa, Hafnia Andromeda, ana kyautata tsammanin zai isa tashar Everglades a ranar 29 ga Maris tare...
    Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025. Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54. An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI). A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025. A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum...
    A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa.  Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980. Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023,  Ƙarƙuzu...
    Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar  Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe. Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom. Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa. Wannan sakamako na nufin cewa Nijeriya na matsayi na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a...
    Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya Duba daga  rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan...
    A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin. A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar. Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain.  Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI...
    Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun. Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata. Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a...
    Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu.  A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar. Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa. Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin...
    Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu. Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su...
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu. Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu. Ya sanar...
    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu mutum 2,000 sabbin kamuwa da cutar SIDA duk rana a faɗin duniya. MDD ta ce tana wannan gargaɗi ne sakamakon matakin Amurka na katse taimakon agajin ƙasashen duniya ƙarƙashin Hukumar ta USAID. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas MDD ta ce ce tilas ne a maye gurbin taimakon idan ana neman kare duniya daga shiga annobar cutar ta AIDS.. Hukumar ta ce muddun Amurka ba ta dawo da tallafin daƙile cutar ba, kuma ba a samu maye gurbin taimakon na Amurka ba, nan da shekaru huɗu za a samu kimanin mutane...
    Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai linzami guda biyu da suka hada da Zulfiqar mai gudun tsiya. Ya kara da cewa hare-haren na goyon bayan Falasdinawa ne a Gaza. Saree ya yi nuni da cewa, dakarun kasar Yemen sun kuma kai hari kan jirgin yakin Amurka Harry S. Saree ya ce harin da aka kai kan jiragen ruwan yakin Amurka shi ne irinsa na biyu cikin sa’o’i 24 da suka gabata....
    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ya yi gargadin cewa hana shigar da kayayyakin jin kai da Isra’ila ta yi a zirin Gaza ya jefa yankin cikin mawuyacin hali na rashin abinci. “Makonni uku kenan da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da kayayyaki cikin Gaza. “Ba abinci, ba magani, ba ruwa, babu man fetur,” inji Philippe Lazzarini a cikin wani sako a shafukan sada zumunta. Tun a ranar 4 ga watan Maris ne Isra’ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa Gaza, bayan karewar kashi na farko na tsagaita bude wuta a yarjejeniyar da ta cimma da kungiyar gwagwarmayar falasdianwa ta Hamas data kunshi musayar fursunoni tsakanin bangarorin. Lazzarini ya jaddada cewa al’ummar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam. A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai. Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a...
    A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum, inda wani dan jarida ya yi tambaya game da ko Sin za ta shiga tattaunawa da Amurka, game da hakan Guo Jiakun ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na da imanin cewa, kiyaye zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa a dangantakar Sin da Amurka, ya dace da moriyar jama’ar kasashen biyu, da kuma fatan al’ummomin duniya baki daya. Dangane da rikicin Ukraine kuwa, Guo Jiakun ya ce a baya-bayan nan, kungiyar “Kawancen zaman lafiya” kan rikicin Ukraine ta gudanar da wani taro a birnin New York, domin tattauna halin da ake ciki game da...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin. He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen...
    Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan. Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye,...
    Ebrahim Rasool, jakadan Afirka ta Kudu da gwamnatin Trump ta kora, ya samu tarba a wannan Lahadin daga daruruwan magoya bayansa da suke rera wakoki  domin karrama shi a filin jirgin sama na Cape Town. Jama’a sun kewaye Rasool da matarsa ​​Rosieda bayan isowarsu, yayin da ‘yan sanda suka yi musu rakiya har zuwa tashar jirgin kasa. Da yake yiwa magoya bayansa jawabi, Rasool ya ce, Abin da ya faru yana a matsayin wulakanta ku ne ku al’ummar Afirka ta kudu, amma kuma idan kuka tsaya tsayin daka kan manufofinku na ‘yancin kai to za ku ci gaba da rayuwa a cikin mutunci da daukaka. Ya ce ba laifi muka yi ba, ammam kuma mun dawo gida ba tare da...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita. “A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza. Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tare da hana kai agajin jin kai a yankin  a matsayin keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu. Ya kuma yi kira da a dauki matakin gaggawa a duniya kan yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin baki daya. Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, amma ta...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.  Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
    Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Islami yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan ci gaban kari ne, kan ci gaban da kasar ta samu a wannan fannin, wanda kuma zai kara kyautata bangaren lafiya na kasar sannan ya zama hanyar samar da kudade ga kasar. Shugaba hukumar makamashin nukliya ta Iran ya kara da cewa a cikin shekarar Iraniyawa wanda ya kara kadai kasar...
    Ya sanar cewa karamar hukumar ta kuduri aniyar daukar tsauraran matakai don dakile wannan barazana ta hanyar tura jami’an GOSTEC da Operation Hattara don inganta tsaro.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan. An kashe shi ne tare da matarsa ​​a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza. Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa...
    Allah Ya yi wa mahaifiyar Gwamnan Katsina, Dikko Umar Radda rasuwa. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahaifiyar Gwamnan, Hajia Safara’u Umar Radda, ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Katsina. Cikin wani saƙo da tsohon mai magana da yawun gwamnan, Isah Miqdad ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Hajiya Safara’u ta riga mu gidan gaskiya bayan ta yi fama da doguwar jinya. Mabiya dandalan sada zumunta na ci gaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Hajiya Safara’u.
    Iran, ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a wani masallaci a kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa masallata. Akalla mutane 44 ne suka mutu yayin da 13 suka jikkata a harin da aka kai a kauyen Fonbita da ke cikin kauyan Kokorou dake jihar Tillabery wanda ya faru a lokacin da wasu ‘yan ta’addan na kungiyar Da’ish a yankin Sahara (ISGS) suka far wa masallacin, inda suka auka wa masu ibada dake sallar Juma’a. Baghaei ya bayyana cewa, wannan ta’addancin da aka aikata a lokacin sallar Juma’a ya saba wa ka’idar Musulunci, kuma ya saba wa...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    Wani ɗan ƙasar Turkiyya da ya rasa gidansa sakamakon wata gagarumar girgizar ƙasa a shekarar 2023, ya shafe shekara biyu yana zaune shi kadai a cikin wani ƙaramin kogo saboda yana ganin ya fi kowane gini da mutum zai yi karko.  A watan Fabrairun 2023, Kudancin Turkiyya ya fuskanci ibtila’in girgizar kasa mai karfin 7.8 da ta yi sanadiyyar mutuwar dubun-dubatar mutane tare da mayar da daukacin unguwanni tamkar kufai. An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan Ali Bozoğlan, mahaifin ‘ya’ya uku daga lardin Hatay da ke kudancin kasar, ya rasa gidansa sakamakon girgizar kasar da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu 2023....
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
    Kyari ya ci gaba da cewa, wannan bangare na noma don samun riba; shi ma zai amfana da Naira biliyan 500, wanda ya kai kimanin dala biliyan 300, wanda su ma wadannan kudaden za a bai wa Bankin Aikin na Noma. Kazalika, Kyari ya yi kira ga Bankin EBRD, da ya zuba hannun jari a fannin aikin noman kasar, domin kasar ta cimma burin da ta sanya a gaba, musamman domin Nijeriya ta rage asarar da take yi a yayin girbin amfanin gona da samar da kayan aikin noman rani da sauran makamantansu. Dakta Heike Harmgart, Manajan Daraknatan Bankin na EBRD da ke kula da yankin Afirka, wadda kuma ta jagoranci tawagar a nata jawabin ta ce, tawagar ta kawo...
    Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa...
    Wata karya ta hadiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka makale masa a mukamuki – lamarin da ya haifar da yi masa tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana. Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon hadiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram. Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Lokacin da ta fara amai,...
    Ya kuma kara da cewa dorewar tsarin dimokiradiyya na bukatar hadin gwiwa daga kowane bangare, “Jam’iyyun siyasa su ne ginshikin dorewar dimokiraɗiyya, kuma yayin da hamayya take da muhimmanci a lokacin zabe, dole ne mu hada kai wajen gina kasar mu, hakan ya sa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda babban jami’in dimokiradiyya ne yake mutunta gasa mai tsafta, amma kuma ya na fifita hadin kai da ci gaban kasa fiye da komai. Shugaban IPAC na kasa, Honourable Yusuf Dantalle, ya ce shirin fim din na tarihi zai bayyana ci gaban da aka samu a fannonin gina ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, da hadin kan al’umma, ya kuma ci gaba da “Fim din zai zama wani muhimmin tarihin kasa,...
    Bubu da kari, abin mahimmancin shi ne, shi talakan Nijeriya zai iya gani a kas na irin wadannan shirye-shiyen da gwamnatin ke son aiwatarwa?   Fannin Da Gwamnatin Za Ta Zuba Kudaden: A kasafin kudin na 2025, Gwamnatin Tarayya ta warewa bangaren tsaro Naira tiriliyan 6.11 wanda ya kai ta samar da karin kaso 88 daga cikin kasafin kudin da ta warewa fannin na Naira tiriliyan 3.25 a 2024. Shin wannan burin na Gwamnatin zai iya cika, duba da yadda aka gaza dakile ta’addanci, ‘yan fashin daji, wanda idan ba a mayar da hankali ba, a 2025, tarihi ne zai sake mai-maita kansa. An ware Naira tiriliyan 5.99 a cikin kasafin kudin don yin tituna, gadoji da kuma manyan ayyuka...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen. A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen. Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin...
    Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion. Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza. Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu  linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman...
    Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata. Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa...
    Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki. Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda. Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin...
    Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da kama Mista Peter Dike da ake zargi da kashe matarsa ​​a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi, Marogbo. Rundunar ’yan sandan a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidan nasu sanadin taƙaddama a ranar Laraba. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Shahararren ɗan kasuwa Nasiru Ahali ya rasu a Kano Wannan mummunan al’amari ya ƙara dagula al’amuran tashin hankali a cikin gidan ma’aratan da ya kawo sanadin mutuwar matar aure. A watan Oktoban 2024, an kuma kama Motunrayo Olaniyi da laifin daɓa wa amaryarsa, Olajumoke wuƙa har...
    Allah Ya yi wa Alhaji Nasiru Ahali, Shugaban Kamfanin Mainasara & Sons, rasuwa. Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108. Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP A cewar majiyoyin na kusa da iyalan marigayin ɗan kasuwar ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis. Ana girmama Ahali a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masanin asalin masana’antu a Kano. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin kasuwanci na yau da kullun. A tattaunawarsa da Daily Trust a shekarar 2018, marigayi Ahli ya bayyana cewa sana’arsa ta haɗa da buga littattafai, bugu takardu, masana’antar bulo, sana’ar...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da...
    Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gabaci da kuma kudancin kasar Lebanon wanda yak eta yarjeniyar zaman lafiyan da HKI ta cimma da kungiyar Hizbullah mai lamba 1701 ta shekara ta 2006. Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon na cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan bayan kauyen taraya a gundumar ba’alabak, cikin lardin Ba’alabak Hermel, da kuma kan garin Shaara kusa da garin Jenta a dai dai kasar tsaunuka da ke yankin. A kudancin kasar Lebanon kuma jiragen yakin HKI sun jefa makamai masu linzami har guda 4 a kan yakunan Jibaa da Snaya Kafafen yada labaran HKI sun tabbatar da wannan labarin sun kuma nakalto sojojin kasar suna...
    Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri,  da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki. Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu. Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.
    Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa. Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci. Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai...
    Wannan hazaka, da hangen nesa na kasar Sin, sun ci gaba da zama ginshiki na ingiza jagorancin dukkanin manufofin kare hakkin bil Adama a duniya, kana hakan zai ci gaba da zama muhimmiyar gudummawar kasar Sin ga duniya, a bangaren kare hakkin rayuwa da walwalar daukacin al’ummar duniya.(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa  ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara ta Farisa a yammacin wannan Alhamis. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada bukatar gwamnati da al’ummar kasar su ci gaba da zuba jari don karfafa azamarsu wajen tunkarar takunkumai na zalunci da masu girman kai na duniya suka kakaba ma kasar. Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa samar da kayayyaki na samun bunkasuwa ne idan aka ba da tallafin jari mai karfi. Jagoran ya kuma...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
    Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki. Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro. ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal. Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan. A yanzu haka yana ganawar sirri...
    Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, rundunar ta yi matukar jimamin hatsarin motar da ya afku a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin karfe 6:58 na yamma kafin gadar Nyanya. Ta kuma ce, ofishin hukumar na Karu ya samu...
    Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin, da yadda ake gaggauta karewa da amfani da kayayyakin al’adu na tarihi da aiwatar da ra’ayin dunkulewar al’umomin Sinawa. Lambun renon furanni mai aiki da fasahar zamani na Lijiang na da fadin hekta 73.3, wanda ya hada aikin shuka da sufurin furanni da yawon bude ido tare, kuma ya habaka aikinsa zuwa harhada man furanni da samar da busassun furanni da sarrafa abinci mai hade...
    Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma  Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa. Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI. Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar...
    A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
    Shugaban kwamiti na musamman dangane da yaki a Ukrai ya bayyana cewa kasar Rasha ta aikata laifukan yaki a yakin da take fafatawa a kasar Ukraine shekaru uku da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai, Africa News’ ya nakalto Erik Mose ya na fadar haka a taron kwamitin da yake jagoranra danagen da yaki a Ukraine a birnin Geneva a jiya Laraba. Mose a fadawa kwamitin mai mutane 47 kan cewa, ya sami shaidu wadanda suke tabbatar da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatin kasar Rasha ta azabtar da wasu yan kasar  Ukraine wadanda ta kama a yankuna guda 3 na Ukraine da ta kwace, kuma jami’an tsaron rasha sun azabtar da su, wasu kuma an...
    LEADERSHIP ta tattaro cewa, kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan. An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi. A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ta yi kakkausar suka ga sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai bayyana su a matsayin “ci gaba da kisan kiyashi da share wata al’umma a yankin da aka yi wa kawanya. Baghaei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i bayan harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara. Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ke da alhakin kashe-kashen da ake yi a Gaza, yana mai cewa, ana kai hare-haren na Isra’ila ne da tare da goyan bayan Washington. Baghaei ya kuma yi kira ga...
    Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan yankin Falasdinu. Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun karbe iko tare da fadada shi zuwa tsakiyar hanyar Netzarim, da nufin fadada yankin tsaro da samar da wani bangare na raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza. A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargadin karshe ga Falasdinawa a zirin Gaza, inda ya bukaci da su sako Isra’ilawa da suke garkuwa da su, su kuma kawar da kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa. “Idan ba a sako dukkan mutanen Isra’ila da aka yi...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin. Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine. “Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma  “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network. Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa...
    Ga shi dai kwanakin Ramadan suna ta gudu, har mun kawo ga goman ƙarshe wanda shi ne dama ta ƙarshe ga wanda ya yi sakaci a farkon watan, ko kuma ya zama cikon alheri ga wanda ya kyautata ya bayar da abin da ake so a baya. Ya ku masoya! Goman ƙarshe na watan Ramadan kasuwa ce babba da masu tsere suke tserereniya a cikinta. Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa DAGA LARABA: Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al’ada Lokaci ne da wanda ya yi sakaci yake ƙara ƙwazo a cikinsa, ake jarraba masu himma a cikinsa, ake tantance ma’abota Lahira da ma’abota duniya. Da yawa masu huɗuba sun...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas. An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba. Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas  Naɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar. Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida. Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba,...