Iran ta yi gargadin cewa zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa kasar Labanon na da matukar hadari kuma barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin da ya dace.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya yi kakkausar suka kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a sassa daban-daban na kasar Lebanon, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama a kasar a baya-bayan nan.

Baghaei ya alakanta hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa kan kasashen Labanon da Siriya da yunkurin kisan kiyashi da Tel-Aviv ta yi a baya-bayan nan a Gaza da kuma gabar yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, yana mai bayyana hare-haren a matsayin wani mummunan tashin hankali da ke barazana ga zaman lafiyar yankin da ma duniya baki daya.

Yayin da yake ishara da keta yarjejeniyar  tsagaita bude wuta da sojojin Isra’ila suka yi, Baghaei ya ce sabbin hare-haren da yahudawa suke kaiwa  a Gaza musamman a cikin ‘yan kwanakin nan, ya kara tabbatar wa duuniya cewa Isra’ila ba ta mutunta dokoki na kasa da kasa.

Ya jaddada alhakin da ke kan kasashen duniya, musamman kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, na shiga tsakani da kuma dakatar da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa a kan fararen hula da kuma keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: hare haren da Isra ila ke

এছাড়াও পড়ুন:

 Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a

Sojojin HKI sun kai wasu hare-hare akan sansanin sojan Sanamain dake gundumar Dara’a a kudancin kasar Syria.

Tashar talabijin din da “ Akhbariyyah” ta Syria ta sanar a yau Litinin cewa; sojojin Isra’ila sun kai hari akan sansanin soja na “Sanamain” wanda yake a gundumar Dar’a, kuma an ga jiragen sama na ‘yan mamaya masu yawa suna shawagi a samaniyar yankin.

Wata majiyar ta Syria ta kuma ambaci cewa; sojojin na HKI sun kursa cikin garin Mu’arrah, tare da  yin kutse cikin gidaje masu yawa a ciki da gudanar da bincike a cikinsu.

A yankin Kunaidhara ma an ga sojojin na mamaya suna yin kutse, haka nan kuma sun kai hari akan filin saukar jiragen sama na Tpor, da kuma wani filin saukar jiragen sama na soja a Tadammur.

Tun bayan da gwamnatin Basshar Assad ta fadi ne dai HKI ta bude kai wa makamai da cibiyoyin sojan kasar hare-hare babu kakkautawa. A cikin kwanakin farko na faduwar gwamnatin Asad, sojojin HKI sun sanar da cewa sun rusa tsakanin kaso 70% zuwa 80% na jumillar makaman da Syria take da su, na sama, kasa da na ruwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
  •  Syria: Isra’ila Ta Kai Hari A Kan Sansanin Soja A Yankin Dar’a
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin 
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • Ana ci gaba da gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falastinu a kasashen duniya
  • Duniya na ci gaba da yin tir da Isra’ila kan dawo da hare-harenta a Gaza
  • Iran Ce Kasar Wacce Ta Fi Shigar Da Kayakin Kasuwanci Zuwa Kasar Afganistan A Shekarar Da Ta Gabata
  • Araghchi : Ya kamata Duniyar Musulmi ta dauki mataki mai karfi kan Isra’ila
  • Iran ta yi Allah-wadai da harin ta’addanci da aka kai a wani masallaci a kudu maso yammacin Nijar