Aminiya:
2025-04-15@14:11:26 GMT

Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba

Published: 23rd, February 2025 GMT

Jami’ar Sojojin Nijeriya da ke Biu (NAUB) ta ƙaddamar da taron magance zamba ta hanyar binciken fasaha karo na farko, wanda ya nuna ƙaruwar tasirin wannan jami’a a fagen ilimi a Nijeriya.

Taron ya gudana ne bisa taken “Kididdigar Forensic: Zuwa Ga Sabon Tsarin Magance da Gano Zamba,” wanda Farfesa Ahmad Imam, ƙwararre a fannin ƙididdigar kuɗi da magance zamba ya gabatar.

Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe

Tattaunawar ta jaddada dabarun zamani domin tunkarar zamba mai salo da kuma tsare-tsaren da za su taimaka wajen gano da magance laifukan kuɗi da ke ƙara ƙamari.

Shugaban Jami’ar NAUB, Farfesa Kyari Mohammed, ya bayyana wannan taro a matsayin wani muhimmin mataki ga jami’ar.

A cewarsa: “Abin alfahari ne mu yi bikin wannan muhimmin taro na farko, wanda ke nuna jajircewar NAUB wajen habaka ilimi da warware matsalolin al’umma.”

Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Farfesa Adamu Isa Harir, ya bayyana taron a matsayin wata al’ada mai cike da tarihi a fagen ilimi.

Ya ce: “Wannan taro ba wai kawai nasara ce ga jami’a ba, har ila yau, yana nuna muhimmancin bincike da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi ga al’umma.”

Farfesa Ahmad Imam ya jaddada bukatar sabon salo wajen yakar zamba, tare da bayyana yadda zamani ke buƙatar sababbin hanyoyin daidaitawa da matsalolin laifukan kudi a duniya da ke sauyawa cikin sauri.

A jawabin godiya, Magatakardar Jami’ar, Birgediya Janar H.Y. Abdulhamid, ya gode wa dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen samun nasarar taron.

A cewarsa: “Muna matukar godiya da goyon bayan shugabannin jami’a da kuma kokarin ma’aikata wajen tabbatar da nasarar wannan taro.”

Haka kuma, Shugaban Sashen Kididdiga, Dakta S.J. Inyada, ya gabatar da kyauta ta musamman ga Farfesa Ahmad Imam a matsayin yabo kan gudunmawarsa a fannin kididdigar bincike ta hanyar fasahar zamani.

Dakta Inyada ya yaba wa Mataimakin Shugaban Jami’ar da shugabannin jami’a bisa jajircewarsu wajen inganta bincike da harkokin ilimi a jami’ar.

Wannan taro ba wai kawai ya zama wani babban ci gaba ga NAUB ba, har ila yau, ya tabbatar da alkawarin jami’ar na ci gaba da girmama bincike, kirkire-kirkire, da kawo sauyi mai ma’ana ga al’umma.

Wannan ya tabbatar da rawar NAUB a matsayin jagora wajen bunkasa bincike da ilimi a Nijeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar Sojoji jihar Borno wannan taro

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran.

Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage.

Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 ta jikkata 69 a awa 24 a Gaza
  • Ministan Harkokin Noma Na Kasar Iran Ya Kama Hanya Zuwa Kasar Brazil
  • Sabon Shugaban Kasar Gabon Ya Bayyana Shiransa Na Kawo Sauyi Mai Kyau A kasar
  •  Aljeriya Ta Kori Jami’an Diflomasiyya Faransa 12
  • Tsangayar Ilimi Ta BUK Ta Yi Bikin Cika Shekaru 50 Da Kafuwa
  • Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Yi Watsi Da Matsawa Sauran Kasashe Lamba
  • Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12
  • Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato
  • Shugaban Kasar Iran Ya Mika Ta’aziyyar Ta Rasuwar Wanda Ya Assasa Hukumar  Makamashin Nukiliya Ta Iran
  • Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri