2025-04-18@16:54:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3465

«Jami ar Sojoji»:

    A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i. Har ila...
    Ndume, ya yaba wa jarumtakar dakarun Nijeriya, amma ya buƙaci ƙarin matakan tsaro. Ya buƙaci gwamnati ta taimaka wa ƙungiyoyin tsaron al’umma da kayan aiki da makamai na zamani. Wannan harin na daga cikin jerin hare-haren da ake fama da su a Jihar Borno a cikin ‘yan kwanakin nan. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali a unguwar Otobi da ke Ƙaramar hukumar Otukpo biyo bayan wani mummunan hari da ya tilastawa mazauna garin barin gidajensu. Kakakin rundunar ’yan sandan, CSP Catherine Anene a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakiliyarmu, ta kuma yi watsi...
    Ya yi bayanin cewa aikin hanyar mai nisan kilomita 700 da ya tashi daga Abuja ya wuce Kaduna ya nufi Zariya zuwa Kano zai yi matukar rage yawan aukuwar hatsari da cunkoson ababen hawa da zarar aka kammala shi. “Muna da sashe na 1, 2, 3. Sashi na 1 yana Abuja da Neja, sashe na...
    Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce...
    Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen...
    Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara...
    “Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari...
    Adadin wadanda suka mutu sakamakon luguden wuta da Amurka ta yi kan tashar jiragen ruwan Ra’as Issa ta Yemen ya kai mutane 38 Ofishin kula da kiwon lafiya na lardin Al Hudaidah ya watsa rahoton cewa: Adadin mutanen da suka yi shahaida da wadanda suka jikkata sakamakon harin da Amurka ta kai kan cibiyar man...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin...
    Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin...
    Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kawo sauyi da kuma zamanantar da kafafen yada labarai na Najeriya da watsa shirye-shirye ta hanyar hadin gwiwa da inganta fasaha.   Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris ne ya bayar da wannan tabbacin a taron manema labarai na 2025 da aka gudanar...
    Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta tura jami’ai 415 a fadin jihar domin tabbatar da tsaro a duk lokacin bukukuwan Easter.   Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar jihar, ASCII Umar Mohammad M. ya fitar, ya ce jami’an sun jibge a...
    Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a...
    Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar,...
    Masarautar Gumel ta ce za ta bayar da dukkan goyon baya da hadin kai da ake bukata domin ci gaban yankin kasuwancin da ba shida shinge na Maigatari a jihar Jigawa.   Mai Martaba Sarkin Gumel Alhaji Ahmad Mohammad Sani ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin Jiha mai kula da...
    Cibiyar Nazarin Dimokuradiyya ta Aminu Kano a Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta shirya taron shekara-shekara karo na 23 don tunawa da cika shekaru 42 da rasuwar Malam Aminu Kano.     A nasa jawabin, Shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya jaddada muhimmancin taron shekara-shekara wajen kiyaye manufofin da Malam Aminu Kano ya tsaya...
    Gwamnatin jihar Neja za ta fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama daga sabon filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu da aka kaddamar a Minna, tare da kamfanin Overland Airways Limited.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in kula da zirga-zirgar jiragen sama na Overland, Captain Edward Boyo ya raba wa...
    Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu. A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa. Masana’antun...
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan...
    Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar. Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa, Iran a shirye take yin aiki tare da Saudiyya a dukkanin bangarori, domin cin gajiyar al’ummomin kasashen biyu da ma duniyar musulmi, tare da yin ishara da cewa, dukkanin ci gaban da Iran ta samu a dukkanin bangarori na ilimin kimiyya da fasaha,...
    Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin. A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Saudiyya za su iya zama abin koyi ga hadin gwiwar yankin, yana mai jaddada cewa hadin kan kasashen musulmi wani lamari ne da ake bukata don samun zaman lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa a yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan...
    Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya. Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027. Cikin wani jawabi da mai...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya mika rubutacciyar wasikar jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ga shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Araghchi, wanda ya je birnin Moscow a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don ganawa da wasu manyan jami’an Rasha, ya gana da Putin a yammacin ranar Alhamis. Ministan ya gabatar da...
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin...
    Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa. Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da...
    Mata da ’yan mata da suka tsira daga tashin hankalin ‘yan Boko Haram a Arewa Maso Gabashin Nijeriya na fuskantar matsaloli masu yawa, ciki har da shiga tsananin damuwa da fuskantar nuna wariya da rashin samun dama na neman kuɗi da kuma uwa-uba rashin samun kulawar gwamnati da na al’umma. A lokacin tashin hankali da...
    Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni  ta sayo ton 2,000 na hatsi iri-iri domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da shirin tunkarar kakar bana a matsayin gudun ko ta kwana. A cikin wata sanarwa da Yusuf Ali, mai bada shawara ta musamman kan harkokin dabarun sadarwa na zamani (SSA) ga...
    He Yongqian ta kara da cewa, bangaren Sin na fatan kokari tare da bangaren Turai, don kiyaye tsarin cinikayya bisa ra’ayin bangarori daban daban tare da kungiyar WTO a matsayin tushensa da bin ka’idojin cinikayya.   Game da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137, wanda aka fi sani...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun...
    Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da...
    Wasu ’yan ta’addan da ake zargin suna da alaƙa da ISWAP sun tayar da wata na’ura mai fashewa a kan gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa da tsakar daren wayewar garin ranar Talata. Kamar yadda majiyar Zagazola Makama ke cewar, wannan harin na bam da waɗannan ‘yan ta’addan suka jefa ya lalata...
    Ban da wannan kuma, alkaluman PMI wato masu bayyana yanayin sayayya da ake ciki ta fuskar sana’o’in samar da kayayyaki a watan Maris ya samu karuwa cikin watanni 2 a jere, matakin da ya bayyana bukatun kasuwanni na kara samun kyautatuwa. Har ila yau, Sin ta kafa cikakken tsarin sana’o’i, da ingantattun manufofin dake da...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Malaysia daga ranar 15 zuwa 17 ga wata. Inda bangarorin biyu suka amince da gina al’ummar Sin da Malaysia mai kyakkyawar makomar bai daya bisa manyan tsare-tsare da samar da wasu sabbin shekaru 50 masu muhimmanci na dangantakar da ke tsakanin Sin da Malaysia....
    “Na gode Allah, babu wanda ya jikkata, kuma an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda.” Ofishin yaɗa labaranta ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce “ƙoƙarinta na kare gaskiya da wakiltar al’ummarta bai kamata a mayar da shi barazana ko tashin hankali ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bada muhimmanci game da tattaunawa da ita kuma a shirye take ta magance matsaloli da takaddamar da ake yi kan Shirin makamashin nukiliyarta Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Kazim Gharibabadi ya bayyana cewa: zagayen farko na tattaunawar da ba na kai tsaye ba da aka gudanar a birnin...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta yi kira ga Birtaniya da ta kama ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Hind Rajab ta gabatar da bukatar fitar da sammacin kame ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar da yake ziyara a Birtaniya. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto...
    Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin...
    Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar...
    Bugu da kari, illar matakin na Amurka na iya gurgunta salon hada-hadar kudade, da kwadago, da kirkire-kirkire da kasuwannin kasa da kasa ke cin gajiyarsu.   Bisa la’akari da tarihi, mun san cewa Sin da Amurka kasashe ne dake da banbance-banbance ta fuskar ci gaba, da yanayin gudanar masana’antu da karfin tafiyar da su, amma...
    A ranar 17 ga watan Afrilun nan, yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi jinping a kasar Cambodia, an yi bikin kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Cambodia, wanda CMG ya shirya a birnin Phnom Penh.   Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali. “Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da...