DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa
Published: 26th, February 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”.
A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa.
Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haihuwa mazan da basa son haihuwa tazaran haihuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu
Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu.
Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.
Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojojiKakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar.
Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da gidan Galadiman Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhininsa kan rasuwar Galadanci, tare da bayyana irin rawar da ya taka a gwamnatinsa.
“Rasuwar Abdullahi Tanka Galadanci babban rashi ne ga gwamnatina da Jihar Kano baki ɗaya.
“Za a yi rashinsa saboda jajircewarsa da ƙwazon da ya nuna wajen inganta harkokin sadarwarmu,” in ji gwamnan.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwa da abokan arziƙi.