2025-02-26@12:24:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1094
«mazan da basa son haihuwa»:
A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya taron kwamitin zartaswa na kasa wanda ake sa ran za ta yi ranar Laraba, jam’iyyar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na iya neman shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa. Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya...
Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa. “A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane...
Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa. A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da...
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen Damascus babban birnin kasar da kuma lardin Deraa da ke kudancin kasar. Hare-haren dai ya biyo bayan kiran da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na karbe yankin kudancin Siriya...

Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa...
Baya ga Messi shi ma Luis Suarez ya fuskanci hukunci bayan tuhumarsa da laifin dukan Birk Risa a wuya duk dai a wannan karawar tsakaninsu da New York, Messi ya koma Inter Miami daga PSG shekaru biyu da su ka gabata, tun bayan zuwanshi Miami Messi ya zura kwallaye fiye da 20 sannan ya taimaka...
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna. Natasha ta shigar da ƙarar ne gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick. Mutum 10 sun...
Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano irin muhimmiyar gudunmuwar da kungiyoyin hadaka ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma karfafa jama’a a kasar. Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horo na musamman ga shugabanni, kwamitocin gudanarwa, da...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage...
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan...
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin. A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara...
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar...
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo. Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu...
Sakamakon binciken da kwamitin ya yi, zai tantance matakin da za a dauka na gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da...
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin...
Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun ‘yan talla da masu kananan sana’o’i. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar. Mohammed Umar Bago...
Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi hadin kan al’umma don gina kasa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kaucewa cin hanci da rashawa ba. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC)...
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware. Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe. Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala. Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da biyar na kananan hukumomi ashirin da uku a matsayin doka. Shugaban Majalisar, Alhaji Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa an kara kasafin kudin zuwa sama da naira biliyan dari da ashirin da...
Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura. Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu...
Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad. Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya...
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a ranar Litinin ya halarci bikin kaddamar da gina yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari, inda ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na bunkasa masana’antu a kudancin Afirka. Kamfanin Xintai Resources na kasar Sin ne ya zuba jarin dala biliyan 3.6 a yankin masana’antu musamman na...
An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri. Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana...
Waɗanda Suka Yi Nasara 1. Aliyu Usman Adam – Matsayi na Ɗaya Aliyu Usman Adam, ɗan asalin Zariya, Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a 2008. Bayan hidimar ƙasa a Jihar Edo,...
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu. Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana wa taron...
Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba. Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na...
Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu. Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce za ta fara gudanar da bincike kan kocin Fenerbahce Jose Mourinho bayan da ta zarge shi da furta kalaman wariyar launin fata bayan da ƙungiyoyin suka tashi 0-0 ranar Litinin. Zuwa yanzu dai ba a bayyana irin kalaman da Galatasaray ke nufin Mourinho da furtawa ba, da yake...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban...
Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin...
Fiye da mutane 7,000 da yawancinsu fararen hula ne aka kashe a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga watan Janairu, in ji Firaminista Judith Suminwa Tuluka a ranar Litinin. Mambobin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun kwace iko da yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo masu arzikin ma’adinai da suka hada...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai kwamitin ya kada kuri’ar amincewa da kudurin na Amurka da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin Ukraine da Rasha. Kuri’u 10 ne suka amince da kudurin,...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa...
’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper...
nkin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a...
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031. A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba. Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa,...
Gwamnatin Trump ta saka sabbin takunkumai kan wasu mutane da ke da alaka da wani kamfanin fitar da mai na Iran. Takunkuman sun shafi mutane 22 da jiragen ruwa 13 da ke da alaka da masana’antar mai ta Iran. Wadannan takunkumin wani bangare ne na matsin lamba na shugaban Amurka Donald Trump kan Iran. Ma’aikatar...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen...
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya...