Jum’ar Nan Ce Duban Farin Na Watan Ramadan – Mai Alfarma Sarkin Musulmi
Published: 27th, February 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa ko Sarki mafi kusa domin sanarda Mai Alfarma Sarkin Musulmi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata, yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga daukacin Musulmin kasar.
Za iya amfani da lambobin nan kai tsaye don sanarda Mai Alfarna Sarkin Musulmi labarin ganin wata
08037157100, 08066303077, 08035965322, 08099945903, 07067146900
NASIR MALALI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Duban Fari Ramadan Wata Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
Fani-Kayode ya zargi Isra’ila da Hannu a tashe-tashen hankula a Najeriya
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya.
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci.
Fani-Kayode ya yi gargadin cewa, rikicin da ake fama da shi na da kamanceceniya da yadda aka kirkiri tashe-tashen hankula a zabukan shekarar 2015, inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fuskanci irin wannan tashin hankali.
“Haka aka shirya a shekarar 2014 kafin a kayar da Goodluck Jonathan, yanzu kuma sun fara shirin irin haka domin tunkarar 2027,” in ji shi. “Mun san su wane ne, kasashen waje ne daga cikinsu har da kasashen Yamma da Isra’ila, da wasu da dama. Ba sa son kwanciyar hankali a Nijeriya.” In ji Femi Fani-Kayode.