Abubuwan Da Suka Ta Da Kura A Litttafin Janar Babangida
Published: 28th, February 2025 GMT
Har ila yau, a cewarsa; Abiola ya samu mafi yawan kuri’u tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata, domin zama shugaban kasa. “Babu tantama a zuciyata, Abiola ne ya lashe wannan zabe tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata”, in ji IBB.
Kazalika, ya kuma bayyana farin cikinsa; kan yadda Buhari ya karrama Abiola da lambar yabo mafi girma ta GCFR, wadda ake bai wa shugabannin kasa.
“Ko shakka babu, Mashood Abiola shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a 1993, da kuri’u sama da miliyan takwas a jam’iyyasa ta SDP, inda ya samu nasara a kan abokin karawarsa, Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC”, in ji Babangida.
A jawabinsa na godiya, IBB ya bayyana rushe zaben 1993 a matsayin wani abu da ya yi yake kuma da-na-sanin yin sa a rayuwarsa.
Har ila yau, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya bayyana dalilinsa na kifar da gwamnatin Buhari, duk kuwa da cewa; shi ne babban hafsan sojin kasar a 1985.
Guda daga cikin dalilan nasa su ne, a babi na shida ya bayar da hujjar cewa; juyin mulkin, wani martani ne ga korafe-korafen ‘yan Nijeriya na bakar azaba da wahalar da suka sha da kuma tabarbarewar al’amuran kasar baki-daya.
“A farkon shekarar 1985, ‘yan Nijeriya sun fara fargaba game da makomar kasarmu, wanda al’amuran suka kasance a matsayin masu matukar hadari, wanda kuma hakan yanzu ma alamu ne a fili na irin wancan hatsari.
“Babu shakka, a bayyane yake ga shugabancin sojoji cewa, aikin da muka yi da nufin ceto kasarmu a shekarar 1983 ya tarwatshe”, kamar yadda ya rubuta a littafin.
Ya kara da cewa, rashin daukar mataki zai iya kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin sojoji, wanda a ganinsa; hakan kan iya haifar da mummunar illa ga kasar.
“Idan sojoji suka samu rarrabuwar kai, al’ummar kasa za su bi sahunsu; sannan abin da zai biyo baya na iya kasancewa mai matukar ban tsoro da ba a taba tunani ba”, a cewarsa.
IBB, ya ci gaba da bayyana cewa, a shekarar 1983; sojoji sun hambarar da gwamnatin Shehu Shagari ne cikin hadin kai, amma sai aka fara samun rarrabuwar kawuna a tsakaninsu daga bisani.
“A matsayin sojoji na wadanda aka sani da hadin kai, sai ga shi kuma an fara samun guna-guni a tsakaninsu, wannan ne yasa dole a yi wani abu, don gudun kada mu rasa kasar”.
Babangida ya ce, “Babban abin da na ji tsoro shi ne, samun rarrabuwar kawuna da ra’ayoyi a tsakanin sojoji na iya haifar da bangaranci a tsakaninsu, wanda idan kuma aka bari abin ya ci gaba da samun gindin zama, akwai hatsarin gaske”.
Haka zalika, ya zargi Buhari da mataimakinsa Birgediya Janar Tunde Idiagbon da mayar da sojoji saniyar ware tare kuma da daukar tsauraran matakan kama-karya wajen tafiyar da mulki.
A cewar tasa, gwamnatin Buhari ta yi mulki ta hanyar tsoratarwa, maimakon sanya kyawawan fata a zukatan al’umma.
“Kyautuwa ya yi mu inganta rayuwarsu, mu karfafa musu gwiwa, don ganin rayuwar tasu ta inganta. Maimakon haka, sai aka yi ta faman kafa musu dokokin kama-karya. Wannan dalili ne yasa, aka wayi gari gwamnatin da aka kafa da niyyar cimma muradun bai-daya na sojoji, ta koma ta wasu ‘yan tsirarun mutane masu taurin kai”, in ji Babangida.
Ya bayyana cewa, “Yawancin juyin mulkin soja, muna yi ne sakamakon yawan korafe-korafen al’umma, musamman Talakawan da suka shiga matsanancin halin rayuwa, sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da aka yi ta faman fuskanta na yau da kullum”.
“Haka zalika, batun komawa amfani da tsohuwar hanyar aiwatar da musayar kayayyaki a kasuwanci na kasa da kasa, na nufin cewa; kwata-kwata ba a kama hanyar kawo karshen matsalolin tattalin arzikin a tsakanin al’umma ba”, in ji IBB.
Har wa yau, sanin kowa ne cewa; dokokin kama-karya, sun tauye ‘yancin walwalar jama’a kai tsaye, sannan kuma ga hukunci mai tsauri, kamar yadda ya bayyana a littafin.
Kazalika, kayayyakin masarufi da sauran bukatun yau da kullum, sun yi matukar karanci, duk dai a wancan lokaci na mulki Buhari, in ji Babangida.
A bangare guda kuma, Janar Babangida a cikin littafin nasa, ya zargi marigayi tsohon shugaban kasa; Janar Sani Abacha da laifin yunkurin kifar da gwamnatinsa ta karfi da yaji da kuma zargin laifin soke zaben shugaban kasa na shekarar 1993.
Badamasi, ya amince da aikata babban kuskure a lokacin da yake shugabancin Najeriya, na gaza yi wa Sani Abacha ritaya daga aikin soja.
A lokacin, Abacha shi ne babban hasfan tsaro; wanda ya kwace mulki tsawon wata uku, bayan Babangida ya ajiye mukaminsa na shugabancin kasa.
Babangida ya kara da cewa, duk da shi da Abacha abokan juna ne, amma a fili yake cewa; Abacha mutum ne mai wuyar sha’ani, wanda ke biye wa munanan zantukan da ke faruwa a tsakanin rundunar sojin Nijeriya.
“Na yi mamakin yadda shi da wasu mutane suke da mummunar fahimta a kaina tare da nuna cewa, ni ne matsala,” in ji Babangida”.
A cikin littafin nasa ya ce, Abacha ne ya kitsa yadda za a cire shi daga shugaban kasa. Sai dai duk da haka, bai sallame shi daga aikin soja ba, saboda gudun zubar da jini a cikin rundunar sojin.
“A lokacin kan jami’an rundunar soji a rarrabe yake, don haka; duk wani yunkuri a lokacin, ka iya haifar da mummunar matsala,” in ji Babangida.
“Abin ya kai ga idan na yi wani kuskure daga bangarena, zai iya jawo zubar da jini, saboda za a samu yunkurin yin juyin mulki.”
Wannan tsokaci da IBB ya yi a littafin nasa, ya ja hankalin iyalan marigayi Sani Abacha, da ta kai har guda daga cikin ‘ya’yansa; Sadik Abacha ya mayar masa da martanin cewa, ‘yan Nijeriya ba za su taba mantawa da kokarin da mahaifinsu ya yi a bangaren ci gaban kasa ba, sannan kuma za su ci gaba da yaba masa kamar yadda suka saba.
“Mahaifina Abacha, kai ne a koda-yaushe suke yi maka hassada da bakin ciki. Saboda haka, tarihi zai ci gaba da tunawa da kai a matsayin shugaba nagari, ko su yabe ka; ko su yi suka, a matsayina na da, ina alfahari da kai, domin kuwa dukkaninsu suna fatan kai wa rabin matsayinka”, in ji Sadik.
Bugu da kari, makudan kudaden da aka tara a wajen kaddamar da littafin, ya yi matukar jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan Nijeriya, domin kuwa Naira na gugar Naira har biliyan 17.5 aka tara wa tsohon shugaban kasar; don gina dakin karatu.
Har ila yau, Alhaji Aliko Dangote, Abdussamad Rabi’u, Janar TY Danjuma, Arthur Eze da sauran makamantansu, su ne wadanda suka tara wadannan makudan kudade; a matsayin gudunmawa, domin gina wannan katafaren dakin karatu na Janar Babangida.
Wanda ya fi kowa tarin dukiya a dukkanin fadin Afirka, Aliko Dangote, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan biyu tare kuma da alkawarin ci gaba da bayar Naira biliyan biyu-biyu tsawon shekara uku, wanda idan aka hada jimillarsu zai kama Naira biliyan takwas.
Sai kuma Alhaji Abdussamad Rabi’u, wanda ya bayar da Naira biliyan biyar; duk da cewa, IBB ya bayyana cewa; tuni ya fara bayar da tasa gudunmawar wajen ginin wannan daki na karatu.
Akwai kuma, tsohon hafsan soji kuma ministan tsaro; TY Danjuma da ya yi alkawarin bayar da Naira biliyan uku. Sai wani shahararren Dan kasuwa mai suna Arthur Eze, shi ma ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 500.
Haka nan, akwai wasu da dama su ma da suka bayar da wannan gudunmawa da kuma wadanda suka yi alkawari; duk dai a wajen wannan kaddamar da katafaren littafi na Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kura Janar Babangida Naira biliyan yan Nijeriya ya bayar da
এছাড়াও পড়ুন:
An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a ƙasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta ɓarke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Kongo.
Ƙungiyoyin raya ƙasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo inda yaƙi ya ƙazanta a gabashin ƙasar.
Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban MajalisaShugabanin ƙasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi naɗin a wani yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin basasa a gabashin Kongo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.
Da yammacin jiya Litinin, suka fitar da sanarwar cewa sun naɗa tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a matsayin waɗanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu.
“An buƙaci dukkan ɓangarorin su mutunta tsagaita wutar da aka ayyana a taron EAC da SADC, kuma an yi kira ga M23 da kuma sauran ɓangarorin su dakatar da kutsawa cikin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo tare da mutunta tsagaita wuta,” in ji ƙungiyoyin a wata sanarwar da suka fitar.
Har yanzu ƙungiyoyin kasa da kasa da suka haɗa da Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongon wanda ya laƙume rayukan fararen hula da dama.
Yaƙi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar, kamar yadda Firaiministar ƙasar Judith Suminwa Tuluka ta shaida wa kwamitin kare haƙƙin ɗan’adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Litinin.