2025-04-01@17:04:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 77
«ya bayar da»:
Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi. Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis tare da ba da umarnin ƙaddamar da bincike a kai. Wata sanarwa da Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Edo, Fred Itua ya fitar, ta...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba. Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Armeniya Ararat Mirzoyan a Yerevan, Araghchi ya nanata cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye da Amurka ba a karkashin yanayin matsin lamba da barazanar soji, da kuma kakaba takunkumi. Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai...
Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu. Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su...
A jiya Asabar 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng, ya amsa gayyatar halartar taro na 2 na tattaunawar sassan Sin da na Amurka game da batun tattalin arziki karkashin cibiyar Jimmy Carter, inda ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. A cikin jawabinsa, jakada Xie Feng ya ce ko kadan, hadin gwiwar Sin da Amurka bai taba zama na wani fanni ya ci riba dayan ya yi asara ba. Maimakon haka, kaso 41 bisa dari na kamfanonin Amurka dake kasar Sin na daukar Sin a matsayin kasa ta biyu a duniya, wajen samun ribar hada hadar kasuwanci. Dole Gwamnatin Tarayyar Nijeriya Ta Daina Barazana Ga Masu Sukar Ta – Amnesty An Kashe Askarawa 6 da...
Kungiyar Taliban ta ce Amurka ta cire tallafin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanai kan Sirajuddin Haqqani, mataimakin shugaban kungiyar kuma ministan harkokin cikin gida. A cewar Abdul Mateen Qani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Taliban, an janye tukuicin da aka bayar a baya a karkashin shirin bayar da lada na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, tare da bayyana Haqqani a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo. Kawo yanzu dai babu wani martani daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka dangane da matakin. Haqqani shi ne shugaban kungiyar Haqqani, wata kungiya mai karfi a cikin kungiyar Taliban wacce ta shahara wajen ayyukanta da makamai. Duk da ayyana shi a baya a matsayin “dan ta’adda na...
Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa...
Ya sanar da cewa, yanzu a Hukumar ana kara samun nada mata kan madafun iko, inda ya sanar da cewa, a yanzu a Hukumar mace ce, ke rike da mukamin Babbar Darakta ta sashen kudi da mulki wato uwargida Bibian C. Richard-Edet. A cewarsa, a shekarun baya, akalla muna da mata sha biyu da suke rike da mukamain Janar Manaja da kuma mukamain Manajoji a Hukumar Shugaban ya bayyana cewa, mata na ci gaba da bayar da gudunmawar su wajen habaka fannonin da ke a Hukumar ciki har da bangaren tsaro, kiwon lafiya da sauransu. “Wadannan wasu misalai ne ‘yan kadan da Hukumar ke yi na inganta ‘yancin mata da tabbatar da ‘yancin su, duba da cewa, bamu iyakance irin...
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da ikon rushe zaɓaɓɓun shugabanni na jiha. Bugu da ƙari, Sambauna ya caccaki yadda Gwamnatin Tinubu ke nuna bambanci wajen raba wa matasa tallafi. Ya ce: “Seyi Tinubu ya bayar da kayan abinci a Arewa a matsayin tallafi, amma a Kudu yana bayar da tallafin kuɗi domin mutane su dogara da kansu wajen bunƙasa kasuwanci. Wannan nuna bambanci ne da...
’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar. Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya. A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan ne a wannan Lahadi, bayan da Washington ta zargi Tehran da taimakawa sojojin Yaman a hare-haren da suka rika kaiwa haramtacciyar kasar Isra’ila a baya-bayan nan tare da yin kira da ta daina yin wanann zargi maras tushe balantana makama. Salami ya ce, “Iran ba za ta taba zama mai fara yaki ba, amma idan aka fuskanci barazana, za ta mayar da martani mai tsanani.”...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin mayar da Filin Idi na Ƙofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa don Harkokin Addinin Musulunci. Sabuwar cibiyar za ta zama wajen gudanar da taruka da karatuttukan addini maimakon barin filin ana amfani da shi sau biyu a shekara don Sallar Idi. HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Akwai ’yan ƙwaya a cikin sarakunan gargajiya — Obasanjo Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron buɗa-baki da ya shirya a Fadar Gwamnatin jihar a ranar 15 ga watan Ramadan. Taron ya samu halartar Mambobin Majalisar Malamai, inda suka tattauna kan haɗin kai da kuma rawar da malamai ke takawa wajen wanzar...

Kungiyoyin Falasdinawa Suna Cigaba Da Yin Allawadai Da Hare-haren Amurka Da Birtaniya Akan Kasar Yemen
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
Kamitin Zakka na Masarautar Hadejia ya raba zakkar kayayyakin amfanin gona da na kudi kimanin naira miliyan 63 a gundumar Birniwa dake Jihar Jigawa. Sakataren kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Injiniya Isma’ila Barde, ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon zakka ga mabukata a gundumar Birniwa. Injiniya Isma’ila Barde ya lissafa abubuwan da aka bayar a matsayin zakka, da suka hada da buhunan Gero 668, da Bahunan Dawa 152 da bahunan shinkafa 8 da rabi da Kuɗi kimanin naira miliyan 17 da dubu ɗari tara da goma sha shida. A nasa jawabin, Shugaban kwamitin zakka na masarautar Hadejia, Barrista Abdulfatah Abdulwahab wanda babban limamin masarautar Hadejia Ustaz Malam Yusuf Abdurrahman ya wakilta, ya yaba wa al’ummar Birniwa bisa bayar da...
Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya. Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu. Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta...
Wani mutum wanda yake nuna kin amincewa da zaluncin da HKI yake yi wa mutanen Gaza, ya hau kan hausumiyar agogon “ Big-Bang” a birnin London dauke da tutar Falasdinu. An sami cunkuson motoci a yankin Westminster dake birnin London a jiya Asabar,yayin da masu ceto suke kokarin isa ga mutumin domin sauko da shi daga kan hausmiyar agogon. Jami’an ‘yan sandan sun sanar da samin rahoton abinda ya faru da misalin karfe 7 na safe,kuma sun fara aiki domin ganin an sauko da mutumin cikin lafiya. Jami’an tsaro sun sanar da cewa an rufe hanyar da take zuwa majalisar saboda abinda ya faru. Haka nan kuma gadar da take zuwa Wesminster da sauran hanyoyin da suke yankin duk an...
A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a. Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin. A shekarar...
SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1 BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 1 Sharhi: Shehun malami Ibnu Juzai (Allah ya yi masa rahama) yana bayani a nan game da ma’anar Tafsiri, wanda ke nufin fassara da ƙarin bayani kan ma’anonin ayoyin Alƙur’ani. A bisa wannan magana, ana iya fahimtar cewa: 1. Tafsiri yana nufin bayani da sharhi na Alƙur’ani – Wato fassara da bayanin ma’anar ayoyi domin su fi zama a fili ga masu karatu da sauraro, don su fahimci saƙon da ke cikinsu. 2. Tafsiri yana bayyana ma’anar ayoyi dalla-dalla – Manufarsa ita ce kawar da ruɗani da kuma hana kuskuren fahimta. 3. Hanyoyin bayani a tafsiri suna da matakai daban-daban: Ta lafazin ayar kai tsaye (بِنَصِّهِ) – Wato bayani...

‘Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Kananan Hukumomi 749 Sun Gaza Bayar Da Cikakkun Bayanan Asusunsu
A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.” Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba. Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas. “Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don...
Kididdigar da hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, zuwa karshen watan Fabarairun shekarar nan ta 2025, yawan musayar kudaden da aka adana na Sin, ya kai dalar Amurka tiriliyan 3.2272, adadin da ya karu da dalar Amurka biliyan 18.2, sama da na karshen watan Janairu, wato karuwar kaso 0.57 cikin dari. Wani jami’i mai aiki a hukumar kula da musayar kudaden kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da tushe mai inganci, da fa’ida mai yawa, da juriya mai karfi, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton ma’aunin musayar kudaden da aka adana. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...

Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar da amsa a nazarin, ya ragu. A cewar nazarin, kaso 62.9 na masu bayar da amsa sun yi Allah wadai da manufar sanya muradun Amurka gaba da komai, inda suka soki manufar suna cewa, ta yi watsi da hakkoki da muradun sauran kasashe. Adadin wadanda suka bayar da wannan amsa daga nahiyar Turai ya kai kaso 67.7. Baya ga haka, kaso 55.1 na masu bayar...
Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da suka shafi fursunonin, Adam Boehler, da shugabannin Hamas, a yunkurin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza. Trump ya ambaci haka ne bayan ganawa da fursunoni shida da aka sako a wani bangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Wani babban kusa na kungiyar Hamas ya shaidawa Al Mayadeen cewa, taron na baya-bayan nan ya bar wa bangaren Amurka...
Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya. An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati. Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon...
’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda. Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari. Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur...
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar. Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma. Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.
Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring rolls’ Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno Haka kuma an ce, jihohin da ba sa noma suna jin tasirin rage farashin kayan abinci. Masana sun danganta faduwar farashin da aka samu a kasuwa ga karancin kudi da kuma yadda aka yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, wanda hakan ya haifar da faduwa farashin sosai. Wasu kuma sun ce, yawan shigo da...
Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru. Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako. Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa,...
Fira ministan hakar Habasha Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa. Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan ta yankin Somaliland. Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu take daukar cewa ba kasa...
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki. Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin. An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban. Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed. Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa. Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya....
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ake tuhuma da almundahana. A ranar Alhamis, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin sakin Farfesa Usman daga gidan gyaran hali na Kuje bayan an cika sharuɗan belinsa. Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe. Ana zargin ya amince wajen sayen motoci a kan Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016. EFCC, ta kuma ce Farfesa Usman ya bai...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta. Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga. Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da...
Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) bisa irin gudunmawar da ya bayar ga ci gaban Najeriya. Shugaban kasar a bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da tallafin, tarihin rayuwar Janar Babangida da gwagwarmayarsa yayin aiki, wanda aka gudanar a Abuja. A yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman, Tinubu ya bayyana ga irin jagoranci Babangida a yayin mulkinsa, wanda ya ce ya abin koyi ne ga kowa. Ya kuma yaba da rawar da IBB ya taka wajen kafa sabbin bankuna na zamani, wanda ya kawo kyakkyawa sauyi a fannin hada-hadar kudi na Najeriya. Tinubu ya kuma yabawa manufofin Babangida da salon shugabancinsa da suka...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta. Yin hakan ya na nuna yanda al-amarin musayar Fursinoni yake da muhimmancin ga falasdinawa. Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran ...
Sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare a yankin Tul-Karam da sansanonin ‘yan gudun hijira da suke cikinta wanda ya dauki kwanaki 21 suna yi. Bugu da kari, sojojin mamayar suna cigaba da kama Falasdinawa a wannan yankin,inda a daren jiya su ka kutsa cikin unguwanni mabanbanta. Har ila yau, sojojin mamayar sun kwace gidajen Falasdinawa da dama da suke a kusa da sansanin Tul-kram, da mayar da su zama sansanonin soja. Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawan da ‘yan sahayoniyar su ka tilastawa yin hijira daga sansanonin Tul-Karam da Nuru-Sahmsh, sun kai 10,000. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa ta sanar da cewa, adadin mutanen da su ka yi shahada a cikin kwanaki 21 na hare-hare sun kai 11, yayin...
Salma Muhammad Salisu matashiya ce da ba ta taba mafarkin yin sana’ar kayan makulashe ba, bayan da ta kammala digirinta na farko a fannin Kididdiga (Statistics). Shekara biyar da kammala jami’a, matashiyar ta tsinci kanta cikin matsalar rashin aikin ofis, duk kuwa da karancin kwararru mata a fannin da ta karanta. Hakan ya sa ta fara tunanin yadda za ta fara sana’a domin dogara da kanta kafin Allah Ya kawo mata aiki. Daga nan ne tunanin fara kasuwancin harkar girke-girke da hada lemo ya zo mata, har ta fara ‘M&S Mannah Wassalwa Kitchen’. Labarin Salma na kama da matasan Nijeriya da dama da suka kammala manyan makarantu, amma ba su samu aikin ofis ba. Hakan ne ya sanya a baya-bayan...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)
Sama Da Masu Amfani Da Kayayyakin Laturoni Miliyan 20 Ne Suka Nemi Tallafin Musayar Kayan Laturoni
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaben 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen manyan ‘yan siyasa da ke hamayya da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda suke tarurruka tare da tuntuɓar juna kan yadda za su kayar da Jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani kan kalaman da wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyun adawa da na cikin gidanta suke yi, inda suka zarge ta da sauka daga kan turbar da jam’iyyar take. Katsina ta zama cibiyar haɗin kan ƙabilun ƙasa a Arewa — Gwamna Radda Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Fadar Shugaban kasa na mayar da martani ne bayan wani taro da jagororin hamayya...
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan. Yayin ganawarsa da tawagar kwamandojin sojojin sama da na sararin samaniya na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Idan Amurkawa suka yi barazana wa Iran, to lallai za su fuskanci mayar da martani, idan kuma suka aiwatar da wannan barazanar, to za su fuskanci mayar da martani Iran mai gauni, kamar yadda idan suka kawo hari kan kasar Iran, za...
“Kowannen masu hada-hadar musayar kudade da aka san da zamansu da suka biya kudinsu na sake sabunta lasisinsu na 2025, an shawarce su da su rubuta zuwa ga Daraktan sashen kudi da tsare da sanya ido na Bankin, domin su karbi kudansu, da aka dakatar da biyan kudi, zuwa cikin asusunsu.” Inji Takardar Takardar ta bayar da tabbacin cewa, Bankin na CBN, har yanzu a tsaye yake akan kafarsawajen ganin ya samar da daidaito da bin ka’ida, musamman wajen gann ana gudanar da hada-hadar musayar kudade na waje a kasuwar musayar kudi.
“Wannan sauye-sauyen an yi su ne, bisa manufar bin ka’idar shigar cikin Tashar, musamman domin a dakile satar hanyar shiga cikin Tashar ga manyan motocin da ba su gabatar da takardun shedar ka’idar shiga cikin Tashar ba.” Acewar Sanarwar. Kazalika, Hukumar ta NPA, ta bayar da umranin da a gaggauta wanzr da sauyin, biyo bayan sauya wadannan sabbin matakan da Hukumar ta yi, wanda za su fara aiki a cikin watan Fabirairun 2025. “Bisa wannan sauyin, daga yanzu daukacin manyan motocin da suka tunkaro domin shiga cikin Tashar, dole su kasance suna sanye da lambar manyan motocin, domin bin ka’idojin da Hukumar ta gindaya.” Inji Sanawar. “Dole ne manyan motocin su manna kwafin takardun shedar bayar bayar da kariya wato...
Kasashen larabawa masu kawance da Amurka sun kasance a sahun gaba wajen mayarwa da shugaban kasar Amurkan martani, bayan da ya bayyana cewa kasarsa za ta shimfida ikonta a Gaza, bayan fitar da Falasdinawa da Gaza. Gabanin wannan sanarwar ta Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa ya tuntubi kasashen Jordan da Masar masu makwabtaka da Falasdinu da su karbi bakuncin mutanen Gaza na wani lokaci har zuwa sa’adda za a gyara wajen. Masar da Jordan sun yi watsi da wannan shirin da suke dauka a matsayin wata dabara ce ta fitar da Falasdinawa daga cikin kasarsu, da maye gurbinsu da yahudawa ‘yan share wuri zauna. A wani bayani da kungiyar hadin kan Larabawa ta fitar ta bayyana cewa; Abinda Trump...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump zai rattaba hannu kan wasu takardun bayar da umarni na bangaren zartaswa, game da janyewar Amurka daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin duniya (UNHRC) da kuma dakatar da bayar da tallafi ga hukumar bayar da agaji ga Falasdinu ta majalisar dinkin duniya (UNRWA). Wata kafar yada labarai ta cikin gida a Amurka ta bayar da rahoton haka, daga wata majiya ta hukuma a fadar White House. Yau talata kuma Trump na ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya dade yana sukar hukumar ta bayar da agaji ga Falasdinu ta UNRWA. A lokacin wa’adin farko na mulkin Trump a watan Yunin 2018, Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisar dinkin...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024. Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma...
“Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai ta Naira tiriliyan 5.81 wacce ta yi daidai da dala biliyan 3.7, a zango na uku hudu a 2024.” Kamar yadda rukunonin taron bunkasa tattalin arziki na Nijeriya NESGya ruwaito. Rahoton ya sanar da cewa, an samu wannan nasarar ce, biyo bayan amfanin da Tashoshin Hukumar Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Sowore, wanda ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 17 daga rundunar ‘yansanda, ciki har da laifi a kafafen sada zumunta da kuma kiran Shugaban ‘Yansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, da “IGP na ƙarya.”
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...
Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu. Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba. Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30. Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya...
Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...

Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...