Kwara ta Raba Littafai Fiye da Dubu 74 Kyauta Ga Dalibai
Published: 28th, February 2025 GMT
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu.
Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar.
A cewarsa ra’ayin gwamnati ne cewa zuba jari zai mayar da matsalar yaran da ba su zuwa makaranta ya zama tarihi a jihar.
Gwamna AbdulRazaq ya bayyana cewa rabon litattafan kyauta shine don a rage musu nauyi a kan iyaye saboda tsadar kayan koyarwa a kasuwanni.
Ya ce gwamnatin ta kuma fara daukar malamai aiki akai-akai tare da kara musu girma idan sun cancanta, da kuma inganta abubuwan more rayuwa a makarantu da sauran hanyoyin da za a bi wajen kawo sauyi a fannin.
Gwamnan ya yabawa jami’an hukumar ta UBEC da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suke ba da goyon baya da jajircewa wajen gudanar da aikin.
A nasa bangaren shugaban kwamitin majalisar dokokin jihar Kwara kan harkokin ilimi, Muhammed Boriya, ya bayyana taron a matsayin wani lokaci mai cike da tarihi na ci gaban ilimi na farko a jihar.
Ya ci gaba da cewa a yanzu jihar ta fice daga munanan abubuwan da suka faru a baya, inda ya ce an cike gibi da dama a bangarori da dama.
A nasa jawabin shugaban hukumar SUBEB ta jihar Kwara, Farfesa Shehu Adaramaja, ya ce raba kayan wasanni za su samar da ingantaccen ilimi da kuma bunkasa ci gaba ga yaran makaranta.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kayan Karatu Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Fursunoni 62 Sun Rubuta Jarrabawar NECO da MBAIS A Kano
A ƙarshe, wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron, Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar Faruk, ya nuna jin daɗinsa da ci gaban da aka samu wajen gyaran ɗaliban ta hanyar ilimi na yau da kullum, yana tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen ilimi na ‘yan gidajen yari a matsayin muhimmin mataki na dawo da su cikin al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp