2025-03-31@05:37:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 147

«Kayan Karatu»:

    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a...
    Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman...
    Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya  ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry. Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya...
    Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya...
    Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na...
    Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa...
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma...
    Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun  tattauna batutuwa da dama domin  karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne  a Abuja  bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da  halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban...
    Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga  Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci  na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a...
    Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya ce kawo yanzu bai da ta cewa kan ko zai tsaya takarar shugabancin ƙasar a Zaben 2027. Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira ta bidiyo a cikin shirin nan na Untold Stories tare da ɗan jarida Adesuwa Giwa Osagie wadda za a haska a yau Laraba....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan al’amura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shi ne na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. NAJERIYA A...
    Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da...
    Kungiyar gwagwarmayar falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da sulhun da aka cimma wajen tattara bayanai kan shugabannin kungiyar ta bi tana kashe su. Saidai mai magana da yawun kungiyar ya ce kungiyar tana da tushe sosai a Falasdinu wanda kisan gillar da Isra’ila ke yi wa shugabanninta ba, bai zai...
    Dakarun sojin Yaman sun ce sun kara kai hare-hare na nuna kyama ga Isra’ila da Amurka a matsayin nuna goyan baya a kan zirin Gaza. Kakakin rundunar Yahya Saree ya ce a daren jiya litinin sojojin na Yaman sun kai hari filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion na Isra’ila da makami mai...
    A wata hira da tashar talabijin din, manzon musamman na Amurka a yankin gabas ta tsakiya Steve Witkoff ya rubuta a shafinsa na; X cewa; Sakon da Trump ya aike wa  Tehran ba ta nufin yin barazana. Manzon na Amurka ya riya cewa;wasikar ta kunshi cewa; Ni shugaban kasa ne mai son zaman lafiya ,...
    Kazalika, a wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Fabrairun 2025 ya tsaya da kashi 1.67 cikin dari, idan aka kwatanta da watan Janairun 2025, an samu raguwar matsakaicin farashin kayan abinci kamar su dawa, dankali, wake, masara da garin masara da rogo. Hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Nijeriya dai ya yi tashin gwauron zabi ne...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin...
    ’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya buƙaci al’ummar jihar da su zauna lafiya sannan su kasance masu kiyaye doka da oda. Fubara ya yi kiran ne safiyar wannan Larabar bayan da yammacin Talatar jiya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi da mataimakiyarsa da duk ’yan majalisar dokoki sannan ya ayyana dokar ta ɓaci a...
    Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar. Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya. Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da...
    Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da tsohon shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum, Nijar na ci gaba da janye jikinta daga ƙungiyoyin yammacin duniya. A baya-bayan nan ma, tare da Mali da Burkin Faso, ƙasar ta fice daga ƙungiyar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya yi gargadin cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba neman wata kasa da yaki ba, amma kuma  a lokaci guda ta shirya tsaf domin mayar da mummunan martani ga duk wata barazana ko shishigi daga makiya. Janar Hossein Salami ya bayyana hakan...
    Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen...
    Hajiya Asta Shehu Timta, mahaifiyar mai martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Muhammadu Shehu Idrisa Timta ta riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da Masarautar Gwoza da ke Jihar Borno ta fitar ta ce Hajiya Asta ta rasu ne yammacin jiya Asabar bayan shafe shekaru 80 a duniya. Yadda za a girka ‘Kamoniya’ An kama malama tana...
    An kama wata malamar makarantar sakandare ta California a Amurka da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17. Wannan da ba shi ne karon farko ba da aka tuhumi wani da irin wannan hali ba a makaranatar. Yadda ango da ’yar uwar amarya suka rasu minti 30 kafin ɗaurin aure a Bauchi...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye...
    A ranar Litinin, Ratcliffe ya shaida wa BBC cewa wasu daga cikin ‘yan wasan Manchester United ba su da ƙwarewa, amma ana biyansu albashi mai yawa fiye da yadda ya dace. Ya kuma bayyana shirin gina sabon filin wasa mai tsadar Yuro biliyan 2, wanda zai iya ɗaukar mutum 100,000 idan aka kammala. A ‘yan...
    Shi ma, Manajan Darakta na CDI, Roland Oroh, ya goyi bayan wannan ra’ayi na Dakta Anyebe Idoga, inda ya sanar da cewa; wannan aiki, zai kara karfafa karfin Nijeriya wajen fitar da kaya zuwa ketare. “Mun ji dadi kan fara wannan yarjejeniya da mu, domin wannan zuba hannun jari, zai taimaka wa Nijeriya wajen kara...
    Rashford, mai shekaru 27, ya buga wa Ingila wasanni 60 tare da cin ƙwallaye takwas. Amma bai samu dama a hannun tsohon koci Gareth Southgate ba, inda aka cire shi daga gasar Euro 2024 da kuma Nations League ta 2024-25. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a...
      Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi.   Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen...
    Tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce idan buƙatar tsige Gwamna Siminalayi Fubara ta zama tilas za a iya yi. Wike ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, inda ya jaddada cewa siyasa ba wasa ba ce, kuma ya kamata a bi ƙa’ida wajen...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna...
    Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da  sauran dangoginsa da sun kai  ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin...
    Aƙalla mutane 26 ne suka riga mu gida sakamakon ɓarkewar cutar Sanƙarau a wasu ƙananan hukumomi huɗu na Jihar Kebbi. Da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi, babban birnin jihar, Kwamishinan Lafiya, Yanusa Ismail, ya bayyana cewa an samu adadin mutane 248 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikin samfura...
    UNRWA ta yi kira ga Isra’ila da ta kawo karshen hana shigar da kayan agaji a zirin Gaza domin dakile bazuwar yunwa da wahala a yankin. “Mun riga mun ga alamun farko na karin farashi a kasuwa,” in ji Kwamishinan UNRWA Philippe Lazzarini yayin taron manema labarai a wannan Litinin, ya kara da cewa yayin...
    Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa...
    Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000...
    Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan  samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Korar sojoijin Faransa daga kasa ta 7 a yammacin Afirka tare bukatar’ macron ya nemi uzurin kasashen’ wanda ni tahir amin zamn karanta. ///…Madalla, Bayan da kasashen Mali da Burkina faso, da Nigerda Ivory Coast suke kori sojojin Faransa daga kasashensu, a yanzun...
    Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka...