An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja
Published: 29th, March 2025 GMT
Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu.
An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin NijeriyaRundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ce ’yan shi’a sun kai wa jami’an tsaro hari da bindigogi, duwatsu, da wasu makamai.
A sakamakon haka, aka tura ƙarin dakaru domin kwantar da tarzomar.
“Kwamishinan ’yan sanda, CP Ajao Saka Adewale, ya yi tir da wannan hari da aka kai wa jami’an tsaro,” in ji kakakin rundunar, Josephine Adeh.
“Ana ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.”
Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda rikicin ya ɓarke.
“Ina wucewa kawai sai naga taron jama’a suna jifan jami’an tsaro. Ba zato ba tsammani, sai aka fara jin harbin bindiga, mutane suka fara gudu,” in ji shi.
Jami’an tsaro sun tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin, sannan sun buƙaci jama’a su zauna lafiya tare da bayar da rahoton duk wank abun zargi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan Shi a Arangama Jami an Tsaro jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya : An samu hargitsi a yayin jerin gwanon ranar Kudus a Abuja
Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya.
Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su.
An ce an kai gawarwakin mutanen goma sha hudu zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Ana gudanar da tattakin ranar Qudus ta duniya duk shekara a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.