2025-03-31@17:56:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 32
«Arangama»:
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba....

Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Zargin Kasar Amurkan Dangane Da Kamfanonin Man Fetur Na Kasar Ba Gaskiya Bane
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba. A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da su kawo karshen rikicin da Isra’ila ke ci gaba da haifarwa a yankin gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, Araghchi ya yi Allah wadai da sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa...
Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi kakkausar suka kan zaluncin da gwamnatin Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu da ba su da kariya a yankin Zirin Gaza, yana mai jaddada bukatar hadin kai da daukar matakin gaggawa na kasashen musulmi domin dakile wadannan laifuka. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace. Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB)...
Iran ta ce za ta fifita diflomatisyya ta tsakaninta da kasashe makobtanta na yankin. Ministan harkokin wajen kasar ne Abbas Araghchi ya jaddada aniyar kasar kan harkokin diflomasiyya a yankin, yana mai bayyana cewa kasashen da ke makwabtaka da kasar na cikin tsarin Jamhuriyar Musulunci. “Makwabtanmu sune fifikonmu,” in ji ministan harkokin wajen Iran a...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in...
Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma aiki tare.”...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa. “Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya soki matakin da sabuwar gwamnatin Amurka ta dauka na janye sassaucin da ta yi wa Iraki na shigo da wutar lantarki daga Iran. Araghchi ya bayyana matakin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin “abin takaici.” Ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta na kokarin hana al’ummar iraki...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo....
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira. A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za...
Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa. “A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane...
Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba. Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa,...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe...
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya...
Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da...
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa duk wata matsin lamba kan kasar ta Donald Trump za ta cutura. Iran dai ta caccaki matakin da shugaban AMurka ya dauka ind aya sanya hannu kan umurnin sanya sauraren matakn matsin lamba kan Tehran a game da shirinta na nukiliya. Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana a wani sako...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya. Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tsananta matsin lamba da ake son dauka kan Iran ba zai yi wani tasiri ba Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Manufar matsin lamba da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan Iran za ta sake yin kasa a gwiwa tare da rashin nasara....
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce; Iran Zata Kalubalanci Duk Wanda Ya Kai Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyarta
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Duk wani hari da aka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai fuskanci mayar da martani cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Harin da Amurka da yahudawan sahayoniyya suke kai wa kan cibiyoyin nukiliyan kasashe, nau’in hauka ne kuma zai jefa yankin cikin bala’i....

Aragchi Yace Duk Wani Harin Da Aka Kaiwa Cibiyoyin Nukliyar Kasar Iran Hakan Wata Musiba ce Ga Yankin Asiya Ta Yamma
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas...