Leadership News Hausa:
2025-03-31@02:00:51 GMT

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Published: 28th, February 2025 GMT

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Kasar Sin ce ke da kusan kashi 30 cikin 100 na karuwar tattalin arzikin duniya a bara, wanda ya yi tasiri matuka ga tattalin arzikin duniya. Gudunmawar da kasar Sin ta bayar ta sake tabbatar da matsayinta na kan gaba a fannin tattalin arziki, kuma ta nuna muhimmiyar rawar da take takawa wajen ciyar da harkokin cinikayyar kasa da kasa gaba, da karfafa zuba jari da ingiza kirkire-kirkire na fasaha.

Hakazalika, darajar cinikin waje na kasar Sin ta kai wani matsayi mafi girma a shekarar 2024, inda jimilarta ta kai yuan triliyan 43.85, wanda ya karu da kashi 5 cikin dari bisa na shekara 2023. Haka ma yawan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje ya karu da kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2023 zuwa yuan tiriliyan 25.45 yayin da yawan kayayyaki da aka shigo da su ya karu da kashi 2.3 cikin dari zuwa yuan tiriliyan 18.39.

Hakazalika, Ci gaban kasar Sin yana haifar da tasiri a sassa da dama, ciki har da masana’antu, da fasaha da ayyuka. Tasirin ayyukanta da suka shafi tattalin arziki yana daidaita kasuwannin duniya, yana haifar da bukatun fitar da kayayyaki daga wasu kasashe, kuma yana taimakawa farfadowar tattalin arzikin yankunan da cutar ta COVID-19 ta fi shafa. Gudunmawar da kasar Sin ta bayar wajen samun ci gaban duniya a shekarar 2024 ta kara tabbatar da rawar da ta taka wajen farfadowa bayan barkewar annobar. Musamman ma, karuwar kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su daga kasashen waje, na taimakawa kasashe masu tasowa wajen habaka kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasashen waje, da gaggauta farfado da tattalin arzikinsu. Ta hanyar soke haraji kan kayayyakin da ke shigowa daga kasashe masu karancin ci gaba wadanda ke da huldar diflomasiyya da kasar Sin, kasar ta nuna aniyarta ta inganta ci gaban tattalin arzikin duniya, da zama amintacciyar abokiyar hulda a fannin tattalin arziki. Wannan manufar ba wai kawai tana karfafa huldar cinikayya da wadannan kasashe ba ne, har ma tana taimaka musu su shiga cikin kasuwannin duniya a dama da su, da samar da ci gaba mai dorewa da kuma taimakawa wajen rage talauci. Kasashe masu tasowa sun kasance babban jigon da ke ingiza fitar da kayayyaki daga kasar Sin zuwa kasashen waje, musamman kasashen da ke aikin samar da ababen more rayuwa karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Hasali ma, a shekarar 2024, kasashen da ke cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya sun kai sama da kashi 50 cikin 100 na jimillar cinikin waje na kasar Sin a karon farko. Wannan ya nuna yadda shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ke da girma wajen karfafa huldar cinikayya da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasar Sin da sauran kasashe masu tasowa, tare da karfafa rawar da kasar ke takawa a fannin cinikayya da raya ababen more rayuwa a duniya. Kasar Sin ta kara fadada kasuwannin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kasashe masu tasowa, tare da inganta cinikayya ta hanyar samun moriyar juna. Yayin da wadannan kasashe ke samun damar shiga kasuwannin kasar Sin mai matukar girma don samar da albarkatun kasa, jarin da kasar Sin ta zuba a fannin ababen more rayuwa karkashin tsarin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya na samar da muhimman damammakin ci gaba ga wadannan kasashe, da samar da ci gaban tattalin arziki da hada kai. Wannan hadin gwiwa ba wai kawai yana karfafa huldar kasuwanci ba, har ma yana sa kaimi ga ci gaba mai dorewa da hadin gwiwar tattalin arziki, tare da amfanar da kasar Sin da abokan huldar kasuwanci a kasashe masu tasowa.

Akwai Daidaito A Adadin Kayayyakin Da Sin Ke Fitarwa Zuwa Ketare

Yanzu yawan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka ya tsaya a kashi 15 cikin 100, inda ya ragu daga kashi 20 cikin 100 a shekarar 2018, lamarin da ke nuni da cewa, kasar Sin ba ta dogara ga Amurka kadai ba wajen yawan kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje ba. A sa’i daya kuma, kayayyakin kasar Sin ne kayayyaki mafi ingancin farashi kuma mafi yawa da Amurka ke shigowa da su, wanda ke amfanar mabukatada masana’antun Amurka. A hakikanin gaskiya, wannan yunkuri na samar da guraben ayyukan yi da dama a Amurka, yana nuna cudanya da moriyar juna na dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Girman cinikin ketare na kasar Sin ya nuna yadda ta ke kara mai da hankali kan fadada huldar da ke tsakaninta da kasashe masu tasowa da kuma kasashen da ke kawance da juna, ya kuma nuna cewa, kasar na rage dogaro ga kasuwannin yammacin duniya, musamman Amurka da Tarayyar Turai. Abu mafi mahimmanci shi ne ba za a iya dakile ci gaban kasar Sin a fannin fasaha ta hanyar shingen kasuwancin da ba shi da tushe balle marika ba. Kasar Sin za ta ci gaba da inganta kirkire-kirkire da karfafa matsayinta na kasancewa kan gaba a fannin cinikayya da fasaha a duniya, tare da karkata akalar kayayyakin da take fitarwa zuwa kasashen waje, ta hanyar mai da hankali kan kayayyakin fasahar zamani, da suka hada da motoci masu amfani da lantarki, da na’urorin dab’a na 3D, da na’urorin fasahar kere-kere, wadanda dukkansu ke samun ci gaba mai karfi, ta yadda za ta mayar da kasar daga masana’antar kera kayayyaki masu rahusa, zuwa kasa mafi girma a duniya a fannin fasaha da kirkire-kirkire. Haka ma sabbin nau’o’in cinikayya, irin su cinikayyar intanet tsakanin kasashe na kara habaka, wanda ya kara kaimi ga karfafa kasar Sin a kasuwannin duniya. Idan aka yi la’akari da ci gaban kariyar cinikayya, da takaddamar cinikayya ta hanyar kakaba haraji da kudin fito kan kayayyaki da kuma kalubalen yanayin siyasa, tabbas ana samun karin damuwa game da makomar dunkulewar duniya. Amma duk da haka matakan cinikayya maras shinge sun kasance ginshikan tattalin arzikin duniya mai fa’ida, saboda ciniki cikin ‘yanci yana habaka wadata, da samar da fa’ida ta zamantakewa da samar da karin ayyukan yi. La’akari da cewa, habaka masana’antu masu inganci da takara, da yin ciniki cikin ‘yanci suna baiwa kasashe damar samun bunkasa a duniya.

Ci gaba da kudurin kasar Sin na bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa a fannin cinikayya da tattalin arziki, ya nuna matsayinta na babbar kasa mai karfin tabbatar da zaman lafiya a duniya, kana mai goyon bayan samun bunkasuwa tare. Don haka, ya kamata Amurka da EU su mai da hankali kan samar da ingantacciyar takara da kasar Sin maimakon daukar matakan kariyar cinikayya don dakile ci gaban kasar Sin, saboda hakan zai kawo cikas ga kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arziki. Maimakon gina shingaye na kasuwanci da aiwatar da tsare-tsare masu hana ruwa gudu, kamata ya yi su zuba jari wajen gudanar da bincike da ci gaba, musamman a fannin fasahar kere-kere, don kara karfin takara a duniya. Hakazalika, ta hanyar ba da shawarar yin kasuwanci a bude, da kafa dabarun kasuwanci da hadin gwiwar zuba jari, da aiwatar da manufofin inganta sabbin abubuwa, Amurka da EU za su iya samar da damar tattalin arziki da za su amfanar da jama’arsu da kasuwancinsu. Bin tafarkin tsaftatacciyar takara, maimakon halin adawa, zai taimaka musu wajen habaka karfin tattalin arziki da samun jagoranci a duniya.

Bunkasar GDPn Manyan Biranen Sin Na Tasiri Ga Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin

Bunkasar tattalin arziki Sin na da nasaba da bunkasar GDPn manyan birane 27 wanda ya zarce yuan tiriliyan 1 a shekarar 2024. Jimillar kayayyakin cikin gida na biranen kasar Sin 27 ya zarce yuan tiriliyan 1 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 137.87 a shekarar 2024, kamar yadda jaridar People’s Daily a ketare ta bayyana a ranar Litinin 17 ga watan Fabrairun 2025. Alal misali, Shanghai, cibiyar hada-hadar kudi ta kasar Sin, da kuma birnin Beijing, babban birnin kasar, sun samu matsayi na daya da na biyu a kididdigar da aka yi, inda a shekarar 2024, adadin GDPnsu ya kai yuan tiriliyan 5.39 da yuan tiriliyan 4.98 bi da bi. Shenzhen, Chongqing da Guangzhou kowanne sun zarce yuan tiriliyan 3 a GDP, yayin da Suzhou, Chengdu, Hangzhou da Wuhan suka zarce yuan tiriliyan 2 a bara. Hakazalika, birane shida sun samu karuwar GDP sama da kashi 6 cikin dari, inda Quanzhou ke kan gaba da kashi 6.5 cikin dari. Wadannan birane gaba daya suna da ingantaccen tsarin masana’antu da manyan masana’antu. Masana’antu a wadannan biranen sun hada da masana’antar kere-kera da samarwa, da masana’antar ba da hidimomi na zamani da sabbin fasahohin kimiyya da fasaha, wadanda ke samar da tsarin kasuwanci iri-iri. Wadannan biranen suna mai da hankali kan habakar tattalin arzikin da ke haifar da kima, suna alfahari da karfin bincike na kimiyya, wanda ke ba da damar ci gaba da habaka masana’antu da sauyi. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tattalin Arziƙi fitarwa zuwa kasashen waje ci gaban tattalin arziki tattalin arzikin duniya a kasashe masu tasowa zarce yuan tiriliyan a shekarar 2024 ke fitarwa zuwa kayayyakin da da kasar Sin a kasuwannin Kasar Sin ta kasar Sin ta cinikayya da kayayyaki da da samar da

এছাড়াও পড়ুন:

Sharhi: Taruka Da Gangamin Ranar Quds Ta Duniya 2025

A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma.

An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi da na larabawa, har da wasu da wasu daga cikin kasashn ymmacin duniya da kuma na Afirka, ta hanyar shirya gagarumin gangamin da ke jaddada aniyarsu ta tabbatar da al’ummar Palastinu ta samu hakkokinta da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta musu, tare da nuna cikakken goyon baya ga gwagwarmayarsu ta neman samun wadannan hakkoki nasu.

A safiyar Juma’ar ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta tarukan sun yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a.

A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na tarukan ranar Kudus da aka saba gudanarwa shekara-shekara.

A birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran haka lamarin ya kasance, inda tun da jijjfin safiya dubun dubatar jama’a suka fara fita domin isa wurare da aka kebance domin taruwa, kamar yadda aka saba a kowace ana taruwa ne babban titin Inqilab, wanda titi ne da ya kai tsawon fiye da kilo mita goma a tsakiyar birnin Tehran, inda jama’a suka cika wannan titi makil a lokacin gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta dunya.

A jajibirin ranar ta Quds Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Sayyed Ali Khamenei ya bayyana cewa, tattakin ranar Kudus ta duniya na wannan shekara da yardar Allah zai kasance mafi girma a kan na sauran shekaru da suka gabata.

A cikin wani sakon da ya aike ta gidan talabijin a daren Alhamis, jagoran ya bayyana cewa, wannan rana a ko da yaushe wata alama ce ta hadin kai da karfin al’umma, yana mai bayyana yadda tattakin ke nuni da cewa al’umma na tare da gwagwarmaya a kan muhimman manufofinta na siyasa, da kuma tsayawa tsayin daka wajen kare hakkokin al’ummar Falastinu.

A kasar Iran dukkanin bangarori na al’umma suna halartar gangamin ranar Quds ta duniya, da hakan ya hada da mabiya addinai daban-daban, da sauran bangarori na al’umma da jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa da ma’aikata da ‘yan siyasa da kuma malamai, inda suke haduwa a kan kalma guda guda da manufa guda daya, ita ce nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu, da kuma yin tir da Allawadai da zaluncin Isra’ila a kans, da kuma yin kira da babbar murya a kan wajabcin kare hakkokin wannan al’umma da ake zalunta tsawon shekaru aru-aru.

A sauran bangarori na duniya kuwa, an gudanar da irin wannan gangami da jerin gwano a kasashe daban-daban, yankin Jammu da Kashmir na kasar Indiya, an samu halartar dimbin jama’a da ke daga tutocin Falasdinawa da kuma hotunan masallacin al-aqsa, yayin da suke rera taken ‘Yanci ga Falasdinu.

A kasar Bahrain musamman a yankin Bilad al-Qadeem, mahalarta taron sun daga hotunan Sheikh Isa Qassim, Sheikh Ali Salman, da shahidi Sayyed Hassan Nasrallah, a matsayi alama ta gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila da kuma nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.

A kasar Yemen, kwamitin al-Aqsa, ya kebance dandalin Sabeen da ke babban birnin kasar Sanaa, tare da wurare sama da 400 a fadin larduna 14, a matsayin wuraren da aka gudanar da gagarumin gangami na ranar  Qudus.

Musulmi da kuma masu fafutukar ‘yanci da kare hakkokin bil adama a duniya suna gudanar da ranar Qudus ta duniya kowace shekara a ranar Juma’ar karshe ta Ramadan, inda suke shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu.

A wasu ƙasashe, ƙungiyoyin zamantakewa daban-daban-ciki har da masana da masu fasaha, suna aiki kafada da kafada don wayar da kan jama’a game da buƙatar tabbatarwa da kiyaye haƙƙin Falasɗinawa ta hanyar gudanar da taruka na kara wa juna sani da laccoci, baje kolin zane-zane, da tattara gudummawa da kayan agaji.

Baya ga sassa na kasashen gabas ta tsakiya da Asia, an gudanar da irin wannan taruka da gangami a wasu kasashen yammacin turai da Amurka da kuma Latin Amurka, da kuma wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, da suka hada da Najeriya, Tanzania, Ghana, Senegal, Mali, Kenya, Afrka ta kudu da sauransu.

Ana gudanar da ranar Qudus ta duniya ne a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan bisa kiran da Imam Khumaini ya yi, wanda shi ne ya jagoranci juyin juya halin Musulunci, sannan kuma yunkuri nasa na ayyana ranar Qudus ta duniya, yana a matsayin wani mataki na kare hakkokin al’ummar Palastinu da ‘yancinsu, bayan shafe tsawon shekaru suna cikin wahala da kangi da hijira da mamaye yankunansu, da kuma tuna da duniya irin wannan mawuyacin halin da Isra’ila tare da taimakon kasashen yammacin duniya suka jefa Falastinawa a ciki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba Za A Iya Dakile Ci Gaban Hakkin Dan Adam Na Xizang Da Kowace Irin Karya Ba
  •  Kasashen Iran Da Tunisya Suna Shirin Bunkasa Alaka A Fagagen Yawon Bude Ido
  • An Gudanar Da Gagarumar Zanga- Zanga Ta Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Roma Na Kasar Italiya
  • Sin Da Laberiya Sun Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Ta Fuskar Tattalin Arziki Da Fasaha 
  • Wani Jami’in Leken Asirin HKI Ya Bukaci Kasashen Afirka Su Taimaka Su Karmi Falasdinawan Da Za;a Kora Daga Gaza
  • Kwamandan IRGC Ya Gargadi Amurka Dangane Da Hari Kan Kasar A Ranar Qudus Ta Duniya
  • Sharhi: Taruka Da Gangamin Ranar Quds Ta Duniya 2025
  • Taron Boao Ya Sake Ba Duniya Damar Ganin Abubuwa Masu Jan Hankali Game Da Sin
  • Xi Jinping Ya Gana Da Wakilan Masana’antu Da Cinikayya Na Kasa Da Kasa
  • Jerin Gwanon Ranar Kudus Na Ci Gaba Da Gudana A Kasashen Duniya