2025-02-28@17:11:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«fitarwa zuwa kasashen waje»:

    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.   Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.   Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa.   Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci.   Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da...
    Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami  ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu  kara  yawan wutar lantarkin da muke samarwa da  megawati 2000 a kowace sa’a daya  daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5. Zangon dai zai kare ne a cikn watan Maris 2029. Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.
    Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping. Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai...
    Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin yin sabon zaɓen ƙananan hukumomi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin IBB – Peter Obi An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, Ministan ya ce kotu ta dawo da zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin da aka zaɓa a ƙarƙashin tsohon Gwamna Gboyega Oyetola, amma ta tsige su ta hanyar umarnin zartarwa da gwamnan...
    Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
    Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar. Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba. Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran. Asghar Jahangir ya bayyana cewa...
    Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar. Ya kuma kara da cewa, zasu kai harin don haka HKI da Amurka kawo mata yaki. Yace wadan nan kasashe suna neman yaki da JMI, amma mafi yawan shirin nasu na farfaganda ne. Amma dolene mu shiga yaki don mu hana yaki faruwa. Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran suna yaki ne don ladabtar da HKI don ta gane cewa JMI ba mai sauki....
    Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    A rana Juma’a da ta gabata, aka kaddamar da gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya karo na 9, a birnin Harbin na lardin Heilongjiang na kasar Sin. Wannan gasa ta kasance babbar gasar wasannin kankara ta kasa da kasa karo na 2 da Sin ta karbi bakuncinta, biyo bayan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da ta gudana a birnin Beijing na Sin, a shekarar 2022. An ce, gasar wasannin kankara ta wannan karo ta samu halartar ‘yan wasa fiye da 1270 da suka zo daga kasashe da yankuna 34 dake nahiyar Asiya, alkaluman da suka kai matsayin koli a tarihi. Inda har wasu kasashen da ba sa samun yanayi mai sanyi da muhalli mai kankara a cikin gida, kamarsu...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
    Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.   Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.   Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.   Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
۱