Kwararrun Masana Sun Gargadi Kan Karkatar da Kudaden Fansho Na Biliyan ₦ 758
Published: 1st, March 2025 GMT
An shawarci gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai kan yadda za a biya ariyas na kudaden fansho da suka kai biliyan ₦758.
Wani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango ne ya bayar da wannan shawarar a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa PENCOM ta yi alkawarin kammala biyan kudin cikin watanni uku.
Farfesa Yushau Ango ya bayyana cewa, takardun lamuni yawanci kayan aikin kudi ne na dogon lokaci da ake samu daga masu saka hannun jari don warware basussukan da ake bin gwamnati, wanda yakan dauki lokacin da aka kayyade.
Ya nuna damuwarsa kan cewa bai kamata a rika rike irin wadannan kudade a bankunan kasuwanci da masu kula da fansho suka yi ba saboda wata manufa ta daban, yana mai jaddada cewa ba za a amince da duk wani mataki da aka dauka ba.
Masanin harkokin kudi ya kuma jaddada bukatar hukumomin da abin ya shafa su bi umarnin shugaban kasa tare da tabbatar da biyan basussukan fansho ba tare da bata lokaci ba.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada wajibcin tunkarar muggan manufofin yahudawan sahayoniyya na tilastawa al’ummar Gaza da yammacin kogin Jordan yin hijira daga muhallinsu, yana mai bayyana halin ko in kula da kasashen duniya suke nun awa kan wadannan laifuka a matsayin abin mamaki da damuwa.
Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Masar bayani kan ci gaban tattaunawar Iran da Amurka kan Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da ake takaddama a kai tsawon shekaru.