Aminiya:
2025-04-02@07:14:53 GMT

Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da ‘yanci daga wuta

Published: 1st, March 2025 GMT

Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa.

Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka.

Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan:

1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu.

Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka.

2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata.

3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya.

4. Yin Umara a watan Ramadan yana daidai da yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW).

5. Watan Ramadan wata ne na Alƙur’ani, saboda a cikinsa aka saukar da shi. Don haka, ya dace a yawaita karanta shi.

6. Watan Ramadan wata ne na kyauta, ciyarwa da sadaka. Manzon Allah (SAW) ya fi yawan kyauta a wannan wata.

7. Baccin mai azumi ibada ne, domin yana rage sha’awa da kula da zuciya.

8. Mai azumi yana da farin ciki biyu:

Yayin da zai buɗe baki bayan azumi. Lokacin da zai haɗu da Allah (S.W.A.) ranar alƙiyama.

9. Azumi garkuwa ne daga wutar Jahannama. Yana kare mutum daga sharrin sha’awa da zunubi.

10. A Ramadan, Allah Yana ’yantar da bayinsa daga wuta. Duk wani dare, Allah Yana yafe wa bayinsa kuma yana kuɓutar da su daga azabar lahira.

Wannan wata mai albarka yana ƙarfafa imani, ibada, da kyautatawa.

Don haka, ya kamata Musulmi su yi amfani da watan Ramadan don samun kusanci ga Allah da aikata kyawawan ayyuka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kyautatawa Manzon Allah SAW Ramadan watan Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar.

Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan  na Ramadan.

Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa  shugabanni jagorancin  don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma.

Namadi ya kuma yi addu’ar samun  zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Radiyon  Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamnan ya kuma karɓi manyan baki da suka kai masa gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NUJ Kebbi Tayi Kiran Ayi Bukukuwan Sallah Lafiya
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
  • Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi
  • Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal
  • Azumin Sitta Shawwal a Musulunci
  • Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
  • Wani Asbiti A Amurka Ya Kori Wata Likita Daga Aiki Bayan Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya
  • Gwamna Umar Namadi Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Sallah Karama
  • Mutane 9 Sun Mutu Sanadin Haɗarin Mota A Katsina