2025-03-31@23:14:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10

«Manzon Allah SAW»:

    A yayin da muka kammala watan azumin Ramadan, muna gabatar da wannan fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki ta Sallah kamar haka: Zakkar Fidir: Zakatul-Fitr ko Zakkar Fid-da-Kai, ita ce sadakar da ake fitarwa a karshen azumin watan Ramadan. Sunnah ce...
    Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa...
    Takawa ta kebantattun kebantattu: sun hada duk abin alkairi na gama-garin mutane, sun hada duk abin alkairi na kebantattu sannan sun kara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah, ba su ganin wanin Allah, a ko da yaushe suna Fadar Allah ko suna Fadar Annabi (SAW) ko suna fadar Waliyyan Allah. Wadannan Takawa guda Uku,...
      Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi. An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa...
    Annabi (SAW) yana da Alfadarai Bakwai, akwai wazanda ya rike har ya rasu suna wurinsa akwai kuma wazanda ya bai wa wasu daga cikin sahabbansa. Wacce ya je yakin Hunaini da ita, wani sarkin Larabawa (zan makafatul kinani) ne ya bashi, akwai wacce sarkin Ailatu ya bashi akwai ta sarkin Limatul Jandali, akwai ta Sarki...
    Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa. Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu. Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne...
    In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin...
    Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita...
    Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara...
۱