Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC
Published: 2nd, March 2025 GMT
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ce ita ce ta kai samame otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Minna, Babban Birnin Jihar Neja.
A yayin farmakin, an kama aƙalla baƙi 10 da ake zargi da aikata damfara a Intanet, wanda aka tafi da su Kaduna.
Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a EdoWani ma’aikacin otal ɗin da ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ’yan bindiga ne suka yi basaja a kayan EFCC, sula sace baƙi 10 a ranar 27 ga watan Fabrairu.
“Ba ’yan bindiga ba ne. Jami’an EFCC ne suka zo suka kama wasu ‘yan damfara suka tafi da su Kaduna,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya kuma yi watsi da wannan jita-jitar.
Ya shawarci ’yan jarida su tuntuɓi EFCC domin tabbatar da sahihancin lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan damfara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a.
Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a ga rayukan wadanda abin ya shafa a kauyen Bunkure na jihar Kano inda wadanda abin ya shafa suka fita tare da kuma da bada tabbacin ga iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a gurfanar da masu laifin gaban kuliya.
Allah wadai da gwamnan ya biyo bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai wa mafarautan, wadanda aka yi kuskuren cewa masu garkuwa da mutane ne, wanda ya yi sanadin kashe mutane 16.
Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce, inda shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a farauto wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da umurtar jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa.
Okpebholo ya bada tabbacin cewa gwamnatin sa za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin an kamo duk wanda ke da hannu a harin tare da gurfanar da shi gaban kuliya. Ya zuwa yanzu dai an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a lamarin.
Gwamnan ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano da ma daukacin yankin Arewa kan rashin daukar doka a hannunsu da sunan harin ramuwar gayya.
Ya sanar da cewa, ana shirin bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.
Gwamna Yusuf wanda ya karbi bakuncin Okpebolo a Kano, ya yi alkawarin bayar da tallafin kudi da kayan abinci ga iyalan mafarauta da aka kashe a Uromi, jihar Edo.
Ya kuma yi alkawarin cewa za a biya diyya ga wadanda lamarin ya shafa, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO