2025-04-02@17:30:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 589
«yan damfara»:
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata,...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin...
Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu. A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa. Haaland Zai...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin...
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang...
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa. “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi. Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu. Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara...
Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi. A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci. Masana harkar man fetur sun yi...
Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo. Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na...
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an...
“Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban. A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda...
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da...
Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a...
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin...
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon...
Rahotanni sun ce, wani ɗan kasar China ya kama matarsa tana cin amanarsa da wanda ya ba ta aiki a lokutan aiki ta hanyar amfani da wata na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙi da ake sarrafa ta daga nesa, tana leƙen asiri daga nesa. Mutumin mai hazaka da aka fi sani da Jing...
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da...

Jakadan Kasar Rasha A Saliyu Ya Ce Kasar Rasha Tana Nazarin Yiyuwar Fara Hakar Ma’adinin bauxite A Kasar
Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin...
Yawancin wadanda suke da HNd basu samu damar tafiya aikin Yiwa kasa Hidima/Aikin Bautawa kasa wanda hakan ne kuma aka gay a kamata ayi masu adalci kan lamarin Sai dai kuma irin ci gaban da aka samu ya kawo ko samar da wata matsala ta yadda wadanda suka yi karatun suka kammala a makaranta sai...
Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar...
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa...
Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu,...
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam...
Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa...
Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har...
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa...
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano...
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki,...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar....
A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da...
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun tattauna batutuwa da dama domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne a Abuja bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci...

Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba...
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu...
Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan...
Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200....
Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo...
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000. An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da...
Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta...