NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki
Published: 3rd, March 2025 GMT
Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa.
NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C.
Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yara Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansuChannels TV ya ruwaito wannan daga sanarwa da NLC ɗin ta fitar a ranar Lahadi bayan wani taro da ta yi a Jihar Adamawa.
“NLC ba ta amince da yunƙurin Hukumar Lantarki ta Nijeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarkin kwastomomi daga layin B da A da sunan haɓaka samun lantarki ba, alhali kuma yunƙuri ne kawai na ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba,” in ji sanarwar.
“Ya bayyana ƙarara cewa dai yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci ta hanyar ƙara kuɗin haraji da lantarki da sauransu a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya tsaya cak.”
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba za ta lamunci ƙarin kuɗin wutar ba, inda ta yi barazanar shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar.
A makon jiye ne dai Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar da cewa za a mayar da masu amfani da lantarki a layin Band C da B zuwa layin A.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kuɗin Lantarki ƙara kuɗin
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɓarayin waya a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago.
Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar SakkwatoSai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata.
SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin sayen wayoyin hannu da aka sata.
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da ababen zargin a gaban kuliya da zarar sun kammala bincike.
Rundunar ta gargaɗi ’yan kasuwa da su zama masu lura da abokan hulɗar da suke mu’amala da su, yana mai cewa akan samu miyagu da suke sojan gona a matsayin masu sayen kayayyaki a kasuwa.
Kazalika, rundunar ta yi kira ga duk wani ɗan kasuwa da irin haka ta faru da shi da ya gaggauta kai rahoto ofishin ’yan sanda mafi kusa.