2025-04-03@21:29:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1013
«ƙara kuɗin»:
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Rahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. “Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce...
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin fasahohin haƙar ma’adinai don tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci. “Lokacin da ya je masana’antar, Gwamna Lawal ya zagaya wurare da dama, inda ya fara tun daga magudanar ruwa da zuwa duka sassan injina da kayan aiki. “Gwamna Lawal ya kuma ziyarci wurare daban-daban a cikin masana’antar, ciki har da gidan wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga ɗaukacin kamfanin,...
An shiga firgici da safiyar Alhamis ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin ruwan. Wutar ta bazu cikin masaukin fasinjoji da sauri ta kama wasu fasinjojin da ke ciki. Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye “Akwai wani babban abin fashewa daga ɓangaren injin jirgin wanda hakan ya haifar da gobara wadda ta laƙume jirgin. Majiyar ta ƙara da cewa, “har yanzu ba a san...
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar wa ɗalibai da ma’aikata hanyar sufuri mafi aminci, mafi dacewa, da sauƙaƙe ƙalubalen da ke tattare da zirga zirga tsakanin sassan jami’ar. Shugaban jami’ar wanda ya samu rakiyar magatakarda Haruna Aliyu da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa da shugaban dakin karatu na jami’ar Dr. Kabiru Dahiru Abbas da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Lamara Garba da Farfesa Yakubu Magaji Azare, Shugaban jami’ar ya...
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida. “Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da...
Daga ƙarshe, ya buƙaci sojojin da su ƙara ƙwazo domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su. Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba. Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba. Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar. Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata, wanda ya wanke gadar wucin gadi da mutanen yankin suka gina a matsayin madadi. Wakilin LEADERSHIP a wurin gadar da sanyin safiyar Larabar nan, ya gano cewa, hanyar wucin gadi da mazauna kauyen suka gina, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya wanke ta, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya suka makale a gaɓar...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban tattalin arziki a duniya. Don haka, ana kyautata tsammanin cewa, wannan sabon tsarin harajin zai sake fasalin yanayin kasuwanci a duniya, ganin cewa, wasu masana’antu za su fuskanci tsadar kayayyaki da kuma durkushewar hanyoyin samar da kayayyaki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu. A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa. Haaland Zai Ziyarci Likita Saboda Raunin Da Ya Samu A Ƙafa Sanarwar ta ce wannan lokaci zai ba shi damar tsara hanyoyin da za su inganta ci gaban ƙasa yayin da yake shirin cika shekaru biyu a kan mulki. Duk da kasancewarsa a waje, Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati tare da tuntuɓar manyan jami’ansa har zuwa lokacin...
A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ƙwazo da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya. A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin. Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko’ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta...
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa. “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi. Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu. Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara cafke wadande ake zargi da aikata wannan aika-aika. “An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi wadanda aka kashe adalci”. In ji Okpebolo Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi. A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci. Masana harkar man fetur sun yi gargaɗin cewa, idan ba a magance rikicin da wuri ba, farashin mai na iya haura Naira 1,000 a wasu yankuna. Gwamnatin Tarayya ta taɓa bayar da umarni cewa a sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da Naira domin daidaita farashin mai, amma yarjejeniyar ta ƙare a watan Maris 2025. A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya. A yayin da...
Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
Jami’an tsaro sun bazama akan titunan manyan garuruwan kasar Zimbabwe domin dakile zanga-zangar da ake shirin yi domin yin kira ga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya yi murabus. Tsofaffon sojoji da mayakan da su ka samarwa kasar ‘yanci ne dai suka yi kiran a yi zanga-zangar, saboda kin amincewa da shirin shugaban kasar na tsawaita wa’adin mulkinsa. A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai jam’iyyar ZANU-Party, mai mulki a kasar ta sanar da cewa tana son Mnangagwa ya ci gaba da rike mukamin shugaban kasar har zuwa 2023. Mnangagwa dai ya hau karagar mulkin kasar ta Zimbabwe ne tun a 2017,bayan sauke Robert Mugabe daga kan karagar mulki cikin ruwan sanyi. Shugaban mayakan nemawa kasar ‘yanci Blessed Geza...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo. Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya. Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya “Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta’aziyya ba ce, a’a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci. “Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
Mai Martaba Idi Chiroma, Sarkin Gassol a Jihar Taraba, ya ce Musulmin da suka gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 sun nuna tsayin daka wajen sadaukarwa ga addini. Chiroma ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga al’ummar Musulmi a wani bangare na bikin Sallar karama a karamar hukumar Gassol da ke jihar. Ya kuma ja hankalin al’ummarsa da su jure duk wani kalubalen da suka fuskanta yayin da suka jure mawuyacin hali na baya-bayan nan domin ibada. Chiroma ya bayyana cewa wadanda za su koma ga tsohon halin da suke ciki na iya zama ba tare da albarkar da ke tattare da azumin watan Ramadan ba. ...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi. Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali. An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare. A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai. Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana shirin tallafa wa marayu 20,000 a faɗin Jihar Zamfara. Yayin da yake magana bayan cin abincin Sallah tare da marayu 500 a gidansa da ke Talata Mafara, Sanata Yari ya ce an shafe watanni tara ana tantance marayun daga ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne za su amfana da shirin. Abba Ya Nemi Gwamnatin Edo Ta Biya Diyyar Matafiyan Da Aka Kashe A Uromi Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF Ya bayyana cewa shirin tallafin wanda zai fara aiki kafin Idin Babbar Sallah, inda za a ware duk abin da marayun ke buƙata don kyautata rayuwarsu. “Mun shirya...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya. Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar. Da yake...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin. Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana. Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin...
A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi. An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi. Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita...
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike. A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa —Gwamnatin Kano Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar...
“Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban. A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar. Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince...
Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah. A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma. Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Sarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci...
Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon. A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba. A halin yanzu dai yan takara...
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1. Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba. Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta...
Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan shekara 4 ya yi kururuwa, inda ya kira ’yan sanda bayan mahaifiyarsa ta shanye masa ice cream dinsa. Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Al’amarin ya faru ne a cikin a garin Mount Pleasant, Wisconsin — mai nisan kilomita bakwai, yamma da Racine — lokacin da yaro dan shekara 4 ya...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru. Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi. Dangane da...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...
Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon bude ido wani yunkuri ne mai matukar muhimmaanci. Kamfanin dillancin labarum “Iran” ya ambato; Ridha Salihi Amiri yana mai yin ishara da tarihin alakar kasashen biyu ta fuskar al’adu, sannan ya kara da cewa; Kasar Tunis ta samu ci gaba sosai a tsakanin kasashen Lrabawa ta fuskar inganta harkokin yawon bude ido. Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Iran take da wuraren bude...
Shugaban gwamnatin soja na kasar Guinea Janar Mamadi Doumbouya ne ya yi wa tsohon shugaban sojan kasar Camara afuwa bayan da aka yanke masa zaman gidan kurkuku bisa laifin kisan kiyashin da ya faru a 2009 a birnin Conakry. Kafafen watsa labarun kasar ta Guinea ne su ka sanar da afuwar da shugaba Mamadi ya yi wa Camara bisa dalilai na rashin lafiya. Bugu da kari kakakin fadar shugaban kasa Janar Amara Camara wanda ya yi sanarwar ya ce, an yi hakan ne bisa shawarar da ma’aikatar shari’a ta gabatar. Camara dai ya mulki kasar ta Guinea ne daga 2008-2009, an kuma yi masa shari’a ne a watan Yuli na 2024, saboda yadda a zamanin mulkin nashi aka yi amfani...
Rahotanni sun ce, wani ɗan kasar China ya kama matarsa tana cin amanarsa da wanda ya ba ta aiki a lokutan aiki ta hanyar amfani da wata na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙi da ake sarrafa ta daga nesa, tana leƙen asiri daga nesa. Mutumin mai hazaka da aka fi sani da Jing ya fara zargin cewa, matarsa na yin wata alaƙa ne bayan ta yi nisa sosai da shi kuma ta canza mu’amalarta sosai, ciki har da ziyartar iyayenta fiye da kowane lokaci da kuma kawo uzuri a duk lokacin da ya yi mata rakiya da kuma ƙarin lokaci a wurin aikinta. Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar...
Ranar idin Karamar Sallah rana ce da Musulmi ke farin cikin kammala azumin watan Ramadan wacce ke zuwa a ranar daya ga watan Shawwal din shekarar Musulunci. Allah Madaukakin Sarki ya shar’anta Sallar Idi a matsayin ibadar kammala Azumin Ramadan wacce take kan kowane Musulumi, baligi, mai hankali, kuma mazaunin gida — namiji ko mace. Zakatul Fidr: Yadda ake fitar da Zakkar Kono Zakkar Fidda Kai ta fi kayan sallah da abincin sallah A yayin da ake shirin shan shagalin Kamar Sallah, malamai sun bayyana muhimman abubuwan da ya kamata su aikata a ranar, kamar yadda Hadisan Annabi (SAW) suka nuna: Duk Musulumi maza da mata manya da kanana su halarci sallar Idi. Fitar da zakkar fid da kai, wato...
Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya bayyana cewa ware ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan wata hikima ce ta jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ruhullah Alkhomaini(q) wanda ya dace da hakan kan musulmi a kan wannan al-amari. Kuma tare da yardarm All…ana ci gaba da samun nasara a kan wannan manufar. Sheikh Kasim ya kara da cewa duk tare da gagarumin taimakon da HKI take samu daga kasashen yamma...
An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan: Kabbarori: Daga lokacin da aka ga jinjirin watan Shawwal (Karamar Sallah) ana so mutum ya rika yin kabbarori a bayyane har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi. Daya daga cikin siffoffin yadda ake kabbarorin shi ne: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd. Zakkar Kono: Wajibi ne ga duk wanda...
A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya. Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama. A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi. Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan...

Jakadan Kasar Rasha A Saliyu Ya Ce Kasar Rasha Tana Nazarin Yiyuwar Fara Hakar Ma’adinin bauxite A Kasar
Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
Shugaban Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam ya kaddamar da rabon kayan sallah da kuma kudin dinki ga al’ummar yankin. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a garin Jahun, shugaban Karamar Hukumar yace Hakimai na gundumomin Jahun da Aujara da Gunka da Kadawawa da Limaman masalatan juma’a 79 na yankin za su amfana da kayan sallah da kuma kudin dinki. Jamilu Muhammad Danmalam ya bayyana rashin Jin dadinsa bisa yadda ake mantawa da iyayen kasa da Malaman Addini a irin wannan lokacin da ya kamata a taimake su. Ya ce yana daya daga cikin kudurorinsa na shigo da kowanne bangare na al’umma cikin tsarin shugabancinsa dan kowa ya anfana. Danmalam ya...
Sunana Naja’atu Baffa Jihar kaduna: Ni dai a gaskia ban son akwai wani anko da za ai wannan sallar ko babu ba. Ina son saka takalmi mai dan tudu ba sosai ba, sai mayafi blue black, sai atamfa ta riga (half bubu) da ‘skirt’, sai sarka da dankunne da Awarwaro ‘silver’. Ina sha’awar cin Snacks irinsu meatpie, samosa, doughnut da kuma cake, sai kuma Yoghurt mai inibi. Ina son in ziyarci kanwar babata wacce take a cikin garin Adamawa. Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa: To batun shidimar sallah sai mu ce Alhamdullilah domin duk tanadin da mutum yayi sai ya kare, duba da yadda kayayyakin suturu ko tufafi suke tsada don haka sai mutum yayi amfani da...
Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300. A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu. Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
Yawancin wadanda suke da HNd basu samu damar tafiya aikin Yiwa kasa Hidima/Aikin Bautawa kasa wanda hakan ne kuma aka gay a kamata ayi masu adalci kan lamarin Sai dai kuma irin ci gaban da aka samu ya kawo ko samar da wata matsala ta yadda wadanda suka yi karatun suka kammala a makaranta sai ta kasance wasu daga cikinsu basu samu damar tafiya aikinyiwa kasa hidima ba saboda irin karatun da suka yi. Da yake bada ta shi gudunmawa darekatan lamurran ‘yan jaridu da hulda da jama’a ma’aikatar ilimi ta tarayya Boriowo Folasade, ya fitar da sanarwa wadda take tabbatar da gaskiyar lamarin na abubuwan da suka biyo bayan dukkan tarurrrukan da kuma ganawar da aka yi. Sanarwa ta...
Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...
Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike da kirkiro wasu abubuwa.” Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya. da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya...
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam Khumaini ( r.a) da ya ayyana ranar Kudus a duniya a 1979, wacce ita ce juma’ar karshe ta watan Ramadan, a wancan lokacin manyan kasashen duniya masu takama da karfi suna kokarin ganin an mance da batun Falasdinu da kuma kasakantar da shi da cewa batu ne na Larabawa kadai. Limamin na Tehran ya kuma kara da cewa, abinda Imam Khumain ( r.a) ya yi...
Aƙalla mutum 19 aka kama bayan wata arangama tsakanin mabiya ɗarikar shi’a da jami’an tsaro a Abuja. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Banex, da ke Wuse 2, inda mutane da dama sun jikkata, sannan mutum ɗaya ya rasu. An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ta ce ’yan shi’a sun kai wa jami’an tsaro hari da bindigogi, duwatsu, da wasu makamai. A sakamakon haka, aka tura ƙarin dakaru domin kwantar da tarzomar. “Kwamishinan ’yan sanda, CP Ajao Saka Adewale, ya yi tir da wannan hari da aka kai wa jami’an tsaro,” in ji kakakin rundunar,...
A yammacin yau Juma’a ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a birnin Lhasa na jihar Xizang wato Tibet, inda aka fitar da “Takardar bayanin ci gaban sha’anin kare hakkin dan Adam a Tibet a sabon zamani”. Takardar ta yi nuni da cewa, a ko da yaushe, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna mai da hankali kan ayyukan da suka shafi Xizang, kuma suna ci gaba da kyautatawa da raya tsarin mulkin Xizang, da daukar matakai masu inganci don raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a, da kawo alheri ga jama’a, da inganta hadin kai da ci gaban kabilu, da kuma kare hakkin dan Adam na dukkan kabilun...
Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai. Matsalar tsaro Ko shakka babu...
Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin. Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana. A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa ka’ida ba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da raunata jama’ar kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na kasar. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kawo karshen rashin daukar mataki da kuma yin shiru dangane da farmakin da sojojin Amurka ke kaiwa Yemen. Ya ce Amurka na ci gaba da kai hare-haren soji kan kasar Yemen tare da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar DSP Yazid, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin. Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan...
A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar. Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin. Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a...
A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun tattauna batutuwa da dama domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne a Abuja bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana. Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana. Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria tsakanin kasashen biyu. Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua ...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, da hauhawar farashin kayan abinci da man fetur, da bala’in yanayi, da kuma matsugunan jama’a, ya sa miliyoyin mutane ke fafutukar samun abinci mai gina jiki. Rahoton UNICEF ya kara bayyana cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Nijeriya, kusan miliyan 11, na fama da matsanancin rashin abinci, wanda hakan ya sa kashi 50 cikin 100 na ka fuskantar barazana ga...
Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025. Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi. Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka...
Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar. Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi Yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe. A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri. A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi...

Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba ne illa murkushewa da kuma takura wa wasu kamfanonin kasashen ketare, tare da danne hakkokin sauran kasashen duniya na samun ci gaba. Yana mai cewa, hakan zai yi matukar cutar da kamfanonin tare da kawo cikas ga kwanciyar hankali da samun wadataccen tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ya kara da cewa, matakin zai yi kafar ungulu ga kokarin warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da...
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji. La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani sabani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za...
Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana wasan ɓuya da jami’an tsaro da wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Ɗan jarida mai bincike kan harkokin ’yan bindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗan bindigar. Isuhu Yellow ya yi fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.
Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar. Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci. A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya. Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da suke rike da birnin na Khartum. Sojojin kasar ta Sudan sun nuna shugaban majalisar sojan kasar Janar Burhan a cikin fadar shugaban kasa, inda ya sanar da cewa; An ‘yanto da Khartum. A karon farko jirgin Janar Burhan ya sauka a filin saukar jiragen sama na Khatrum, tun bayan da yaki ya barke. Tun a jiya Laraba ne dai sojojin na Sudan su ka sanar...
Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet. “Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in...
Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na tallafawa shirin inganta ilimi na bunkasa Afirka (BEAR) III, wani shiri na hadin gwiwa da hukumar kula da ilimi da kimiya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da Jamhuriyar Koriya suka yi. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Balarabe Abdullahi Kiru, yace aikin yana da nufin haɓaka ilimin fasaha da na sana’a a faɗin Afirka, tare da mai da hankali kan ƙarfafa tsarin ilimin fasaha da na sana’a da horo (TVET). Aikin zai mayar da hankali ne kan harkar noma, tare da mai da hankali kan sarrafa kayan noma da sarrafa su bayan girbi. A cewar...
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi alkawarin inganta sansanin horas da kuratan sojoji dake Zaria wato Depot domin baiwa hukumar Soji damar ci gaba da aikin horaswa a wajen. Ministan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kai ziyarar tantance sojojin Najeriya da ke Chindit Cantonment a Zariya. Ministan ya kuma ce, ma’aikatar tsaro ba za ta bar wani abu ba, wajen tabbatar da cewa makarantar firamare ta Chindit ta samu ingantuwar kayan aiki don dacewa da tsarin zamani a matsayin hanyar kara kwarin gwiwa na hafsoshi da sojoji na Kantoment da ke amfana da wajen. Ya kara da cewa ofishin sa zai hada kai da gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an kammala makarantar...
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000. An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma’aikatan gwamnati. “Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,”...
Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman. Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu. Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a...
Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...