Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ina mana lale barka da zuwan masoyi watan Ramadan. Da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkan alheran da ke cikinsa kuma Ya sa mu zama daga cikin ’yantattun bayinsa, amin.
Ramadan: Alherai goma ga Ma’aurata.
1. Gyaran aure:
Ramadan lokaci ne na ibada da kyautata ibada. Aure da zamantakewar aure yana ɗaya daga cikin manyan ibadojin Addinin Musulunci.
A wani ingantaccen Hadisi, Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Yace, Aure rabin Addini ne. Don haka kamar yadda muke dagewa wajen ayyukan addini da gyaran alakar mu da Allah, to ya kamata ma’aurata suyi amfani da Ramadan wajen gyaran alakar su da inganta zamantakewar tsakaninsu.
Bayan dagewa wajen ayyukan ibada irinsu Sallah cikin lokaci, karatun Alkur’ani, tarawiy da sauransu, to sai a dubi wasu wajibbun ayyuka zaman aure su a ingantasu, a kyautata su, waɗanda aka mance ba a yi a farfaɗo da su.
Haka kuma yadda muke yawan istighfāri cikin Ramadan da komawa ga Allah cikin tuba da neman yafiyar ayyukanmu na zunubi, to haka ya kamata ma’aurata su koma ga abokin aurensu, su tunano abubuwan da suka aikata na rashin kyautatawa da ba daidai ba da ganganci ko bisa kuskure, su basu hakuri kuma su nemi yafiya da gafararsu. Sannan su juya cikin kawunansu, su duba su gani meye abokin aurensu ya yi musu na laifi bisa kuskure ko da ganganci da kyautata niyya su yafe masu, wannan laifin su share shi da zuciya da ma’aikatar hankalinsu.
Duk Ma’auratan da suka aikata haka za su ji wata sabuwar iska mai daɗi tana ratsawa cikin rayuwar aurensu. Wannan zai sa ayyukan ibada su zama masu sauki da daɗin aikatarwa garesu. Sakamakon hakan shi ne more ma jiga-jigen alherai guda biyu, na watan Ramadan da kuma na ibadar aure.
2. Ibadar aure:
An san watan Ramadana watan ibada da neman kusancin Allah da tsarkake ruhi.
Abinda ba a cika ba muhimmanci shi ne alakanta watan Ramadan a matsayin watan assasa da inganta ibadar aure. In mun lura, a cikin Alkur’ani, bayan Allah Maɗaukakin Sarki ya yi magana akan Ramadan, aya mai bi mata sai tayi magana akan addu’a.
Aya mai bi mata sai ta yi magana: An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah Yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa’an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, za su yi taƙawa. -Aya ta 187, Suratul Bakarah Wannan aya ta bayyana muhimmancin ibadar aure a tsakanin Ma’aurata, don haka yakamata ma’aurata su assasa wannan ibada tare da sauran ibadojinsu a cikin wannan wata mai alfarma.
Mu sani cewa azumi yana wanke hanyoyin jini, yana kauda dattin na’urorin kwakwalwa, kuma yana gyara manyan namomin jiki, ciki har da na’urorin sha’awa.
Sannan canjin yanayin abinci ta hanyar yawan kayan marmari da ganyayyaki shi ma wani al’amari da ke taimaka wa ma’aikatar sha’awa. Don haka ma’aurata suyi amfani fa ɗimbin damarmaki wajen assasa da zafafa ibadar aurensu cikin Ramadan.
3.Tahaddu Tahabbu
Manzon Allah Sallalahu Alayhi wa Sallam Ya ce: Ku yi musayar kyaututtuka tsakaninku, sai ku so junanku. Wannan wata kyakykyawar Sunnah ce da ya kamata ma’aurata su assata cikin wannan wata na Ramadan don karin dankon so da kauna a cikin rayuwar aure.
Ba dole sai abu mai tsada ba, kawai ’yan ƙananan abubuwa da za su sa abokin aure ya ji, shi na musamman ne, za su sa yaji ai ana ji da shi ko ita.
Misali kamar maigida ya sayowa uwargida wata irin cakwalet mai daɗi koda kwaya ɗaya ce, ko uwargida ta shirya wani girki na musamman daga aljihunta don mijinta, abinda ta san yana matukar so koda kwaɗon rama ne ko rummace.
Sai mako na gaba in sha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a ko yaushe
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ramadan watan Ramadan ma aurata su ibadar aure
এছাড়াও পড়ুন:
Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya
Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci.
A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba boyayayen abu bane, musammamn duba da cewa, yawan aukuwar tashe-tashen hankula, kalubalen rashin tsaro da matsatin tattalin arziki, suna manyan hummulhaba’isin da ke janyo karancin abinci a a cikin alumma.
Misali, yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabas, ayyukan ‘yan bindiga daji a yankin arewa masu yamma da kuma rikice-rikicen kabilanci a sauran yankuanan, sun janyo tarwatsa miliyoyin alumomi daga matsugunan su, lalata gonakansu wanda hakan ya janyo, aka samu raguwar noma amfanin gona, sauyar da amfanin gonar, inda hakan ya kuma haifar da karancin abinci a cikin alumma tare da samun hauhawan farashin kayan abinci.
Akasarin fannin noma a kasar nan, ya dogara ne kachokam kan samun ruwan damina, inda kuma fanin ke cin karo da samun sauyin yanayi, wanda hakan ke sanya wa a fusaknaci fari ko sauyin samun yanayin saukar ruwan sama da kuma akuwar annobar ambaliyar ruwan sama, inda hakan ke yiwa amfanin gona da aka shuka illa da kuma shafar dabbobi.
Wannan matsalar ta ambaliyar ruwansaman ba wai ta tsaya a kan amfanin gona bane, ta na kuma lalata matsunan alumma da kuma kara haifar da talauci a tsakanin su.
Sauye-sauye na dogon zango kan tattalin arziki da Gwamnatin Tarayya mai ci ta kirkiro da su a shekarar 2024 ta kuma wanzar da su, sun kasance za su iya janyo nakasu, a yunkurin da ake yi na samar da wadataccen abinci a kasar nan.
Duba da yadda ake ci gaba da samun hauhawan farashin kaya, karyewar darajar Naira, samun karuwar farashin man fetur, hakan yakara haifar da tsadar noma amfanin gona, tsadar sufuri, wanda hakan zai kara sanya wa masu sayen kayan abincin, su saya da tsadar gaske.
Bugu da kari, matsain na tattalin arzikin ya kuma janyowa alumma rashin samun wasu abubuwa kamar na iya kula da kiwon lafiyarsu da ci gaba da daukar nauyin karatun ‘ya’yansu.
Hukumar FOA tare da sauran masu ruwa da tsaki da suka hada da sasshen samar da abinci na Majalisar dinkin Duniya wato WFP da Asusun tallafawa kanannan yara na Majalisar dinkin Duniya UNICEF, Gidanuniyar Kula da kananan Yara da kuma kungiyar Kare Raji ta Mercy Corps, sun jima suna jaddada mahimmancin daukar matakan gaggawa na jin kai kafin aukuwar dukkanin wata annoba.
Daga cikin sakamkon taro na CH da aka gudaanr a Abuja wakilin FOA Nijeriya Kouacoau Dominikue Koffy ya jabawa Gwamnatin Tarayya da kuma masu ruwa da tsaki a CH, musamman bisa mayar da hankali da suka yi wajen ganin an samar da wadataccen abinci da kuma sanya ido da suke yi don a samar da wadataccen abincin.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatocin Jihohi da sauran abokan hadaka da su zuba kudade domin a wanzar da tsarin na kasa da a za a gudanar a watan Okotobar 2025, inda ya yi nuni da cewa, ba tare da an samar da bayanai da samar da kyakyanwan shiri zai yi wuya, a cimma burin da aka sanya a gaba.
A ra’ayin wannan jaridar, mun yi amannar cewa, kalubalen karancin abinci abu ne da ke bukatar hada karfi da karfe, wanda hakan zai wuce batun siyasantar da maganar da shelanta samar da Rumbunan adana hatsi.
Ya zama wajibi Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta baci wajen samar da wadataccen abinci tare da kafa tawaga mai karfi da za ta hada da Ma’aikatun Gwamnati, Hukumomin Tsaro, kungiyoyin Jin kai, Kamfanonin Masu Zaman Kansu da sauran masu ruwa da tsaki, musamman domin a samar da tare da kaddamar da kyakyawan tsari na kasa.
Dole ne Gwamnatocin Jihohi su marawa kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi kan zuba nannun jari wajen samar da abinci, samar da kayan adana amfanin gona, tsarin rabar da amafnin gonar, kuma kamfanoni masu zaman kansu, musamman masu yin noma domin samun riba, suma suna da gudunmawr da za su bayar wajen kara bunkasa fannin aikin noma, musamman domina a tabbatar da cewa, abincin ya isa ga teburin, musamman marasa karfi, wadanda kuma za su rinka sayen abincin, a cikin farashi mai sauki.
Ya zama wajbi UNICEF, FAO, WEF, da sauran takwarororin su, da su kara kaimi wajen aikin sa kai a yankunan da karancin abinci ya fi kamari, domin taimakawa Gwamnati wajen wanzar da aikin na dogon zango.
A zaman mu na kasa, ba ta sabu mu yi ikirarin cewa, kasar na kan turba ba, bayan alhali, ‘yan kasar na ci gaba da fuskantar yunwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp