2025-03-06@03:56:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1646

«ibadar aure»:

    Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar  Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa. Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na...
    Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin  daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma. Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar. Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau. Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran  masu bukata ta...
    A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Wannan mataki ya zo ne saboda yadda ayyukan hukumar ke jan hankali, inda sau da yawa ake samun saɓani tsakaninta da wasu. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala ne, ya bayyana cewa an yi wannan dokar gyara ne don daidaita harkokin ɗaukar fina-finai da kare addini da al’adu. Ya ce daga yanzu...
    Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar. Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu...
    A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14. Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban kasar Sin, musamman ma a fannin sa kaimi ga inganta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da dunkulewar masana’antu, da sa kaimi ga inganta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, da shigewa gaba wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na ci gaban kasar, da kuma ba da misali a fannin samar da wadata ga jama’a baki daya. (Safiyah Ma) Daga...
    Hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila (Shin Bet) ta amince da gazawarta wajen hana harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su. Ya ce, da hukumar ta Shin Bet ta yi wani abu daban a cikin shekarun da suka gabata kafin harin da kuma a daren da aka kai harin… da an kaucewa hakan. “A matsayina na shugaban hukumar, zan...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York. Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.” Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya...
    Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi. Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5. “Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da shirin sake gina Gaza na Masar da aka amince da shi a wani taron gaggawa na kasahen Larabawa da aka yi a birnin Alkahira. Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, taron na birnin Alkahira ya nuna wani muhimmin mataki na daidaita alaka tsakanin Larabawa da Musulunmi da Falasdinu, musamman a ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da yammacin kogin Jordan da kuma al-Quds. Kungiyar ta yabawa shugabannin kasashen Larabawa da suka yi watsi da yunkurin raba Falasdinawa da kasarsu, tana mai danganta da sako mai cike da tarihi. Hamas ta yi marhabin da kiran tana mai bayyana shi a matsayin “tsari...
    Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi A ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba. Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci. Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar. Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.” Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta. Martanin Akpabio Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta gabatar da ƙorafinta a gaban Majalisar Dattawa kan Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, bisa zargin cin zarafi da kuma tauye mata haƙƙi a majalisa. A ranar 20 ga watan Fabrairu ne rikici ya ɓarke a zauren majalisar, lokacin da Shugaban Majalisar, Akpabio, ya umarci wani ma’aikacin majalisa da ya fitar da Sanata Natasha daga zauren, bayan da aka ce ta ƙi komawa sabuwar kujerar da aka ware mata. Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Wannan lamarin ya jawo suka daga ƙungiyoyi da mutane da dama, inda suka nemi a yi bincike kan abin da ya faru. Abin da Sanata Natasha...
    Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba. Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance. Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa. Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki. A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta. Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin  yakin neman zabe. Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani matashi Safiyanu Dalhatu, mai shekara 20, kan zargin kashe mahaifiyarsa har lahira a unguwar Abujan Kwata. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ’yan Kwamitin Tsaro na Unguwar ne suka kai rahoton lamarin ofishin rundunar na ‘A’ Division da ke Bauchi. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau Bincike ya nuna cewar mahaifiyar matashin, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta samu karaya a hannayenta biyu sakamakon dukan da ya mata bayan sun samu saɓani. Bayan samun rahoto, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Abdullahi Muazu, sun garzaya wajen da lamarin ya faru. Sun kai Salama Asibitin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya nesanta kansa daga zargin cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ya ce mahaifiyarsa ta ba shi tarbiyya mai kyau, kuma yana mutunta mata. Akpabio ya bayyana hakan ne bayan da Sanata Natasha ta zarge shi da cin zarafinta ta hanyar neman kwanciya da ita, wanda ya haifar da rikici a zauren majalisa. Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce: “Ina son duniya ta sani cewa ban taba cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace ba. Mahaifiyata ta yi min tarbiyya mai kyau, ina girmama mata.” Wannan bayani na Akpabio ya zo ne a yayin...
    Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
    Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma  jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne. Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ya yi watsi da bukatar HKI na kwance damarar dakarun kungiyan a matsayin sharadi na ci gaba da aiwatar da yarjeniyar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025. Kungiyar ta kara da cewa, kwance damara dakarun kungiyar jar layi ne a wajenta. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa HKI tana bukatar ta raba kungiyar da makamanta, kafin ta ci gaba da aiwatar da yarjeniyar ta watan Jeneru. Wannan  bukatar dai ta sa tababa a cikin yiyuwar tsagaita wuta tsakanin HKI da Hamas ya dore. Yarjeniya ta yanzu dai, wacce ta faraaiki a ranar 19 ga watan Jenerun shekara ta 2025, kuma an tsara shi bisa marhaloli 3. Daga...
    Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai  a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna. Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin...
    “A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.”   Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai...
    Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza. Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba. Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700. EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa. ’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan...
    Tunin Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya umarci babban baturen ɗansanda a C Division da ya jagoranci tawaga ta musamman da za su gudanar da bincike kan lamarin a tsanake. A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, yunkurinsu a halin yanzu ya kai ga kama Fatima Mohammed, kishiya ga mamaciyar wacce a halin yanzu take tsare a hannunsu. “Bincike na farko ya nuna cewa, akwai zargin Fatima Mohammed na da hannu a mutuwar Hajara. A yayin da ake yi mata tambayoyi, an ce ta amince ta shaƙe ta har lahira, sannan ta yi yunƙurin ɓoye laifin ta hanyar zuba mata tafasasshen ruwa tare da ƙona jikinta da buhun da ke narkewa,” in ji CSP Wakil A...
    ’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe. An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin. Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa. Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba...
    Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka  kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. “Ma’aikatan jihar za su je aiki karfe 9 na safe sannan su tashi da karfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis maimakon zuwa karfe 5 da ake kai wa a baya, sai ranar Juma’a ma’aikatan za su je aiki da karfe 9 na safe su tashi da karfe 1 na rana kamar yadda aka saba”. Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, an yi wannan karimci ne da nufin samarwa ma’aikatan...
    Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira. Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta riƙa laƙume kaya da kadarori kafin ’yan kwana-kwana su iso wurin. Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa...
    Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba. A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za...
    A cewar rahoton, za a samar tare da aiwatar da wani tsari mai wa’adin shekaru 3, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa bangaren ilimi. Haka kuma, kasar za ta inganta raya ilimin dole mai inganci kuma bisa daidaito, tare da kara bayar da damar shiga makarantun sakandare. Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta inganta hada ilimin sana’o’i da ilimi na gama gari, tare da hada hannu da masana’antu da makarantu ta yadda ilimin sana’o’i zai kara dacewa da tsarin ilimi. Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin za ta aiwatar da gyare-gyare a makarantun gaba da sakandare cikin rukunoni, tare da daukar matakai masu kwari wajen fadada ingancin karatu da gaggauta samar da jami’o’i da bangarorin...
    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana farin cikinsa akan wannan tarihi, inda yace abu mafi muhimmanci shi ne ganin cewar Arsenal na da babbar damar tsallakawa zuwa matakin na kusa da na kusa da na karshe duk da cewar akwai jan aiki idan PSV ta ziyarci Arsenal a gidanta inji Arteta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila. Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban. Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da  shirin na...
    Babban magatakardar MDD Antonio Guterres  wanda ya halarci taron da kasashen larabawa suke yi a Masar, ya bayyana goyon bayansa ga tsarin da su ka bijiro da shi na sake gina yankin Gaza, ba tare da an fitar da Falasdinawa daga cikinsa ba. Gutress ya ce; Ina maraba da kuma nuna cikakken goyon bayana ga shirin da taron kungiyar kasashen larabawa ta bijiro da shi na sake gina Gaza.” Gutrress ya kuma ce: MDD a shirye take ta shiga da karfi a yi wannan aikin da ita. Haka nan kuma babban magatakardar MDD ya yi kira da a dauki duk matakin da ya kamata domin ganin ba a sake komawa yaki a Gaza ba. Gutteres ya kuma ce, Gaza ba...
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
    Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”. Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran. Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana...
    Shugaban  kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar. Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma. Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.
    Wasa ya koma kuka bayan da wani mai wasan barkwanci manne laɓɓansa ba sa buɗewa bayan da ya shafa musu gam din sufa-gilu a yayin da yake yin bidiyo kai-tsaye domin ƙayatar da masu bibiyarsa. Mutumin ya shafa gilu ne, inda ya manne laɓɓansa, wanda cikin dakika kaɗan, mannewar ta kama fatar laɓɓan kamar yadda ya so, inda hakan ya sa yabar laɓɓansa a rufe sosai. Fasinjoji 16 sun ƙone ƙurmus a Ogun DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana A zamanin da ake amfani da shafukan sada zumunta na zamani, mutane sukan yi iyakacin ƙoƙarinsu don samun mabiya da sakonsu zai kai gare su a intanet. Raye-rayen zuwa abubuwan barkwanci, suna yin tasiri a shafukan sada...
    Aƙalla fasinjoji 16 suka ƙone ƙurmus, yayin da wasu uku suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku ranar Talata a Jihar Ogun. Aminiya ta ruwaito cewa hadarin wanda ya rutsa da mota ɗaya kacal ya afku ne a gidan Buhari da ke kan titin Abeokuta zuwa Shagamu. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana ‘A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice’ An bayyana cewa, hatsarin dai ya rutsa da wata farar motar bas kirar Mazda mai lamba KJA 949 YJ, da misalin ƙarfe 1:00 na rana. Kakakin Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar. Ta ce ba...
    A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl. Game da hakan, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya riga ya sha fayyace matsayinsa na nuna adawa da matakin. Ya ce, har kullum jama’ar kasar Sin suna adawa da nuna fin karfi, da yin matsin lamba, da tilastawa, da kuma barazana, saboda hakan ba hanya ce da ta dace a bi yayin mu’ammala da kasar Sin ba. Ya kara da cewa, idan bangaren Amurka...
    A Talatar nan ne ofishin yada bayanai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da batutuwan da suka shafi sinadarin Fentanyl. Takardar mai taken “Shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl-Gudummawar kasar Sin.” Ta yi fashin baki game da yadda a ‘yan shekarun baya bayan nan, kasar Sin ke ta kara dora muhimmanci kan matakan shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, kana take ta karfafa hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, wajen dakile bazuwar miyagun kwayoyi, da zurfafa hadin kai da sauran kasashe masu ruwa da tsaki, ciki har da Amurka, wajen shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da sinadaran da ake samar da shi daga gare su, inda kuma aka cimma manyan...
    “Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.”   Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma.   Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa.   Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar...
    A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
    Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje.   Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS).   Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.   “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal   Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”   A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana...
    Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja. Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar da safiyar wannan Talatar. Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace Makama ya ce ’yan ta’addan sun biyo sawun tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ne bayan ya ciro kuɗi a banki, inda suka karɓe kuɗin sannan kuma suka kashe shi. Wannan lamari dai ya sake ɗaga hankalin mazauna Abuja a fannin tsaro musamman yadda...
    A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga a dama da ita, kuma za ta kasance mai bayar da shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Da yake tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, Lou ya ce, daukar matakin da Amurka ta yi bisa radin kai ya saba wa ka’idojin kungiyar...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin,  take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamsedeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta Janar na Tarayya. Naɗin nasa, wanda aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne daga ranar 7 ga Maris 2025, ranar da Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. Muhimmancin ƙamshi a rayuwar mace An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ana iya tuna cewa, tun a watan Disambar da ya gabata ne aka bayyana Ogunjimi mai shekaru 57 a matsayin magajin Madehin. Daga baya wani aka naɗa wani kwamitin ƙwararru da zai tantance wanda ya haɗa da manyan daraktocin daga a ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya yi...
    Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau ne za a gurfanar da yan adawar siyasa guda 40 da ake tuhumarsu  da aikata laifukan dake barazana ga tsaron kasa, a shari’ar da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama suke daukarta a matsayin bi ta da kullin siyasa. Wadanda ake tuhumar sun hada da jami’an diflomasiyya da yan siyasa da lauyoyi da kuma yan jarida dake sukar salon mulkin shugaban kasar Kais Saied. Zargin yi wa tsaron ƙasa zagon kasa da kuma shiga kungiyar yan ta’adda zai fuskanci hukunci mai tsananin, ciki har da hukuncin kisa. Tun a shekara ta 2023 ne ake tsare da wasu , yayin da da dama kuma suka tsere zuwa kasashen ketare. Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun yi kira da a...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa  kuma...
    Gwamnatin jamhuriyar  Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu  a kasar. Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen  50 zuwa 100 dole ne yayi rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa. Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci,  wannan yasa za ta bullon da sabon shiri tare da  wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar da ta bada damar aiki da shafukan sada zumunta a Kasashen,  domin dakile amfani da ita ta hanyar da...
    Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green Horizon, Farfesa Muhammed Sabiu (SAN) ne ya jagoranci taron wanda shirin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta shirya. Tun da farko a jawabinsa na bude taron, Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Sarkin Fulani Hamceta Alhaji Aminu Lawal Bagiwa ya wakilta, ya ja hankalin mahalarta da su tsaya domin sanin abin da za a ilmantar da su kasancewarsu na shugabannin al’umma kuma na farko da ake kawo...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis. Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), Sepp Blatter, da tsohon shugaban UEFA, Michel Platini, za su sake gurfana a gaban wata kotu a Switzerland kan zargin cin hanci da rashawa. Kotun ɗaukaka ƙara da ke Muttenz za ta saurari buƙatar ofishin babban mai shigar da ƙara na ƙasar, wanda ke son sake dawo da tuhume-tuhumen da ake yi wa Blatter, mai shekaru 89, da Platini, mai shekaru 69. Hasashe Kan Tarukan CPPCC Da NPC Na 2025 Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya Blatter ya ce yana fatan kotun za ta tabbatar da sahihancin kwantiragin da ke tsakaninsa da Platini, kamar yadda wata kotu ta yi a shekarar 2022, lokacin da aka wanke su daga...
      Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa.   Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa, Abuja, a yau.   Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin kuɗin wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin daɗi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.   “Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai wata takarda ta kuɗi ba...
      Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025.   Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu.   “Farawa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe kuma su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis, raguwar awanni biyu daga tsohon lokacin rufewa na karfe 5:00 na yamma. A ranakun Juma’a kuwa, ma’aikata za su fara aiki da karfe 9:00 na safe su kuma tashi da karfe 1:00 na rana, kamar yadda aka saba.” A...
    A cewar ‘yansandan Ukraine, hare-haren Rasha sun raunata mutane a yankin Donetsk, sannan a ƙaramar hukumar Kherson, mutum biyar sun mutu, yayin da 13 suka jikkata, ciki har da ‘yansanda da suka je ɗauko gawar wani mutum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin  kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
    Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa sojojin  HKI sun  sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’. Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba,  a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya  Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa;               “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
    A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83. Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.” Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida wa kotun cewa mutumin ya yi yunƙurin aika-aikan ne bisa zargin matarsa da kama kuruwar ɗansu da ya jima yana fama da rashin lafiya. Magidancin da ke zaune a ƙauyen Gawo da iyalin nasa ya musanta tuhumar da ake masa, don haka, Alƙali Nura Ahmad ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari. Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a...
    Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza. Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Jami’in na Hamas y...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi wannan kiran ne bayan wata maganan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya yi dangane da kasar Iran. Labarin ya kara da cewa, Hakan Fiddan ya bayyana cewa shirye-shiryen JMI a kasar Siriya masu rusa kasar ne, kafin juyin mulkin da Turkiyan ta dauki nauyinsa a baya-bayan nan a kasar Siriya. Ya ce: Fidan yana magana kan gagarumin taron Jana’izar Shahid Sayyid Hassan...
    Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC. Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.
    A wani rahoto wanda ba’a tantance ba kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta a wajen kungiyar OPEC +  za su kara yawan man fetur da suke haka da ganga 138,000 a cikin watan Afrilu mai zuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wasu majiyoyin kungiyar wadanda ba’a bayyana ba suna cewa kungiyar OPEC + bata kara yawan man da take haka ba na lokaci mai tsawo, amma a halin yanzu zata kara kamar yadda aka sanar. Labarin ya kara da cewa kungiyar tana rage ganga miliyon 5.85 wanda kuma shi ne kashi 5.7%  na yawan man da ake haka a duniya, wannan kuma ya yi dai dai da shawarar da OPEC + suka dauka tun shekara...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta bada sanarwan cewa, sauye –sauye na asasi dake faruwa a kasar Amurka, zai shafi hukumar da ma MDD. Kwamishinan hukumar Volker Turk ya bayyana cewa fadar ‘White House’ a halin yanzu ta na gudanar da sauye-sauye na asasi a cikin hukumomi da ma’aikatu a Amurka, wadanda kuma za su shafi al-amura da dama a cikin gida da kuma sauran kasashen  duniya. Volker Turk ya ce al-amura da suka shafi nuna wariya ne, mai yuwa su zama akasin haka nan gaba, bayan wadannan sauye sauye sun fara aiki. Wannan dai shi ne jawabi mai muhimmancin da wani jami'an MDD ya gabatar dangane da abubuwan da ke faruwa a sabuwar gwamnatin Amurka. Turk ya kuma...
    Haka kuma, an sake zaɓar Mojisola Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar bayan sauka daga matsayinta na kakakin majalisar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro sun hana mutane zuwa kwasar man fetur daga wata tankar mai da ta yi hatsari a Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. A safiyar ranar Litinin ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC), suka ɗauki wannan mataki bayan faɗuwar tankar man a kan babban hanyar Jalingo zuwa Wukari. Rahotanni sun bayyana cewa faɗuwar tankar man ke da wuya, jami’an tsaron suka isa wurin, inda suka killace wurin domin hana mutane kaiwa inda man yake. Daga nan ɗauke tankar man da babbar motar ɗauko, aka mayar  wata motar sannan aka tafi da ita. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
    Taron kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin (CPPCC) da za a fara ranar 4 ga watan Maris, da na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da za a fara ranar 5 ga watan Maris, su kasance manyan taruka biyu na kasar Sin inda ake gangamin siyasa domin nazartar baya da kuma hangen gaba. Wadannan hukumomi biyu suna karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda ke karkashin jagorancin babban sakataren Xi Jinping. Kwamitin CPPCC na kasa, mai mambobi 2,169, yana aiki ne a matsayin babbar hukumar da ke tafiyar da tsarin dunkulewar sassan kasar ta fuskar siyasa, wanda ke hada kungiyoyin zamantakewa daban daban mashawarta jam’iyyar. Ita kuma, majalisar NPC mai wakilai 2,977, tana aiki ne a...
    A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki wani fim da aka shirya a kasar Sin kai tsaye, a allunan sinima na kasashen yammacin Afirka. Kuma a cewar wani manajan gidan sinima dake Abuja, fadar mulkin Najeriya, duk da kasancewar fim din shi ne na farko da ya shiga gidajen kallon na kasuwanci a birnin, jigon labarin ya samu karbuwa matuka tsakanin masu kallo. Ya ce shigar fina-finan Sin kasuwar gidajen kallo a...
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da hurumin gudanar da bincike kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduagha ke yi wa Sanata Godswill Akpabio. A bayan nan dai ana ci gaba da samun ƙarin kiraye-kirayen gudanar da cikakken bincike kan zargin da Sanata Natasha ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio a kan cewar ta ƙi ba shi haɗin kai, shi ne ya sa ya ke yi mata bita da ƙulli. NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17 yana ɓuya An sake zaɓen Obasa Kakakin Majalisar Legas Sanata Natasha Akpoti Uduaghan daga Jihar Kogi ta yi wannan zargin ne jim kaɗan bayan da aka soma kai ruwa rana tsakaninta da...
    Hukumar kula da gandun daji da filayen ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, namun dajin kasar ta Sin sun karu yadda ya kamata ba tare da cikas ba. Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau, yayin da yawan damisar dusar kankara ya kai fiye da 1,200. Sai kuma adadin giwayen daji nau’in na Asiya da ya karu daga fiye da 150 zuwa sama da 300. A fannin shuke-shuke da tsirrai na daji kuwa, an samu nasarar dawo da nau’o’in halittunsu fiye da 200 dake cikin hadarin bacewa bat a duniya, kuma yawancin jinsunansu sun farfado tare da samun kariya yadda ya kamata....
    Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya. Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin. Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo...
    Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) za ta gudanar da taron shekara-shekara daga ranar 4 zuwa ta 10 ga Maris a nan birnin Beijing, a cewar wani kakaki a yau Litinin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Litinin ne aka gudanar da taron manema labarai na taro na uku, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC karo na 14, inda mai magana da yawun taron Liu Jieyi, ya gabatar da yanayin taron ga kafofin watsa labarai na kasar Sin da na waje, tare da amsa tambayoyin manema labarai. A fannin gudanar da ayyuka da ba da shawarwari, Liu Jieyi ya gabatar da cewa, CPPCC ta mai da hankali kan batutuwa masu muhimmanci da wahala, da suka hada da inganta zamanantarwa irin ta Sin, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali na zamantakewar al’umma, kuma ta gudanar da ayyuka da suka shafi tattauna batutuwan siyasa guda 85, da aiwatar...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
    Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.” Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka”...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa. ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci. Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.  Amma daga bisanio ya zarge su da...
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin sake gina ba zai kasance na Masar ne kawai ko kuma na Larabawa ba amma zai nemi goyon bayan kasa da kasa don tabbatar da aiwatar da shi cikin nasara. Abdelatty ya ce “Za mu yi tattaunawa mai zurfi tare da manyan kasashe masu ba da taimako da zarar an amince da shirin a taron kasashen Larabawa mai zuwa.” Abdelatty ya ce bayan taron gaggawa...
    Babban jami’in bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya kira matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin dake shiga Gaza a matsayin abin damuwa. Jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Tom Fletcher, ya yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na katse taimakon da take baiwa Gaza, yana mai cewa abin takaici ne. A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya tuna cewa “Dokar kasa da kasa ta bayyana karara cewa dole ne a bar agajin jin kai ya shiga zirin Gaza.” Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da dama da kwararru kan kare hakkin bil adama sun yi gargadin cewa wannan mataki ya zama keta dokokin kasa da kasa da kuma...
    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin nasa, Macron ya ba da shawarar cewa kasashen Turai su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro da kashi 3 zuwa 3.5 na GDP don mayar da martani ga canje-canjen abubuwan da Washington ta sa a gaba. “Tsawon shekaru uku, Rashawa suna kashe kashi 10% na GDPn su a fannin tsaro; Don haka dole ne mu shirya don abin da ke gaba. »
    Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana. Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar. HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki Bayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana. Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa. Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta...
    Kamfanin gungun gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, zai watsa bikin bude zama na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC karo na 14 a gobe Talata 4 ga watan nan. Za a bude taron ne da karfe 3 na rana bisa agogon Beijing. Kuma shugaban majalisar ta CPPCC Wang Huning, zai mika rahoton aikin zaunannen kwamitin koli na majalissar CPPCC. Kazalika a yayin zaman, kafofin rediyo da na talabijin daban daban dake karkashin CMG, za su gudanar da shirye-shirye kai tsaye, kana su ma sabbin kafofin sadarwa na zamani za su shiga a dama da su a wannan aiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa  zuwa aiki. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin. A cewarsa, wani bincike da aka gudanar  bayan hawansa karagar mulki, ya nuna cewa malaman makarantu da dama ba kasafai suke zuwa aiki ba. Ya ce hakan na daga cikin dalilan tabarbarewar ilimi a yankin, wanda ke bukatar kulawar gaggawa. Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya yi nuni da cewa, “Ilimi muhimmin abu ne a kowane fanni na rayuwar dan Adam, don haka ba za mu yi kasa...
    Ƙungiyar Kwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin wutar lantarki a daidai lokacin da ’yan ƙasar ke fama da ƙuncin rayuwa. NLC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C. Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yara Miji ya amince saurayin matarsa ya tare a gidansu Channels TV ya ruwaito wannan daga sanarwa da NLC ɗin ta fitar a ranar Lahadi bayan wani taro da ta yi a Jihar Adamawa. “NLC ba ta amince da yunƙurin Hukumar Lantarki ta Nijeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarkin kwastomomi daga layin B da A...