Aminiya:
2025-03-06@03:13:13 GMT

Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa

Published: 5th, March 2025 GMT

Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan.

Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka:

Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata

1.

Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar abin da zai rage lada ko karya azumi.

2. Sallah: Ya fi dacewa a dage da Sallar Taraweeh da Tahajjud, tare da yin sallolin farilla a cikin jam’i da nafiloli da ake yi kafin ko bayan su.

3. Ciyarwa: Ciyarwa tana da matuƙar muhimmanci, ko da dabino ko ruwan sanyi ne. “Domin Annabi (SAW) ya ce, duk wanda ya ciyar da mai azumi, za a ƙara masa lada kamar ya yi wani azumin ne,” in ji Sheikh Daurawa.

4. Umrah: Idan mutum yana da hali, yana da lada mai girma yin Umrah a watan Ramadan. Idan kuwa ba shi da hali, sai ya maye gurbinsa da ciyarwa.

5. I’tiƙafi: Sheikh Daurawa ya shawarci Musulmi da su mayar da hankali wajen shiga I’tiƙafi, idan suna da hali, domin yin ibada tare da nesantar shagalin duniya.

6. Daren Lailatul Ƙadar: Ya buƙaci Musulmi da su dage da neman dacewa da daren Lailatul Ƙadar ta hanyar yin salloli, addu’o’i, da sauran ayyukan alheri.

7. Yafiya: Sheikh Daurawa ya buƙaci Musulmi da su yafe wa juna, domin neman gafarar Allah a cikin wannan wata mai alfarma.

8. Karatun Al-Ƙur’ani: Ya ce ya dace Musulmi su dage da yawaita karatun Al-Ƙur’ani, domin a watan Ramadan aka saukar da shi.

9. Addu’a: Yana da muhimmanci a dage da yin addu’a, musamman a lokacin Sahur, lokacin buɗa-baki, da lokacin da ake cikin azumi, domin a waɗannan lokuta Allah na karɓar addu’o’i.

10. Zumunci: Sada zumunta a watan Ramadan yana ƙara albarka, arziƙi, da zaman lafiya, kamar yadda Sheikh Daurawa ya bayyana.

11. Tausayi: Azumi yana koyar da tausayi da taimako, domin mai azumi zai jin halin da masu buƙata ke ciki, hakan zai sa ya fi jin ƙansu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Al Ƙurani Ramadan Sheikh Daurawa Tausayi Sheikh Daurawa ya a watan Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17 yana ɓuya

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas.

Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa ne bayan shafe shekaru 17 yana ɓuya, inda yake fataucin miyagun ƙwayoyi na biliyoyin nairori a faɗin duniya.

Sanarwar ta ambato Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya yana bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a yau Litinin.

Shugaban NDLEA ya kuma bayyana yadda jami’an sashen ayyukan musamman na hukumar suka riƙa bin diddigin Ogbonnaya biyo bayan nemansa ruwa a jallo da hukumar ’yan sandan duniya INTERPOL ke yi da kuma bayanan sirrin da hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ta samar a kansa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata
  • Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu
  • Bayan Cece-ku-ce Da Zelenskyy, Trump Ya Dakatar Da Tallafin Soji Ga Ukraine 
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba
  • NDLEA ta cafke madugun fataucin miyagun ƙwayoyi bayan shekaru 17 yana ɓuya
  • Ramadan: Coci ya ciyar da Musulmi 1,000 a Kaduna
  • Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda
  • MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan
  • NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan