2025-03-06@04:14:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6

«Sheikh Daurawa ya»:

    Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan. Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka: Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata 1. Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar abin da zai rage lada ko karya azumi. 2. Sallah: Ya fi dacewa a dage da Sallar Taraweeh da Tahajjud, tare da yin sallolin farilla a cikin jam’i da nafiloli da ake yi kafin ko bayan su. 3....
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin. Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole. Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka...
    Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland. Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada. Jaridar ta...
    Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta yi allawadai da takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun, ta kuma kara da cewa zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya kamar yadda ta saba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kotun ICC kotu ce wacce take karban koke-koke na mutane da kasashe a duk fadin duniya, amma wacce gwamnatin Amurka ta ke son takaita ikonta don tallafawa HKI a yakin da take fafatawa da Falasdinawa wadanda ta mamaye kasarsu fiye da shekaru 76 da suka gabata. A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a kan wata doka wacce ta dorawa kotun ta...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi. Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe. Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa waɗanda maharan suka yi raunin harbi suna samun kulawa a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya. Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da  cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma ya zauna da shugaban kasarta. A wani bangare na maida martanin Aragchi ya bayyana cewa dangane da fadinsa, ba zai taba amincewa Iran ta mallaki makaman Nukliya ba, yace Iran mamba ce a yarjeniyar NTP, a kuma hukumar makamashin nukliya ta IAEA. Zasu lamunce masa kan cewa Iran bata bukatar makaman nukliya. Amma duk da haka Iran ba zata taba sayar da hakkinta na mallakan...
۱